‘Yan Sandan Reshen Jihar Katsina sun Kame Wani Shugaban ‘Yan Fashi

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta kama wani mugun shugaban ‘yan fashi da garkuwa, mai shekaru 20 ga haifuwa da suna, Aliyu Sani na Sabuwar-Unguwa barikin soja, Katsina.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Gambo Isah ne ya bayyana hakan ga manema labarai yayin wani taron manema labarai ta ranar Litinin a Katsina.

Ya bayyana da cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 4 ga wata Disamba, a cikin garin Katsina, bayan wata likin sirri da suka karba.

“Wani lokaci cikin watan Afrilu, wanda ake tuhumar ya hada kai da Abdulrahman Danfillo, mai shekara 25, adireshi iri daya, wanda yanzu haka aka yaudari da kuma sace wani mai suna Abubakar Muhammad da Aliyu Ahmed, dukkansu mazauna Sabuwar-Unguwa, Katsina.”

“Wadanda ake zargin sun dauki wadanda suka sace din zuwa ga wasu ‘yan fashi a dajin Gora da ke karamar hukumar Batsari a jihar Katsina.”

“An tilasta Mahaifin Abubakar Muhammad da biyan Naira dubu dari da hamsin N150,000 a matsayin kudin belin dan sa, yayin da Aliyu Ahmed ya samu tserewa daga kogon ‘yan fashinr.” Inji shi.

Mahara Da Bindiga Sun Sace ‘Yan Sanda Biyu A Jihar Adamawa

Alhaji Ahmadu Dahiru, Shugaban Hukumar Kula da Canji, karamar hukumar Mubi ta kudu a Adamawa, ranar Asabar ya ce wadanda ake zargi sun sace wasu ‘yan sanda biyu sun kuma sace mutane bakwai a karkarar.

Bisa hirar Dahiru da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Gyela, ya ce; lamarin ya faru ne a kan hanyar Mubi zuwa Gyela, a ranar Talatar da ta gabata.

“Masu satar mutane suna tsoratar da kuma tsananta wa al’ummominmu a kullayomi, suna satar mutane da gangan a dare da rana. Sun kashe jami’an tsaro biyu a ranar Talatar da ta gabata wadanda suka yi sintiri a kan hanyar Mubi da Gyela.”

“A haka da nike magana da ku, kwanaki uku da suka gabata sun sace mutane biyar a Kwaja da biyu kuma a ?auyen Sauda,” in ji Dahiru.”

Ya bayyana da cewa, barayin sun yi ta tururuwa ne a saman wasu tsaunuka kusa a iyakar Najeriya da Kamaru.

Dahiru ya kara da cewa, al’ummomin sun yi asarar miliyoyin nairori ga masu garkuwa a yayin neman kubutar da wadanda aka sace daga hannunsu.

Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Adamawa, DSP Sulaiman Nguruje ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura wata rundunar jami’an tsaro don magance matsalar a yankin.

Ya kuwa yi kira ga jama’ar jihar da su kai rahoton duk wani alamun hari ko shigar ‘yan garkuwa da suka gane da shi zuwa ofishin tsaro mafi kusa.

‘Yan Hari da Makami Sun Kashe Jami’an Tsaro Biyu a Yola

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, reshen jihar Adamawa ta tabbatar da kisan wasu ‘yan sanda biyu na Rundunar ta hannun wasu ‘yan hari da makami da ba a san ko su wanene ba a Mubi, wani gari da ke kasuwanci a arewacin babban birnin jihar Yola.

Naija News ta samu labarin cewa an kashe ‘yan sanda biyun ne a ranar Litinin da daddare ta hannun wasu ‘yan hari da bindiga da suka boye a cikin daji kusa da Titin Gyella, cikin Karamar Hukumar Mubi ta Kudu.

A cewar wata majiya, an ce an kashe jami’an ‘yan sanda biyun ne hadi da sace wasu mazauna yankin shida a lokacin da wasu ‘yan bindiga suka hari ‘yan sanda da mazauna a kan hanyar Gyella.

Daga baya dai, rundunar ‘yan sanda ta ba da tabbacin cewa ba wanda aka sace yayin harin na daren Litinin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Sulaiman Nguroje, Mataimakin Sufeto Janar na ‘Yan sanda (DSP), ya tabbatar da kisan ‘yan sandan biyu.

Ya ce, “A daren jiya wasu jami’an ‘yan sanda da ke sintiri sun hangi wani mutum yana yawo a kan hanya, a bakin daji, suka kuwa yi la’akari da yanayin mutumin cewa bai cikin hankalinsa.”

