Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 19 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 19 ga Watan Nuwamba, 2019

1. INEC ta ayyana wanda ya lashe zaben gwamnan Kogi

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Litinin, ta bayyana sakamakon karshe da kuma wanda ya yi nasara a zaben gwamna na Kogi na shekarar 2019.

Jami’in hukumar INEC da ya jagoranci hidimar zaben gwamnan da ta majalisa, Farfesa Ibrahim Umar Garba, ya bayyana sakamakon, a ranar Litinin, 18 ga Nuwamba a cibiyar tattara kuri’u da ke a Lokoja, babban birnin jihar bayan an samu sakamako daga dukkan kananan hukumomin.

2. Isah Almasihu zai Kalubalanci Yanayin Najeriya Idan Da A Ce Zai Kasance anan – Obasanjo

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, yayin da yake magana kan halin da Najeriya ke ciki, ya bayyana cewa idan har Annabi Isa zai kasance a wannan kasar a wannan lokacin, zai yi korafi kan yadda masu iko ke tafiyar da mulkin kasar.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wajen taron shekara da shekara ta karo na 64 na cocin Foursquare Gospel Church da aka yi a harabar cocin a kan Shiyar Lagos-Ibadan Expressway, Ajebo, Jihar Ogun.

3. Abin da Jonathan ya ce Bayan INEC ta ayyana Lyon da lashe zaben Gwamna a Bayelsa

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya taya dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), David Lyon murnar nasarar lashe zaben jihar Bayelsa.

Naija News ta rahoto cewa Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ayyana David Lyon a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnonin Bayelsa wanda aka yi Asabar, 16 ga Nuwamba 2019.

4. Wada ya Mayar da Martani Bayan da INEC ta Gabatar da sanarwar lashe zaben Kogi ga APC

Dan takarar gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Musa Wada, ya nuna rashin gamsuwarsa da sanarwan Hukumar Zaben Kasa (INEC) saboda yadda aka gudanar da zaben na Jihar Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a ranar Litinin, ta ayyana sakamakon karshe da kuma sanar wanda ya yi nasara a zaben gwamna na Kogi na 2019.

5. Gobarar Motar Tanki Ya Tafi da Rayuka 5 a Jihar Kogi

Rahoton da ke isa ga Naija News daga manema labarai ya bayyana da cewa a kalla mutane biyar suka mutu, wasu kuma da raunuka yayin da motar tankin da ke dauke da man fetur rutsa da wasu motoci cikin Kogi.

A haka wannan al’amarin ya sanya mutanen Felele da ke a karamar Hukumar Lokoja cikin zaman makoki da jinya bayan a kalla mutane biyar ne aka ruwaito sun mutu sakamakon hatsarin da ya afku da motar tankin.

6. Shugaba Buhari Yayi Taron Siri da Oshiomhole, Gwamnonin APC da Sauransu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin da ta wuce ya gana da shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, a fadar shugaban kasa, Abuja.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa an gudanar da taron ne da kofa kulle.

7. Dubi Dalilin da yasa Timi Frank ya nemi Uche Secondus Da Neman Afuwa ko Yayi Murabus

Tsohon Mataimakin Kakakin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Timi Frank, ya yi kira ga Shugaban neman zabe ga Jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus da Kwamitin Ayyuka na Jam’iyyar da su nemi afuwa ko su yi murabus da matsayinsu sakamakon asarar Jam’iyyar a zaben Jihar Bayelsa a watan Nuwamba 16.

Frank ya bayyana hakan ne yayin da yake taya murna ga zababben gwamnan jihar Bayelsa, David Lyon.

8. An Kame Tsohon Ofisan Janara, Adoke a Dubai

Kungiyar ‘yan sanda ta kasa da kasa ta kama tsohon babban Ofisan Tarayya da kuma ministan shari’a ga Najeriya, Mista Mohammed Bello Adoke (SAN) a Dubai.

Naija News ta fahimci cewa hakan ya faru ne da babban Lauyan, wanda a isarsa Dubai a ranar Litinin, 11 ga Nuwamba, don shirin duba lafiyar jikinsa aka kame shi, sannan aka tsare shi.

9. Amurka, Burtaniya, Tarayyar Turai sun yi Allah Wadai da Hukuncin zaben Bayelsa da Kogi

Kasar Amurka, Burtaniya da Tarayyar Turai (EU) sun yi Allah wadai da mummunan tashe-tashen hankula da aka samu yayin zabukan gwamnonin Bayelsa da Kogi.

