Trump: An Kashe Baghdadi, Shugaban Kungiyar ISIS

Shugaban Kungiyar ISIS, Baghdadi Ya Mutu bayan Wata Harin Rundunar Sojojin Amurka

Kafofin yada labarai ta Amurka sun bayar da rahoton cewa, shugaban kungiyar Islamic State (ISIS), Abu Bakr al-Baghdadi ya mutu bayan wani hari da sojojin Amurka suka kai a yankin Idlib na Siriya.

Ko da shike ana zargin cewa shugaban ISIS din ya kashe kansa ne da mayafin kunar bakin wake yayin da dakarun Sojojin musamman na Amurka suka kai hari yankin da yake, in ji kafofin watsa labarai.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a ranar Lahadin da ta gabata ya bayar da tabbacin Mutuwar Abu Bakr al-Baghdadi, shugaban kungiyar Islamic State (ISIS).

Da Trump ke gabatarwar a wata faifar watsa labarai daga fadar White House, ya ce; “Baghdadi ya mutu kamar kare,” a cikin wani mummunan hari, da sojojin Amurka na musamman suka yi a yankin arewa maso yammacin Siriya.

“Babu wani Sojar US da yayi rauni ko kadan, duk da yawar harbe-harben da aka yi hade da fashewar bama bamai. Wanda kawai aka rasa kawai shi ne shugaban na ISIS, Baghdali hade da Karen rundunar Sojoji Amurka a cikin wata garwa inda shugaban kungiyar ya fashe da bam.” inji Donald Trump.