“Jami’an sun gano da cewa mutumin ya tsere ne daga hannun ‘yan fashi. Daga nan sai jami’an suka yanke shawarar shiga cikin daji don fatattakar ‘yan fashin” Inji mutumin.

Ya kara da cewa, rundunar ‘yan sanda ta tattara darukan tsaro da yawa hadi da jami’ai da ke a Mubi da kewayenta, da iyaka yankin zuwa garuruwan da ke kusa da Jamhuriyar Kamaru don murkushe masu aikata muggan laifukar.

‘Yan Hari da Bindiga sun Sace Insfekta na ‘Yan Sanda, tare da Wasu A Abuja

An samu rahoton cewa an sace Insfekta Janar na ‘yan sandan Najeriya (NPF) da wani mutum guda, a kauyen Rubochi da ke Kuje, karamar hukuma a Birnin Tarayyar Najeriya (FCT), Abuja.

Rahoton da aka bayar akan jaridar The Nation wanda jaridar ta Naija News ta gane da ita ya bayyana da cewa an sace Sufeto Janar na ‘Yan Sandar ne da wani mutum a tsakar dare ranar Lahadi, 27 ga Oktoba ta hannun wasu ‘yan hari da bindiga wadanda suka afka wa al’ummar yankin da harbe-harbe.

Naija News Hausa fahimta da cewa masu sace mutanen su sace har da Kani ga tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kuje, wanda aka fi sani da Mohammed Galadima, ‘yan kwanaki kadan da suka gabata a cikin wannan yankin.

A wata majiya, an sanar da cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na safiyar ranar Juma’a, yayin da ‘yan bindigar suka fada wa gidan Galadima ta hanyar tsallake shingen gidan, inda kuma suka sace mutumin a gidansa.

Wannan gidan labaran tamu ta gane da cewa ‘yan garkuwan sun bukaci biyan naira Miliyan 10 kamin su sakeshi.

Mataimakin Kakakin yada yawun Rundunar ‘yan sandan Birnin Tarayyar Najeriya (FCT), ASP Mariam Yusuf, a lokacin da aka kira ta da bayani ta bayyana da cewa zata mayar da kira idan ta samu cikakken bayani game da yanayin.

‘Yan Sandan Najeriya sun Fitar da Sabon dabarun yaki da Laifuka a kasar

A kokarin dakile tasirin ayyukan masu aikata laifuka da hana manyan cibiyoyin sadarwa damar shawo kan manyan laifuka da ke afkuwa a kasar, Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP MA Adamu, NPM, mni yana shirya wani taron kwanaki 3 da kuma ja da baya ga dabarun Jami’an rundunar ‘yan sanda ta Najeriya.

Taron, wanda aka yiwa lakabi da “Saka karfi ga kalubalen Ingantaccen Tsaro a cikin karni na 21”, zai gudana ne daga ranar Litinin, 28 ga Oktoba, 2019 zuwa Laraba, 30 ga Oktoba, 2019 a Jasmin Hall, Eko Hotel da Suites, Legas.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ci karo da wata Cibiyar Azabtarwa ta addinin Musulunci ’a Nassarawa Quarters, Sabon Gari, Daura, garin shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari.

Hakan ya biyo ne bayan makwanni biyu da aka ci karo da irin wannan a yayin binciken da aka yi a Kaduna, inda aka gano ‘yan fursuna da aka tsare.

El-Zakzaky: ‘Yan Shi’a na Shirin Fita Zagaye a dukan Kasa don Hidimar Shekara-Shekara

Wakilan Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da ‘Yan Shi’a sun bayyana shirye-shiryen fara taron shekara da shekara da suka saba yi ta Arba’een a kasar, a ranar Asabar din nan.

Naija News ta bayar da rahoton cewa IMN ta ba da tabbacin cewa hidimar tasu za ta kasance cikin lumana kuma ba ta da duk wani yunƙurin wargaza tafiya da fitar mutane a kan hanya a ranar.

Ka tuna a baya  da cewa Farmaki ya tashi tsakanin Jami’an tsaro da ‘Yan Shi’a a birnin Tarayya, Abuja, bayan da IGP Mohammed Adamu, shugaban ‘yan sandan Najeriya ya bayar da umarni cewa a kama dukan shugabanan kungiyar Harkan Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da Shi’a.

Farmaki da ya faru a Abuja ya haifar da kashin wani babban Jami’in tsaro tare da wasu mambobin shi’a.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 21 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 21 ga Watan Agusta, 2019

1. ‘Yan sanda sun sake kama Babban Shugaban Barayi na Taraba Hamisu Wadume

Rundunar ‘yan sanda ta Najeriya (NPF) a ranar Talata da ta gabata, ta tabbatar da sake kame babban dan ta’adda da shugaban barayi a jihar Taraba, Alhaji Hamisu Bala Wadume.

