Zaben Kogi: Natasha Ta Gabatar Da Karar Rashin Amince Da Zaben Bello a Kotu

‘Yar takarar kujerar gwamna a jihar Kogi a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna a ranar 16 ga Nuwamba 2019, Natasha Akpoti, ta tunkari kotun kolin zabukan gwamnoni kan sakamakon zaben.

A cikin takardarta, Barr. Akpoti ta shigar da kara a gaban kotun a ranar Asabar da daddare, na neman a soke zaben.

Ta sanya sunan wanda ya lashe zaben, Gwamna Yahaya Bello, da abokin karawarsa Edward Onoja, da Hukumar Gudanar da Zaben Kasa (INEC), hadi da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a matsayin wadanda take karar akai.

A cikin karar da Akpoti ta gabatar, ya bayyana da cewa zaben ya gudana ne da rashin daidaituwa tare da tashin hankali kuma a saboda haka, ta bukaci kotun ta nemi Bello da sauka daga kujerar sannan ta umarci INEC ta sake gudanar da sabon zabe.

Ta kara a cikin karar da cewa cire sunan ta daga wasu takardu na sakamakon zaben da aka yi, da kuma matakin rubuta sunanta da Biro a takardar sakamakon abu ne da bata amince da shi ba.

Naija News ta fahimci cewa Babban Lauya, Ola Olanipekun, (SAN) ne ya wakilci Akpoti a gabatar da karar.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 4 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 4 ga Watan Disamba, 2019

1. Rufewar kan iyaka: PPPRA Sun Karyata Shugaba Buhari Kan Amfanin Da Man Fetur a Kasa

Babban Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (PPPRA) ta karyace zance da ikirarin da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi game da yawan man da kasar ta samu ta hanyar rufe iyakar.

Naija News ta samu labarin cewa shugaban a yayin karban tawagar kungiyar dattawan jihar Katsina a garinsa Daura ya bayyana cewa, yawan diba da amfani da man fetur a kasar ya ragu sama da kashi 30 cikin 100 tun lokacin da aka rufe kan iyaka da makwabtan kasashe, yana mai nuni da cewa tun a baya akwai yawaitar zuba da amfani da man kasar. Ya kuma ce matakin da gwamnatin sa ta dauka kan yanayin zai ceci kasar biliyoyin nairori kan kudaden shigo da kaya.

2. DSS ta Bayyana Wata Sabuwar Shiri Na Kawo Damuwa A Najeriya

Ma’aikatar Tsaro ta kasa (DSS) a ranar Talata ta bayyana sabbin makircin da wasu kungiyoyi ke yi na jefa Najeriya cikin tashin hankali da aiwatar da zanga-zanga.

Hakan ya bayyana ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar.

3. Gwamnan PDP Ya Bayyana Goyon Baya Ga Buhari Kan rufe Shingen Kasar

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, a ranar Litinin, ya ba da cikakken goyon bayansa ga matakin Shugaba Muhammadu Buhari na rufe iyakokin kasar.

Umahi ya bayyana matsayin sa ne kan zancen a yayin makon bude Babban Bankin Kasa, a filin wasa na Onueke da ke karamar Hukumar Ezza ta Kudu a jihar.

4. Biafra: ‘Yan Sanda Sun Bayyana Kudurin Kamun Lauyan Nnamdi Kanu

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Anambra ta bayyana tabbacin neman kamun Ifeanyi Ejiofor, Lauya ga shugaban kungiyar‘ Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.

A ranar Talata da ta wuce ne Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Anambra, CP John Abang ya ba da sanarwar cewa, suna neman kamun lauyan gwagwarmayar neman kafa kasar Biafra.

5. Saraki Ya Kalubalanci EFCC A Yayin Da Kotu Ta ba da Umarnin Sadaukar da Gidajen sa Ga Gwamnati

Tsohon shugaban majalisar dattijai na Najeriya Dr. Bukola Saraki ya bayyana umarnin da aka bayar na karbo kadarorin sa a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, a matsayin cin mutuncin tsarin kotun da kuma keta dokar hana fita ta babban kotun tarayya da ke Abuja.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa wata babbar kotun tarayya da ke Legas ta ba da umarnin cewa Saraki ya sadaukar da wasu gidajensa guda biyu a Ilorin sakamakon wata takaddar da hukumar EFCC ta gabatar akansa.

