‘Yancin El-Zakzaky Baya A Hannun El-Rufai Yake ba – IMN Sun fada wa Gwamnatin Buhari

Kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wacce kuma aka fi sani da suna Shi’a, ta yi Allah wadai da bayanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa ‘yancin shugabanta, Ibrahim El-Zakzaky ya dangana ne a hannun gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.

Naija News ta tuno cewa yan Shi’a sun yi kiran a saki El-Zakzaky ne bayan sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore.

Amma a wata sanarwa da Gwamnatin Tarayyar Najeriya a karkashin shugabancin shugaba Muhammadu Buhari ta bayar, suna mai cewa sakin jagoran Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN) Ibrahim El-Zakzaky, ya dogara ne kawai ga gwamnatin jihar Kaduna.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wakilan Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da Shi’a a ranar Laraba da ta gabata sun halarci hidimar coci ta Kirsimeti a wasu sassan arewacin Najeriya.

A cocin daban daban na Advent, Samaru, Zariya, jim kadan bayan kammala hidimar, shugaban kungiyar, Farfesa Isa Hassan-Mshelgaru ya ce muhinmancin halartar wannan hidimar shine inganta soyayya, hakuri da fahimta a tsakanin yan Najeriya.

Kungiyar ‘Yan Shi’a Ta El-Zakzaky Sun Halarci Coci Da Bayar da Kyautannai A Ranar Kirsimeti

Wakilan Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da Shi’a a ranar Laraba sun halarci hidimar coci ta Kirsimeti a wasu sassan arewacin Najeriya.

A cocin daban daban na Advent, Samaru, Zariya, jim kadan bayan kammala hidimar, shugaban kungiyar, Farfesa Isa Hassan-Mshelgaru ya ce muhinmancin halartar wannan hidimar shine inganta soyayya, hakuri da fahimta a tsakanin yan Najeriya.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa wasu ‘yan Bindiga Sanye Da Kayan Sojoji sun sace yara uku na Mista Obi a Jihar Kaduna

Mugun yanayi ya sanya wani dan kasuwa a Kaduna, Christian Obi kuka da hawaye a ranar Alhamis bayan da wasu ‘yan bindiga sun sace yaransa uku.

Mutumin yayin da yake zantawa da manema labarai a gidansa da ke Sabon Tasha, Kaduna, ya ce ya ga wadanda suka sace yaran ne sanye da kayan sojoji a cikin gidansa amma sai ya shiga buya.

Kotu Ta Umurci Hukumar DSS Da Ta Mayar Da El-Zakzaky Ga Cibiyar Horon Al’umma

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta ba da umarni ga hukumar DSS da ta dauki shugaban IMN, kungiyar ci gaban Musulunci da aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da uwargidansa Zeenat daga tsarewar ma’aikatarta zuwa cibiyar gyara halin al’umma ta jihar Kaduna.

Alkalin kotun ya bayyana da cewa yin hakan na da kyau don inganta da samun saukin saduwa da shi.

Wakilin kamfanin dilancin labarai na TVC, Tesem Akende, ya ce a duk lokacin da aka gabatar da zancen, hukumar kan tsauya zancen don tabka magudi a babban birnin jihar kamar yadda aka saba yi a koyaushe a duk lokacin da za a fara sauraron karar.

A haka an sanar da daga karar zuwa 6 ga Fabrairu na shekara mai zuwa don sauraron kara.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da ya sa har yanzu ba a biya Albashin NPOWER Na Watan Oktoba da Nuwamba ba.

El-Zakzaky: Kalli Bidiyon Lokacin da aka yi Munsayar harin Wuta da ‘Yan Shi’a a Kaduna

Bisa Umarnin da IGP Mohammed Adamu ya bayar da cewa a kama dukan shugabanan kungiyar Ci Gaba da Harkan Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da lakabi ‘Yan Shi’a, Kungiyar basu daina da ayukan su ba.

Ka tuna an gargadin kungiyar da zancen hidimar Ashura da suka shirya da yi a yau Talata,10 ga Satumba 2019, amma membobin kungiyar a Jihar Kaduna sun kauracewa wa gargadin da aka bayar, sun kuma fita zanga-zangar su a yayin da Jami’an tsaro suka tsare su har ga harbin bindiga.

