Jihar Plateau: Zamu samar da tsaro ga Jihar, Mafarauta sun gayawa Simon Lalong

Wata kungiyar Mafarautan Jihar Plateau (PHA) sun yi barazanar cewa zasu karfafa tsaro a Jihar Plateau.

Kwamandan Kungiyar (PHA), Mista Igyem Danladi ya gabatar da cewa kungiyar na goyon bayan Gwamna Simon Lalong saboda irin gwagwarmaya da kokarin sa na ganin cewa akwai zamantakewar lafiya a Jihar Plateau.

“Zamu karfafa samar da tsaro a kewayen Jihar Plateau don magance duk wata rukuni na ‘yan ta’adda” inji Danladi, shugaban kungiyar (PHA) a yayin da suka gana da Gwamnan Jihar a yau Talata 29 ga Watan Janairu.

“Sau dayawa mun kwato dabbobi daga hannun mahara a yankin a yayin da suke kokarin sace ta daga masu shi” in ji Danladi.

“Sau da dama kuwa mafarauta sun bi ‘yan hari har cikin bakin daji don kwato hakin mutane daga garesu, harma da kame barayi da ke muzunta mutane a yankin Shedam” inji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Kashim Shettima, Gwamnan Jihar Borno ya gabatar da cewa zai sanya Mafarauta ga yaki da Boko Haram a Jihar.

Karanta kuma: Yan Hari da bindiga sun Kashe Insfektan ‘Yan Sanda biyu a Jihar Katsina

Buhari ya sauya labarin da aka saba yi game da Najeriya – Lalong

Simon Lalong, Gwamnan Jihar Filato ya ce shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauya labarin da aka saba yi game da Nijeriya a kasashe akan yaki da cin hanci da rashawa.

Lalong ya ce wannan ne a sakon sa na musanman zuwa ga Shugaba Buhari ta hannun Babban shugaba Harkokin Sanarwa, Mista Mark Longyen, a ranar Lahadi a Jos.

“Mai Girma, ka yi nasara wajen canza labarin da aka saba yi game da Najeriya da siffarta a tsakanin  Jam’iyan haɗin gwiwar al’ummomi.

“Buhari ya yi nasarar aiwatar da wanna a sa’ar shi na farko a ofishin,” inji shi.

Lalong, wanda ya taya Shugaba Buhari murna a shirin bukin ranar haihuwar sa ta shekaru 76 wanda zai yi a yau Litini, ya bayyana shi a matsayin mai tsari da kuma tattalin zamantaka na Nijeriya.

Gwamna ya ce, ranar haihuwar Buhari ya tuna masa da cewa ya kasance wani tauraron yaki da cin hanci da rashawa, mai son al’umma duka, mashahuriyar kasa da nagari.

 

Karanta kuma: Za mu gudanar da zaben 2019 tare da dokokin da aka saba da ita – INEC