6. Gwamna Yahaya Bello ya Nemi Ma’aikatansa Da Su Nuna Masa Sakamakon Zaben Mazabarsu

Gwamnan jihar Kogi, Mista Yahaya Bello ya ba da sanarwar ka’idoji da kawai zai yi amfani da shi wajen zabin sabbin kwamitocinsa na siyasa wadanda za su yi aiki tare da shi a shekaru hudu masu zuwa.

Naija News ta tuno da cewa Gwamnan ya kori duk zababbun ma’aikatansa da bude sabon filin daukar sabbin ma’aikata.

7. Shugaba Buhari Ya Aika da Jerin Sabbin Shugabbanin Kula da Hidimar Hajji a Majalisa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika sunayen sabbin Shugabannai da membobin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa (NAHCON) ga Shugaban Majalisar Dattawa don tabbatarwa.

Hakan ya bayyana ne a cikin wata wasika da ya aika wa Majalisar Dattawa, wacce kamfanin dilancin labarai ta PRNigeria ta karba, Shugaba Buhari ya rubuta cewa:

“Bisa ga sashi na 3 (2) na Dokar Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) 2006, Ina mai farin cikin mikawa da neman tabbaci daga majalisar dattawa kan wadannan sunayen da aka zaba don matsayin Shugaba da membobin Hukumar Kula da Aikin Hajji ta kasa.”

8. Kada Ku Bawa Buhari Rancen Kudi – Inji Cif Olabode

Cif Olabode George, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa ya yi kira ga kasashen waje da kar su bai wa Shugaba Muhammadu Buhari rancen kudi da yake bukata.

Mista George ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani game da shirin rancen dala biliiyan $29.96 na 2016-2018 da Shugaba Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa saboda dubawa da amincewarsa.

“kasashen turai za su yi dariya da ba’a ga Najeriya saboda karbar irin wadanan bashi, saboda ya koka da yadda ake asarar kudaden kasar ta hanyar gudanar da yauka.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Naija News Hausa

Kogi: Yahaya Bello Ya Bada Umarnin Korar Manyan Ma’aikata A Karkashinsa

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya umarci duk masu rike da mukaman siyasa su mikar da matsayinsu ga mafi girman ma’aikatan farar hula a ma’aikatar su, sashen su da kuma hukumar (MDA).

Sanarwar wacce aka rattaba hannu da kuma bayar a ranar Litinin ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar, Dakta Folashade Arike Ayoade ta lura cewa an raba wadannan a kasa da matsayinsu a yanzu.

“Dukkanin kwamishinoni, Darakta-Janar a harabar shugabancin Gidan Gwamnatin jihar. Ma’aikata ga Gwamna, Ma’aikata ga Mataimakin Gwamna, Ma’aikata ga shugaban Ma’aikata, Ma’aikata ga Mai Martaba, matar gwamnan da kuma mataimakiyarta, Matar Mataimakin Gwamna.”

Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa umarnin bai shafi “Shugaban Ma’aikatar Babban Sakatare-Janar na jihohi da Karamar Hukumar, Ciyamomi da Membobin kwamitocin jihar ba.”

“Dole ne a kawo karshen mikawar matsayin a ranar Talata, 3 ga Disamba, 2019. A mikar da kwafin bayanai na barin matsayin ga ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kogi a kwafi mai laushi da kuma a takarda”

Sanarwar ta kara da cewa, “Sabuwar Dokar Gwamnatin Jihar ta nuna godiya ga jami’an da abin ya shafa don irin gudummawar da suka bayar wajen ci gaban jihar a wa’adin nasu.”

Bello: Natasha Akpoti ta Aika wa Shugaba Buhari Gargadi akan zaben Kogi

‘Yar takarar kujerar gwamna a zaben 2019 na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a jihar Kogi, Natasha Akpoti ta kalubalanci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya sake yin la’akari da yanayin da ya shafi sakamakon zaben ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi.

Natasha a cikin gargadin ta bukaci Shugaba Buhari da ya binciki alamuran tashe-tashen hankula yayin zaben gwamna na Kogi da aka kamala a mako biyu da ta gabata.