Tabbacin hakan ya  samu ne bisa wata sanarwa da Kakakin Jami’an tsaro, Frank Mba, ya aika wa Naija News da cewa ‘yan sanda sun ci nasara da sake kama Wadume a cikin daren Litinin din nan a inda yake buya, nan Layin Mai Allo Hotoro na jihar Kano.

2. Kotun Koli ta yanke hukunci a kan Atiku da Jam’iyyar PDP

Kotun koli ta yi watsi da Wata kara da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takarar shugaban kasa a zaben 2019, Atiku Abubakar, suka shigar.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa matakin kotun ya bayyana rashin amincewa da bukatar Jam’iyyar PDP da Atiku Abubakar.

3. EFCC ta Hari Gidan Ambode

Hukumar Yaki da yi Cin Hanci da kare Tattalin Arziki Najeriya (EFCC) a ranar Talata, sun kai hari da mamaye gidan Mista Akinwunmi Ambode, tsohon Gwamnan Jihar Legas da ke a Epe.

Ko da shike Naija News ta fahimta da cewa mazauna yankin Epe sun hari hukumar da hanna su aiwatar da gurin su.

4. Diezani ta La’anci Hukumar EFCC a kan fada wa Gidanta

Tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke, ta kalubalanci Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kare Tattalin Arzikin kasa (EFCC), game da dauke kayan ado da kwalliya masu tsadar gaske na kimanin dala miliyan $40m.

Naija News Hausa ta gane da bayanin Diezani ne bisa wata kara wacce aka gabatar a madadin ta ta bakin lauyan ta, Farfesa Awa Kalu (SAN).

5. Abin da EFCC ta ce game da harin gidan Ambode

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kare Tattalin Arzikin kasa (EFCC), ta mayar da martani kan zancen cewa hukumar a ranar Talata, ta kai samame da hari a gidan tsohon gwamnan Legas, Akinwumi Ambode, a nan Epe.

Hukumar ta bayyana da cewa ba wai sun hari gidan Ambode ba ne don wata abu amma don binciken sa akan wata zargi.

6. Shugaba Buhari ya sake nada Femi Adesina, Garba Shehu da wasu a rukunin sa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Femi Adesina a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkar yada labarai a layin yanar gizo.

Naija News ta gane da cewa Shugaba Buhari ya kuma sake nada Garba Shehu a matsayin Mataimaki na musanman akan yada labarai a layin yanar gizo.

7. Mazauna Epe sun katange Hukumar Tsaro da shiga gidan Ambode

Wasu mazauna shiyar Epe sun tsaya kai tsaye da dakatar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kare Tattalin Arziki kasa (EFCC) daga kai hari gidan tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode.

Naija News ta tuno da cewa hukumar EFCC ta afka hari ne a gidan tsohon gwamnan a bisa wata binciken da suke kokarin yi akan gwamnatinsa a baya.

8. Yadda Sojojin Najeriyar ‘suka Taimaka mini da mafita daga tsari – Wadume

Fitaccen dan ta’adda da shugaban barayi a jihar Taraba mai suna Alhaji Hamisu Bala Wadume, wanda aka sake kama ranar Litinin, ya bayyana dalla-dalla game da tserewarsa.

Naija News Hausa ta tuna da cewa a ranar 6 ga watan Agusta da ta gabata, rundunar Sojojin sun hari Jami’an Tsaro sun a yayin da suke kokarin wucewa da Wadume akan hanyar Ibi zuwa Wukari.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 13 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 13 ga Watan Agusta, 2019

1. Gwamnatin Tarayya ta ba da Dalilin da yasa ba ta aiwatar da biyan kankanin Albashi ba

Bayan barazanar shiga zanga-zanga da kungiyar kwadago ta yi, Gwamnatin Tarayya ta danganta jinkirin aiwatar da sabon albashi mafi karancin ga Ma’aikata da sanadiyar wasu bukatu marasa manufa da kungiyar kwadago ta gabatar.

An bayyana wannan zancen ne a bakin, Richard Egbule, Shugaban Hukumar Albashi ta Kasa, da Hukumar Inshorar a yayin wata tattaunawa da yayi da NAN a ranar Litinin da ta wuce.

2. Shugabancin Kasa ta Bayyana Abinda Shugaba Buhari keyi Game da Rikicin Sojoji da ‘Yan Sanda

Shugabancin kasar ta bayyana da cewa akasin ganewa da imanin wasu a kasar na nunin cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai damu da rikicin da ya afku tsakanin jami’an ‘yan sanda da sojoji ba.