Kalli Bidiyon a Kasa;

IMN: ‘Yan Shi’a sun gabatar da ranar Hidimar su duk da Hukuncin Kotu

Kungiyar Ci Gaban Harkan Musulunci ta Najeriya ta Kaurace wa Hukuncin Kotu

Duk da sammaci da Kotun Najeriya ta gabatar, Kungiyar Ci gaban Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wacce kuma ake wa lakabi da Shi’a, ta tsayar da ranar Talata don bikinta na Ashura.

Naija News ta fahimci cewa hidimar Ashura wanda kuma ake kira da ranar Ashura, rana ce ta goma ga Muharram, watan farko a kalandar Musulunci.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Babban Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya  (IGP), Mohammed Adamu ya ba da umarni ga dukan rukunin ‘yan sanda a duk jihohin Najeriya da su fara kame shugabannin kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), da aka fi sani da Shi’a.

IGP Adamu ya bayyana hakan ne bisa umarnin da aka wallafa daga Hedikwatan Rundunar Tsaron zuwa ga dukan Rundunar ‘Yan sanda na Jiha, a ranar 30 ga watan Agusta, 2019, wanda kuwa aka yi gargadi da rashin jinkiri da bin umarnin.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 15 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 15 ga Watan Agusta, 2019

1. Buhari ya sanya hannu kan dokar canza sunan Ofishin fursuna na Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a wata doka da ya baiyana canza sunan gidan yari na Najeriya daga Nigerian Prison Service zuwa to Nigerian Correctional Service.

An baiyana hakan ne a wata sanarwa da aka bayar daga hannun Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa a harkan gidan Majalisa, Mr. Ita Enang, a ranar Laraba da ta gabata.

2. El-Zakzaky Ya Ki Amincewa Da Likitocin da bai San da su ba

Naija News ta fahimci shugaban kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) da aka fi sani da suna Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kin karban likitoci da bai san da su ba.

Rahoton da aka bayar ya baiyana da likitocin sun bambanta da wadanda aka sanya ga El-Zakzaky kamin barin sa kasar Najeriya ranar Litinin da ta gabata.

3. EFCC ta gurfanar da Surukin Atiku Abubakar

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) sun kame Abdullahi Babalele, suruki ga tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma dan takarar Shugaban kasa daga jam’iyyar Dimokradiyya, a babban zaben shekarar 2019, Atiku Abubakar.

Naija News ta fahimci cewa, an gurfanar da Babalele ne a ranar Laraba a gaban Mai shari’a Nicholas Oweibo a wata babbar kotun tarayya da ke a Legas, kan zargin kudade da aka fyauce na kimanin dala $140,000 a yayin babban zaben shekarar 2019.

4. Borno Ta Bayar Dajin Sambisa ga Gwamnatin Najeriya don kafa tsatsan Ruga

Gwamnatin Jihar Borno a karkashin jagorancin gwamna Babagana Umara, ta bayar da dogon dajin Sambisa da ake tsoro ga gwamnatin tarayya don shirin sasanta rikicin RUGA.

Gwamnan ya kuma umarci hukumomin tsaro da suka hada da Rundunar Tsaron Civil Defence (NSCDC), Agro Rangers da mafarauta da su tabbatar da tsarin dajin.

5. Buhari ya Ziyarci sansanin IDP A Katsina

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya ziyarci karamar hukumar Batsari domin nuna juyayi ga ‘yan gudun hijirar a cikin yankin.

Naija News Hausa ta fahimci cewa Batsari na daya daga cikin bangarorin takwas na karamar hukumar jihar da ke fuskantar hare-haren da ayyukan masu sata da garkuwa da mutane a jihar Katsina.

6. Asibitin Indiya ta Amince Da Bukatar El-Zakzaky

Asibitin Indiya da ke jagorantar kulawa da jagoran Harkar Ci gaban Musulunci na Najeriya (IMN), Ibrahim El-Zakzaky, sun amince da barin sanannun likitoci ga El-Zakzaky da kulawa da shi.

A cewar PRNigeria, wakilin kungiyar kare hakkin dan adam ta IHRC, ya ce an warware matsalar mahawara kuma El-Zakzaky ya ci gaba da karbar magani tare da Likitocin da aka fara bayarwa a gareshi.

7. Obasanjo Ya baiyana Abubuwa 3 Wadanda Zasu Inganta Najeriya

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya gano da gabatar da wasu matakai ta musanman da zasu iya inganta da karfafar da Najeriya.