Ta bukaci Shugaban kasar da ya umarci ‘Yan sanda su yi nazari da binciken zargin da ake wa Yahaya Bello, gwamnan jihar da kuma dan takara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a yayin zaben, da cewa Gwamnan ya ba da umarnin a kashe ta.

Natasha ta gabatar da hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata, a sakon ta da ta wallafa a shafin Twitter inda ta rubuta:

“Ya Shugaba Buhari, na gode da bada umarnin gudanar da bincike kan kisan shugaban matan PDP, Malama Abuh, wadda ‘yan jam’iyyar APC suka yi a Kogi. Don Allah a umarci ‘yan sandan Najeriya da su binciki wannan hari da Yahaya Bello hadi da ‘yan ta’addan Jam’iyyar APC a Kogi suka gudanar a ya yi zaben jihar da aka kamala.”

Dino Melaye Ne Sanadiyar Kashe-kashe Da Aka Yi A Zaben Kogi – APC

Gwamnatin jihar Kogi ta zargi Sanata Dino Melaye da alhakin tashe-tashen hankula da ya afku a yayin hidimar zaben fidda gwani wadda aka yi a kwanan nan a jihar.

Babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Yahaya Bello, Mohammed Onogwu ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a gidan talabijin na Channels ranar Lahadi da ta gabata.

Onogwu a cikin hirar ya yi ikirarin cewa gwamnatin jihar tana da shaidar bidiyo da zai bayar da tabbacin cewa Sanata Dino ne ke rarrabar da kudi a ranar zaben.

“Muna da bidiyo, shaidar inda shi Dino Melaye yake rarraba kudi a layin da ake jefa kuri’a.”

“Sakamakon rahotannin da masu sa ido daban-daban suka bayar a bayan zaben, an karshe da cewa hakika zaben gwamnan ya karshe da gaskiya.”

“Duk tashe-tashen hankula da suka faru a zabukan da suka gabata, Dan takaran, Sanata Dino Melaye ne ya ke da alhakin haka.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dan takarar All Progressives Congress, Smart Adeyemi zai yi takara da Dino Melaye a zaben cike gurbi wanda aka dage zuwa ranar 30 ga watan Nuwambam, kamar yadda Hukumar Zabe  ta sanar”.

Kogi: Hukumar INEC Ta Baiwa Gwamna Bello Takardar Shaidar Nasara da Jagoranci

Hukumar da ke gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) ta bayarwa dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Kogi, Yahaya Bello da abokin karawarsa Edward Onoja Takaddun shaida na Komawa kan mulki a ranar Alhamis.

Hukumar zaben a yau Alhamis ta bayar da takardar shaidar komawa kan kujerar gwamnan jihar Kogi ga Yahaya Bello, a nan dakkin bikin Farfesa Mahmoud Yakubu, a hedikwatar hukumar zaben da ke a Lokoja, babban birnin jihar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dan takarar jam’iyyar APC, Yahaya Bello ya samu yawar kuri’u 406,222 don kayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Musa Wada, wanda ya samu kuri’u 189,704.

Kwamishinan hukumar na kasa wanda ke lura da yankin Arewa ta Tsakiya, Mohammed Kudu Haruna, wanda ya gabatar da takardun shaidar ga zababben gwamnan ya ce, “Yau ne sabon wa’adi ya fara bayan kamala zaben da kuma kira zuwa ga jagoranci ga zababban gwamna da mataimakin nasa.”

Kogi: Karya Ne ba a bi na Bashin Albashin Ma’aikata – Yahaya Bello

Gwamna Jihar Kogi, Yahaya Bello ya karyata rahoton da ke cewa ana bin sa bashin albashin ma’aikata a Jihar, ya lura cewa irin wannan rahoton karya ne.

Gwamnan jihar Kogi ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta gamu da alawus din ma’aikatan da ke jihar kuma ya nace cewa gwamnatinsa ba ta bin ma’aikata bashin ko taro.

Bello yayin da yake magana a gidan talabijin na Channels TV ya zargi ‘yan ta’addan jam’iyyar Peoples Democratic Party da soke wani mazaunin shiyarsu bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben Nuwamba 16.