Ka tuna kamar yadda Naija News ta sanar a baya da cewa darukan sojojin Najeriya sun kashe wasu jami’an ‘yan sanda a jihar Taraba wadanda ke biye da wani jagoran ‘yan fashi, Alhaji Hamisu.

3. El-Zakzaky da Matar sa sun tashi daga Najeriya zuwa kasar Turai

Shugaban kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN), wanda aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Shaikh Ibraheem El-Zakzaky da matarsa, Zeenat, a daren ranar Litinin din nan, sun bar kasar zuwa Indiya don binciken lafiyar jikinsu.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa sun tashi zuwa India ne a kan jirgin Emirate daga filin jirgin sama ta Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

4. Dalilin da yasa ya zan dole ga EFCC ta Kama Buhari da Tinubu – Omokri

Reno Omokri, tsohon mai mataimaki ga hidimar aiki ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, ya ce ikirarin da Timi Frank ya bayar ya tabbatar da cewa ya karyata Jonathan.

Ya kara da cewa furucin Frank, tsohon Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC na kasa ya tabbatar da cewa tsohon Shugaba Jonathan mai Imani ne.

5. Abinda ya zan Dole da yi ga ‘Yan Najeriya  – Bola Tinubu

Jagoran jam’iyyar APC na kasa baki daya, shugaba Bola Tinubu, ya ce dole ne ‘yan Najeriya su sadaukar da kansu ga ci gaba da karuwar kasar.

Naija News ta gane da cewa Tinubu yayi wannan tsokaci ne yayin da yake zantawa da manema labarai bayan kammala sallar Eid-el-Kabir.

6. Abin da Shugaban Guinea ya fada wa Buhari game da Tinubu

Naija News Hausa ta fahimta bisa rahotannai da cewa daya daga cikin dalilin ziyarar shugaban kasar Guinea, Shugaba Alpha Conde ga Buhari ita ce neman dama ga Cif Bola Tinubu don maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2023.

Ka tuna da cewa Conde ya halara a garin Daura na jihar Katsina a karshen mako don ziyarar shugaba Buhari yayin da shugabannin kasashen Afirka biyu ke bikin zagayowar Sallar Eid-El-Kabir.

7. Rundunar Sojojin Najeriya ta Kori wani Jarumi don Lalata da wata Daliba Jami’a

Sunday Adelola, mai igiyar daukaka ta Lance Corporal ta sojojin Najeriya wanda aka kama da yi wa wata daliba makarantar Jami’a ta Adekunle Ajasin Akungba Akoko fyaden Dole.

Naija News ta fahimci cewa an mika Mista Adelola ga ‘yan sanda don bincike tare da gurfanar da shi nan take rundunar ta kore shi.

8. Kungiyar Kwadago ta Najeriya ta gabatar da sabon gargadu  ga Gwamnati

Kungiyar kwadago ta kasa (TUC) ta gargadi gwamnatin tarayya da ta daina jinkiri da biyan sabon albashi mafi karanci ga Albashin ma’aikatan Najeriya.

Shugaban TUC na jihar Ekiti, Sola Adigun, wanda ya yi wannan kiran, ya roki Gwamnatin Tarayya da kar ta kara ga jinkirtar biyan albashin, da kuma kada su wuce ranar Laraba, 14 ga Agusta 2019.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 9 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 9 ga Watan Agusta, 2019

1. Kotu ta Umarci EFCC da ta Kama Tsohon Shugaban INEC, Maurice Iwu

Babbar Kotun Tarayya da ke a Jihar Legas ta umarci Hukumar Yaki Cin Hanci da Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) da ta tsare tsohon Shugaban Hukumar gudanar da Zabe a Najeriya, Farfesa Maurice Iwu, har zuwa ranar Juma’a don sauraron karar tasa.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa a ranar Alhamis da ta gabata ne hukumar ta gurfanar da tsohon Shugaban Hukumar INEC bisa zargin ake da shi na karkatar da sama da Naira Biliyan 1.

2. Jam’iyyar APC ta Jihar Kogi ta Tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Simon Achuba

Mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba ya samu dakatarwa daga sashin jam’iyyar APC ta Jihar.

Naija News ta fahimci cewa Achuba, mataimakin gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, bai sami kyakkyawar alakar aiki tare da shugaban sa ba tun da aka zabe su tare.

3. Bazaka Iya Amfani da Cin Hanci ba Don Yaki da Cin Hanci da rashawa – Lauyan ya gayawa shugaba Buhari

Inibehe Effiong, daya daga cikin lauyoyin da ke neman a saki Omoyele Sowore, dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 daga tsare a hannun Jami’an tsaro don wata hidimar Zanga-Zanga.