Tsohon shugaban kasar a mulkin soja da na dimokiradiyya ya bayyana a wata babban taron wake-waken kasa da cewa Yabo, Addu’o’i da Ibada ne zasu iya inganta da gina kasar. Ya kuma bayar da tabbacin hakan daga Littafi Mai Tsarki kamar yadda take a lokacin Yehoshafat,’ (II Labarbaru 20:22).

8. An gurfanar da Sojan Najeriya da laifin Fyade da Dalibar Jami’a

An gurfanar da Lance Corporal Sunday Awolola, jarumin soja da aka tsige daga tsaron kasa bisa zargin yiwa wata daliba mai digiri 300 a jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba Akoko, AAUA, Fyaden Dole a jihar Ondo.

Naija News ta gane da cewa an gurfanar da shi ne a ranar Laraba da ta wuce a Kotun Majistare da ke zaune a Akure, babban birnin jihar Ondo.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 14 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 14 ga Watan Agusta, 2019

1. El-Zakzaky Ya Isa kasar Indiya Don Binciken Lafiyar Jikin sa

Jagoran Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), Sheik Ibrahim El-Zakzaky a ranar Talata ya sauka a Delhi, babban birnin kasar Indiya don neman karin lafiya.

Likitocin kasar Indiya sun karbe shi da kuma shigar da shi a cikin asibiti.

2. Shugaba Buhari ya baiwa Babban Banki CBN Sharadi Kan shigar da Abinci

Shugaba kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da daina ba da musayar kudin kasashen waje don shigo da abinci daga waje.

Naija News ta fahimci cewa an sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu.

3. ‘Yan Jam’iyyar APC ne Kadai zan nada a cikin Karatuna – Oyetola

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola ya bayyana cewa membobin jam’iyyar All Progressives Congress ne kawai za su yi zami jagoranci da wakilci a rukunin shugabancin sa.

Gov. Oyetola, a yayin da yake zantawa da manema labarai a Iragbiji, ya bayyana cewa duk da hakan ba zai yi watsi da ra’ayoyi daga ‘yan majalisar adawa ba, idan har zasu taimaka wa jihar ta zama da alheri.

4. Shugaban PDP Ya Bayyana Tallafi Ga RUGA Da Aka Kafa, tare da Dalilai

Babban jigon jam’iyyar Dimokradiyya, PDP, babbar Jam’iyyar adawar Najeriya, ya baiyana goyon baya ga kafa shirin karkara ta RUGA) da Gwamnatin Tarayya ta shirya da yi.

Naija News ta fahimci cewa Ciyaman, Kwamitin Amintattu (BOT) na PDP, Sen. Walid Jibrin ne ya sanar da hakan a ranar Talata da ta gabata.

5. Uwargidan tsohon Gwamnan Jihar Kwara ta musanta hada kai ga magudin kudi  Naira Biliyan N2bn

Lanre Bello, Babban Darakta na Leah Group ta mayar da martani game da wani labari da ake zargin ta dashi, mai cewa Uwargidan Tsohon Gwamnan Jihar Kwara na da halaka da cin hancin N2bn a asusun Kasuwancin kananan Hukumomi da Matsakaici (SMED).

Wannan ya bayyana ne kamar yadda wasu gidan labarai (ba da Naija News ba) suka yi jita-jitan cewa wata kila Hukumar Yaki da Cin Hanci da kare tattalin arzikin kasa (EFCC) zata kama Lanre akan zancen kudi Biliyan 2bn.

6. Gwmanan Jihar Legas, Sanwo-Olu mikar da jerin Ministocin Zuwa Ga Majalisar Dokoki ta Jiha

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas a ranar Talata da ta wuce, ya mika jerin sunayen wadanda aka zaba domin nada ministocinsa ga majalisar dokokin jihar.

Naija News Hausa ta kula da cewa wannan Jerin itace na biyu bayana ‘yan makwanni hudu a baya da Gwamnan ya aikar da rukunin farko domin tantancewa.

7. Zargin Fyade: PFN na shirye Don Bada rahoto akan Fasto Biodun Fatoyinbo

Bayan zargin fyade da aka yi wa babban Fasto na Ikilisiyar CommonWealth of Zion Assembly (COZA), Biodun Fatoyinbo, kungiyar hadayyar Fentikostal ta Najeriya ta bayyana cewa za ta gabatar da rahotonta kan binciken zargin fyade a wannan makon.