Zababben gwamnan na jihar Kogi ya yi zargin cewa har ma da matar mataimakinsa an harbe ta bayan da ya lashe zaben gwamnan.

“Duk wadannan rahotannin da ni ke samu na albashi karya ne. Gwamnonin da suka gabata a Jihar Kogi sun mallaki albashin ma’aikata, tun daga wa’addin Audu zuwa magabaci na. Jihar Kogi ba ta bin kowa bashi a kowane sashi, abin da ya rage kawai shi ne kashi goma daga gwamnatin da ta gabata.” inji Yahaya Bello.

“Game da durkusawar El-Rufai, yana rokon mutanen jihar ne su yiwa Bello afuwa don tabbatar da cewa cika da tsaro, zaman lafiya, ba wai saboda ya kasa biyan albashi ba.”

Kogi: Hukumar INEC ta Gabatar da Mai Nasara Ga Zaben Jihar Kogi (Kalli Yawar Kuri’u a Kasa)

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Litinin, ta bayyana sakamakon karshe da kuma wanda ya yi nasara a zaben gwamna na Kogi na shekarar 2019.

Jami’in hukumar INEC da ya jagoranci hidimar zaben gwamnan da ta majalisa, Farfesa Ibrahim Umar Garba, ya bayyana sakamakon, a ranar Litinin, 18 ga Nuwamba a cibiyar tattara kuri’u da ke a Lokoja, babban birnin jihar bayan an samu sakamako daga dukkan kananan hukumomin.

Dangane da sakamakon, Gwamna Yahaya Bello na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu yawar kuri’u 406,222 don kayar da sauran ‘yan takara, musanman Engr. Musa Wada na Jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 189,704.

Zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi ya kumshi yawarn ‘yan takara 24 da suka fafata a zaben.

Dubi cikakken sakamako bisa ga kuri’un da aka tattara daga kananan hukumomi na manyan jam’iyyun siyasa biyu a zaben.

1. Olamaboro
APC – 16,876
PDP – 8,155

2. Idah
APC – 4,602
PDP – 13,962

3. Yagba West
APC – 7,868
PDP – 8,860

4. Ajaokuta
APC – 17,952
PDP – 5,565

5. Mopa-muro
APC- 4,953
PDP – 3,581

6. Okehi
APC – 36,954
PDP- 478

7. Yagba East
APC – 6,735
PDP – 7,546

8. Koton Karfe
APC – 14,097
PDP – 9,404

9. Kabba/Bunu
APC – 15,364
PDP – 8,084

10. Okene
APC – 112,762
PDP – 139

11. Igala Mela/Odolu
APC- 8,075
PDP – 11,195

12. Adavi
APC – 64,657
PDP – 366

13. Omala
APC- 8,473
PDP – 14,403

14. Ijumu
APC – 11,425
PDP – 7,585

15. Ogori-Magongo
APC – 3,679
PDP – 2,145

16. Bassa
APC – 8,386
PDP – 9,724

17. Ankpa
APC – 11,269
PDP – 28,108

18. Ofu
APC – 11,006
PDP – 12,264

19. Dekina
APC – 8,948
PDP – 16,575

20. Ibaji
APC – 12,682
PDP – 10,504

21. Lokoja
APC – 19,457
PDP – 11059

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 18 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 18 ga Watan Nuwamba, 2019

1. INEC ta Dakatar Da Sanar da Sakamakon Zaben Gwamnonin Kogi

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Lahadi ta sanar da cewa ta dakatar da sanarwar sakamakon zaben gwamnoni na ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi.

Wannan sanarwan an bayar da ita ne a bakin Babban Ofisan da Shugaban Hukumar INEC ta Jihar, wanda ke jagorancin hidimar zaben.

2. Tsoracewa A Yayin da INEC ta Fara Bayyana Sakamakon zaben Bayelsa

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka gudanar ranar Asabar.

Naija News ta fahimci cewa an jinkirta ne da sanar da sakamakon wanda ada aka shirya da farawa a karfe 10 na safiyar ranar Lahadi a cibiyar Farfesa Mahmood Yakubu.