Effiong ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da kin sauraren kukan ‘yan Najeriyar “duk da amfani da kudin masu biyar haraji don magance kamuwa da cutar kunne da yake da shi, a kasar Turai.”

4. Shugaba Buhari ya mayarda martani ga kisan jami’ai a jihar Taraba

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya umarci hedikwatar tsaron kasar da ta fara gudanar da bincike ta musanman da hanzari game da kisan jami’an ‘yan sanda uku da wani mutumi da sojoji suka kashe a Jihar Taraba.

Naija News Hausa ta sami tabbacin umarnin Buhari ne a wata rahoto da aka bayar daga hannun Babban Hafsan Hafsoshin na Sojojin Sama, Air Marshal Sadique Abubakar, ga manema labarai, bayan wata ganawa da shugaba Buhari ya jagoranta.

5. Gidan Majalisar Wakilai ta Mayar da Martani ga hukuncin Kotu akan Majalisar Jihar Edo

Majalisar wakilai ta yi Allah wadai da hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta bayar na hana Majalisar Dokoki da daukan mataki akan hidimar Majalisar Wakilai ta Jihar Edo.

Ka tuna cewa kotu ta hana Magatakardan Majalisar Dattijai, shugaban majalisar dattijai da kuma kakakin majalisar wakilai damar karbe ikon majalisar wakilan jihar Edo.

6. Ku gayawa Al’umar Najeriya inda Alhaji Hamisu yake –  ‘Yan Sanda sun kalubalanci Rundunar Sojoji

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tuhumi hukumomin Sojojin Najeriya da su bayyana inda sanannen dan fashin nan, Alhaji Hamisu Bala Wadume yake.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa ‘Yan Sanda sun furta hakan ne ga Sojojin Najeriya bayan ganin yadda aka kashe jami’an tsaron su guda Uku a Taraba da barin mugun Dan Fashin da gujewa.

7. Shugaba Buhari Ya kara Ganawa Da Shugabannin Tsaro A Abuja

A ranar Alhamis din da ta gabata, shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da shugabannin ma’aikatu inda aka yi masa jawabai kan yanayin rashin cikakken tsaro da ake fuskanta a kasar.

Bisa ganewar Naija News, ganawar ta fara ne a ofishin shugaban kasa a fadar gwamnatin da misalin karfe 10:30 na safiyar yau.

Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa

Jami’an tsaro sun kama wani da laifin soke kaninsa da Wuka har ga mutuwa

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutumi mai shekaru haifuwa 57, da suna Tijjani Yahaya da zargin soke kaninsa da wuka har ga mutuwa.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana da cewa marigayin, Aminu Mohammed ya mutu ne a lokacin da ake bashi kulawa a asibitin Murtala Mohammed Specialists Hospital, bayan da yayansa Tijjani ya soke shi da wuka.

A bayanin DSP Abdullahi, ya bayyana da cewa abin ya faru ne a ranar Jumma’a da ta gabata a missalin karfe 9:00 na dare, bayan da wata rashin jituwa ya auku tsakanin su Tijjani da Aminu.

Naija News Hausa bisa rahoton da aka karba ta fahimta da cewa marigayin da yayansa mazauna ne a shiyar unguwar Kofar Ruwa ta karamar hukumar Dala a Jihar Kano.

An bada haske da cewa wanda ake zargin ya soke kaninsa ne da wuka a kirjinsa a ranar 19 ga watan Yuli 2019, a misalin karfe Tara na daren ranar.

Jami’an tsaro sun gane da hakan ne bayan da suka karbi kirar kula a rukunin tsaro ta Dala Division da cewa wani mai suna Tijjani Yahaya da shekaru 57 ya soke kanin sa Aminu Mohd mai shekaru 20 ga haifuwa da wuka a kirji, a nan Makarantar Islamiyya ta Annandini Islamic school da ke a Kofar Ruwa, karamar hukumar Dala.

Jami’in tsaron ya bayyana da cewa lallai a haka, lallai an hanzarta da kai mutumin a asibiti don bashi kulawa, amma dai ya mutu a yayin hakan.

Ya kuma karshe da gabatar da cewa sun rigaya sun kame mai laifin, kuma kwamishanan tsaron jihar ya rigaya ya bayar da umarnin cewa a gabatar da karar ga rukunin hukumar da ke jagorancin halaye irin wannan.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hukumar Tsaron Jihar Ogun sun kame Fulani Makiyaya 3 da zargin kashe wani dan shekaru 40.