Ka tuna cewa Hadadden kungiyar Kristocin Najeriya (CAN) ta baiwa PFN makwanni biyu don gabatar da rahoto kan zargin fyade da aka yiwa Fasto Biodun Fatoyinbo ta hannun Misis Busola Dakolo.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 2 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 2 ga Watan Agusta, 2019

1. Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da rufe karar su a Kotun Koli

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar shugabancin kasa (APC) sun rufe kare karar su a gaban kotun daukaka kara ta Shugaban Kasa.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne a sanarwan Kungiyar lauyoyi ga Buhari, karkashin jagorancin Wole Olanipekun (SAN) da kuma jagorantar lauya a jam’iyyar APC, Lateef Fagbemi, da cewa suna sanar da niyyar rufe bakin su yayin da suka gurfana a gaban kotun a ranar Alhamis.

2. An dakatar da Shugaban Karamar Hukuma Don boye ‘Yan bindiga

Majalisar Wakilai ta Jihar Zamfara ta dakatar da Ciyaman na Karamar Hukumar Maradun, Ahmad Abubakar saboda laifin raunana tsaro a Jihar.

Naija News Hausa ta gane da cewa hakan ya biyo ne bayan wata takardar karar da majalisar ta gabatar kan Shugaban karamar hukumar, wanda wasu mutane shida da ke zama a yankin suka sanar ga Majalisar Jihar.

3. Diyar El-Zakzaky ta mayar da Martani ga zancen dakatar da  Zanga-zanga

Diyar Ibraheem El-Zakzaky, shugaban kungiyar cin gaban harkan musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da Shi’a, Suhaila Zakzaky ta dage cewa dage da cewa kungiyar ”yan shi’a za ta ci gaba da zanga-zangar ta har sai an sako mahaifinta.

Suhaila ta sanar da hakan ne a yayin da ta ke mayar da martani ga wata sanarwa daga Ibrahim Musa, shugaban kungiyar watsa labarai ga IMN da cewa, an dakatar da zanga-zangar kungiyarsu a birnin Abuja.

4. Rayuwata na cikin Hadari – Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Achuba Ya sake daga muryar sa

Mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba ya sake tayar da murya game da barazanar da ake yiwa rayuwarsa.

Naija News ta tuno a baya da cewa Mista Achuba a farkon wannan shekarar, a watan Fabrairu ya zargi maigidan nasa da yin barazanar kashe shi. Kazalika a wata hira a ranar Alhamis da ta gabata da manema labarai a gidan sa da ke a Lokoja, Mataimakin gwamnan ya bayyana da cewa gwamna Yahaya Bello ya bada dama ga ‘yan bindiga don kashe shi.

5. Abin da kungiyar neman yanci ga Atiku suka fada bayan da Buhari da APC ta rufe kare karar sua kotu

Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 daga jam’iyyar PDP ya mayar da martani ga matakin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari suka dauka na janye kansu daga kare karar da ake da su a Kotun shugaban kasa.

Paul Ibe, mai taimaka wa Atiku ga yada labarai a yanar gizo, ya yi amfani da shafin Twitter ranar Alhamis don bayyana ra’ayinsa game da hukuncin da APC da Buhari suka yanke.

6. An Kama wani Mutumin Saboda samar da Jabun Takaddar yancin Jagoranci da kuma Sa hannun Shugaban INEC

Rundunar Jami’an tsaro da shiyar jihar Legas ta gurfanar da wani mutum da aka sani da suna Toluwalope Akanni bisa wata zargin karkatar da takardar yancin jagoranci ta Hukumar Zabe da kuma dagewa a matsayin zama dan Majalisar Wakilai.

An zargi mutumin mai shekaru 30 da laifin samar da sanya hannu iri ta shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

7. Sowore na shirye don jagorar wata Zanga-Zangar Juyi

Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 daga Jam’iyyar African Action Congress a babban zaben da ya gabata, ya yi kirar goyon baya ga Matasan Najeriya don kadamar da zanga-zanga.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa zanga-zangar zata kasance ne don neman juyin zamantakewa a kasar Najeriya, kamar yadda Sowore ya gabatar da cewa zanga-zangar zata kasance ne tun daga ranar 5 ga Agusta, 2019.