3. Fayose ya Kalubalanci zaben Jihar Kogi da Bayelsa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya koka da sakamakon zaben gwamnonin jihar Kogi da na jihar Bayelsa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa duka zabukan da suka gudana a ranar Asabar sun kasance da rikice-rikice da kuma magudi.

4. Dalilin da yasa Membobin Edo na APC ke son Obaseki ya fita – Airhavbere

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo, Charles Airhavbere, ya ba da dalilan da suka sa membobin jam’iyyar ke son tsige Gwamna Godwin Obaseki.

A yayin da yake zartawa da manema labaran NAN a ranar Lahadi, tsohon mai neman takarar gwamna a Edo ya zargi Godwin Obaseki da kin sauraren muryar dalilai.

5. Abinda aka ga Yahaya Bello na yi yayin da INEC ke sanar da sakamakon zaben Kogi

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka hango Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a hotuna tare da mukarraban sa a Lokoja, babban birnin jihar, yayin da suke shan shayi da nishadewa.

Ka tuna kamar yadda Naija News ta sanar, ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba ne Hukumar Zabe ta gudanar da zaben Gwamnonin jihar Kogi.

6.  Ban Amince da Sakamakon Zabe ba – Musa Wada ya Kalubalanci Hukumar INEC

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.

Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.

7. Zaben Kogi: INEC ta ayyana ma’aikata 30 da suka Bata

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC), ta bayyana jami’anta 30 da suka bace a zaben gwamnoni da aka yi a Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta fahimta da cewa mutane 30 din da suka bata suna cikin malaman zabe da aka dauka don hidimar zaben zaben gwamnoni na ranar Asabar a jihar Kogi, arewa maso-tsakiyar Najeriya.

8. Kotun daukaka kara ta Soke Dan Jam’iyyar PDP a Majalisa

Kotun daukaka kara da ke zaune a Owerri ta tsige dan majalisa mai wakiltar mazabar Isiala Mbano / Onuimo / Okigwe da ke jihar Imo a majalisar wakilai, Obinna Onwubuariri.

Da yake yanke hukuncin a ranar Asabar, shugaban kwamitin, Mai shari’a R.N Pemu, ya bayyana da cewa nasarar Onwubuariri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a watan Fabrairu ya kasance ne da sabawa dokar zaben kasa kamar yadda aka ayyana tun shekarar 2010.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Kogi: Ban Amince da Sakamakon Zabe ba – Musa Wada ya Kalubalanci Hukumar INEC

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.

Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.

Naija News ta fahimci cewa a cikin sakamakon zaben da aka riga aka sanar, gwamna Bello na gaban sauran ‘yan takara da yawar kuri’u.

Rahoton sakamakon ya nuna da cewa Gwamna Bello yana kan gaban sauran ‘yan takara 23 da yawar ƙuri’u sama da dubu 200, 000 a cikin kananan hukumoi 15 daga kananan hukumomi 21 da ke a Jihar, kamar yadda aka sanar.

Wada wanda ya yi magana da manema labarai a Lokoja a ranar Lahadi, ya yi watsi da sakamakon, yana zargin cewa mataimakin gwamnan jihar, Cif Edward Onoja tare da hukumomin tsaro suna tafiya ba tare da izini ba kuma suna ziyartar cibiyoyin tattara kuri’u inda suke sauya sakamakon don fifita jam’iyyarsu.

“Lallai PDP zata kalubalancin wannan sakamakon a kotu.” inji Wada.

“Sakamakon ba tabbacin gaskiyar abin da ya faru ba ne a runfar zabe. Mutanen jihar sun zabi PDP amma APC ta canza sakamakon da ya gamshe su.

Sakamakon da hukumar INEC ta bayyana har zuwa yanzu sakamakon ba zamu yarda da hakan ba. An riga an canza duk sakamakon da aka samu a kowace runfar zabe kuma za mu kalubalanci wannan zaben. Ba gaskiyar abinda ya gudana aka sanar ba.”  inji shi.

“Ni ne dan takarar Jam’iyyar PDP kuma ba lallai ne in jira har sai sun kashe ni ba. Dole ne in yi kira ga jama’ar Najeriya su sani cewa APC ta yi magudi a zaben,” in ji Wada.