8. Shugabancin Kasa Ta Bayyana Dalilin da yasa Har Yanzu ba a gabatar da Rukunin shugabancin Buhari ba

Shugabancin kasar Najeriya ta bayyana cewa har yanzu majalisar dattawa ba ta yi magana da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba akan  kammala tantance wadanda aka bayar da sunayen su ga matsayin ministoci.

Ka tuna da cewa majalisar dattijai a ranar Talata da ta wuce ta kammala gwaji da tantacewar jerin sunayen da shugaba Buhari ya mika ga Majalisar don tabbatar da nadinsu a mukamin ministocin jumhuriyyar tarayyar Najeriya.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a NaijaNews.Com

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 31 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 31 ga Watan Yuli, 2019

1. Majalisar Dattijai ta Tabbatar da Duk Ministoci 43 da Buhari ya mikar da sunan su

Majalisar dattijan Najeriya ta tabbatar da nadin dukkan ministocin 43 da shugaba Muhammadu Buhari ya mikar da ita ga majalisar a kwanar baya.

Wannan ya biyo ne bayan cikar tsawon kwanaki biyar da Majalisar ke tantance jerin sunayan da shugaba Buhari ya bayar.

2. Shugaba Buhari ya bayar da takardun shaida ga Kotun Shugaban Kasa

A ranar Talata da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da takardu 26 a yayin da yake zancen dage ga nasarar sa bisa hidimar zaben shugaban kasa ta 2019.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa takaddun sun kunshi kwafin takardun shaidar sa na ilimi, wanda ya kunshi tabbataccen kwafi (CTC) na Takaddar Sakamakon jarabawawr Jami’ar Cambridge.

3. Lawan Ya Bayyana Shugabannin Kwamitin Majalisar Dattawa

Shugaban Majalisar Dattawa na Najeriy, Ahmad Lawan a ranar Talata, 30 ga Yuli ya ba da sanarwar shugabannin majalissar dattawa ta tara (9).

Ya sanar da hakan ne yayin zaman majalissar kafin Sanatocin su ci gaba da hutunsu ta shekara da shekara da aka daga zuwa ranar 24 ga Satumbar, 2019.

4. Majalisar Dattijai Ta Ba da Umarni ta musanman ga Obaseki Kan Rikicin Majalisar Edo

Majalisar dattijai a ranar Talata ta umarci gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki da ya fitar da wata sabon sanarwa domin rantsar da ”yan majalisar dokokin jihar.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa akwai matsaloli da majalisa jihar ke fuskanta akan jagorancin jihar.

5. Kotun Koli ta gabatar da ranar sauraron karar da Atiku yayi wa INEC

Kotun koli ta tsayar da ranar 20 ga watan Agusta, 2019, don sauraron karar da jam’iyyar PDP, babban jam’iyyar adawa ta Najeriya da dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar, akan  kalubalantar zaben watan Fabrairu.

Naija News ta tuno da cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa da dan takaran kujerar shugaban kasar a baya y bukaci hukumar INEC da binciken na”urar  da aka yi amfani da ita a zabe baya.

6. Kotun Koli ta kori memba a Majalisar Wakilai ta Tarayyar APC

A ranar Talata da ta wuce, Kotun koli ta tsige Mustapha Usman, dan majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Yola ta Kudu da Yola ta Arewa a Tarayyar Girei na jihar Adamawa.

Naija News ta gane da cewa Usman ya wakilci mazabarsa a karkashin Jam’iyyar APC a gidan majalisa.

7. Majalisar dattijai ta dage sauraron karar har zuwa ranar 24 ga Satumba

Majalisar dattijan Najeriya a ranar Talata sun fara hutunsu na shekara da shekara bayan tantance sunayen ministocin da Shugaba Muhammadu Buhari ya mikar a garesu.

Ka tuna da cewa a baya Shugaba Buhari ya aikar da jerin sunayen mutane 43 don tantacewa da gabatar da su a matsayin Ministoci a kasar.

8. Gwamnatin Tarayya ta hana ‘yan Kungiyar IMN (Shi’a) da yin ayukan su a kasar

Gwamnatin tarayyar Najeriya a jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta sanarwar da hana Kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN), da aka fi sani da ‘yan Shi’a da tafiyar da ayukan su, musanman zanga-zanga.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa sanarwan da shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bayar a wata ganawa da manema labarai a birnin Abuja, ranar Talata da ta wuce.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNews.Com

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 30 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 30 ga Watan Yuli, 2019

1. Boko Haram: Shugaba Buhari Ya mayar da martani game da mutane 60 da aka kashe

Bayan harin da aka yi wa masu makoki a wani taron jana’izar da ya gudana a jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 60, Shugaba Muhammadu Buhari ya la’anci da wannan matakin.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya bayar ta hannun mai magana da yawun sa, Garba Shehu, ya fada da tabbacin cewa za a kama ‘yan ta’addan da suka aikata kisan.

2. Rikicin Majalisar Edo: Obaseki ya ki bayar da sabon sanarwar

Gwamna Godwin Obaseki a ranar Litinin ya ce ba zai fitar da wata takaddar shelar sanarwa ba domin kafa majalisar dokokin jihar Edo ta bakwai.

Ya sanar da hakan ne yayin da yake mayar da martani kan wata rahoton da Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar na umartan sa da gabatar da sabon shirin.

3. Abin da Dino Melaye ya fada Game da Tantancewar Ministoci

Sanatan da ke wakilcin maharabar yamma ta Kogi, Dino Melaye ya kalubalanci hidimar tantance sunayen ministocin da Majalisa ke yi ga marasa gabatar da jakar su.

Naija News ta fahimci cewa Sanata Dino a yayain da yake mayar da martani ga hidimar tantancewar, ya bayar da cewa tantancewar sunan Ministocin ya kasance da sauki a saboda abin bai cika da gaskiya ba bisa tsari.

4. Biafra: ‘Yan Kungiyar IPOB sunn bayyana lokacin da shugabansu Nnamdi Kanu zai dawo Najeriya

Kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) sun gabatar da cewa shugabansu Mazi Nnamdi Kanu zai dawo Najeriya nan ba da jimawa ba.

Mai magana da yawun kungiyar, Emma Powerful ya fada da cewa Kanu zai dawo Najeriya don shirin tsarafa da kuma tabbatar da kafa Biafra, “a yayin da wannan na cikin dalilin da yayi tafiya.

5. Yadda Aregbesola ya ba ni Albashinsa Shekaru 7 da suka gabata – Sanata Abbo

Sanata Elisha Ishaku Abbo, Sanata da ke wakilcin yankin Arewacin Adamawa a Jam’iyyar PDP, ya bayyana da cewa tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya taba tallafa mashi da albashin sa shekaru bakwai da suka gabata don tsayawa takara.

Dan majalisa ya bayyana wannan zancen ne a yayin da ake tantace jerin sunayan Ministoci da shugaba Buhari ya baiwa ‘yan majalisa.

6. INEC ta ki gabatar da shaidu don kalubalantar Jam’iyyar PDP

Hukumar gudanar da hidimar zaben Najeriya (INEC), ta sanar ga Kotun kara ta shugaban kasa da ke a birnin Tarayya, Abuja da cewa, ba zasu yi kira ga wani shaida ba kamar yadda jam’iyyar PDP ke bukata da su.

Naija News ta fahimci cewa Lauyan INEC, Yunus Usman (SAN) ne ya sanar da hakan a lokacin da aka bayyana a kotun da gabatar da hukunci akan karar.

7. Kotu ta sake daga sauraron takardar neman belin El-zakzaky har zuwa 5 ga watan Agusta

Babbar Kotun Jihar Kaduna ta dage sauraron karar da ake yi ga shugaban kungiyar ‘yan Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky, don neman beli daga tsarewa.

Naija News ta fahimci cewa Mai shari’a Darius Khobo ya yi alkawarin gabatar da hukunci game da karar a ranar Litini 5 ga watan Agusta 2019.

8. NLC taki amincewa da Nadin Ngige A Matsayin Ministan Kwadago

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari da cewa kada sake nada Dokta Chris Ngige a matsayin Ministan kwadago da samar da ayyuka.

Naija News ta gane da cewa Kungiyar kwadago ta Najeriya ta dade da bayyana rashin amincewa da Ngige a matsayin shugaban ‘yan kwadago tun jagorancin sa ta farko a matsayin Minista.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a NaijaNewsHausa