Naija News ta tunar da cewa Hukumar Zaben Kasa (INEC) ce ta gudanar da zaben gwamnonin Bayelsa da Kogi a ranar Asabar, 16 ga Nuwamba da ta gabata.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 18 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 18 ga Watan Nuwamba, 2019

1. INEC ta Dakatar Da Sanar da Sakamakon Zaben Gwamnonin Kogi

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Lahadi ta sanar da cewa ta dakatar da sanarwar sakamakon zaben gwamnoni na ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi.

Wannan sanarwan an bayar da ita ne a bakin Babban Ofisan da Shugaban Hukumar INEC ta Jihar, wanda ke jagorancin hidimar zaben.

2. Tsoracewa A Yayin da INEC ta Fara Bayyana Sakamakon zaben Bayelsa

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka gudanar ranar Asabar.

Naija News ta fahimci cewa an jinkirta ne da sanar da sakamakon wanda ada aka shirya da farawa a karfe 10 na safiyar ranar Lahadi a cibiyar Farfesa Mahmood Yakubu.

3. Fayose ya Kalubalanci zaben Jihar Kogi da Bayelsa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya koka da sakamakon zaben gwamnonin jihar Kogi da na jihar Bayelsa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa duka zabukan da suka gudana a ranar Asabar sun kasance da rikice-rikice da kuma magudi.

4. Dalilin da yasa Membobin Edo na APC ke son Obaseki ya fita – Airhavbere

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo, Charles Airhavbere, ya ba da dalilan da suka sa membobin jam’iyyar ke son tsige Gwamna Godwin Obaseki.

A yayin da yake zartawa da manema labaran NAN a ranar Lahadi, tsohon mai neman takarar gwamna a Edo ya zargi Godwin Obaseki da kin sauraren muryar dalilai.

5. Abinda aka ga Yahaya Bello na yi yayin da INEC ke sanar da sakamakon zaben Kogi

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka hango Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a hotuna tare da mukarraban sa a Lokoja, babban birnin jihar, yayin da suke shan shayi da nishadewa.

Ka tuna kamar yadda Naija News ta sanar, ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba ne Hukumar Zabe ta gudanar da zaben Gwamnonin jihar Kogi.

6.  Ban Amince da Sakamakon Zabe ba – Musa Wada ya Kalubalanci Hukumar INEC

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.

Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.

7. Zaben Kogi: INEC ta ayyana ma’aikata 30 da suka Bata

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC), ta bayyana jami’anta 30 da suka bace a zaben gwamnoni da aka yi a Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta fahimta da cewa mutane 30 din da suka bata suna cikin malaman zabe da aka dauka don hidimar zaben zaben gwamnoni na ranar Asabar a jihar Kogi, arewa maso-tsakiyar Najeriya.

8. Kotun daukaka kara ta Soke Dan Jam’iyyar PDP a Majalisa

Kotun daukaka kara da ke zaune a Owerri ta tsige dan majalisa mai wakiltar mazabar Isiala Mbano / Onuimo / Okigwe da ke jihar Imo a majalisar wakilai, Obinna Onwubuariri.

Da yake yanke hukuncin a ranar Asabar, shugaban kwamitin, Mai shari’a R.N Pemu, ya bayyana da cewa nasarar Onwubuariri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a watan Fabrairu ya kasance ne da sabawa dokar zaben kasa kamar yadda aka ayyana tun shekarar 2010.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

APC: Hukumar INEC ta Gabatar da Mai Nasara ga Zaben Jihar Bayelsa (Kalli Yawar Kuri’u da ya kai shi ga Nasara)

INEC ta ayyana David Lyon na dan takarar APC a zaben Bayelsa

Hukumar da ke gudanar da hidimar zabe ta Kasa (INEC), ta ayyana David Lyon, dan takara daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC),  jam’iyyar da ke mulkin Najeriya, a matsayin wanda ya yi nasara da lashe zaben Gwamnonin Bayelsa.

Naija News ta samu tabbacin rahoton nasarar Lyon ne a matsayin wanda ya lashe zaben Bayelsa ta hannun shugaba da jagoran hidimar zaben jihar, Mataimakin shugaban jami’ar Benin, Farfesa Faraday Orunmuwese, a safiyar Litinin, 18 ga Nuwamba.

Kamfanin Dilancin Labarai ta Naija News Hausa ta fahimci cewa hukumar INEC ta a jagorancin Farfesa Orunmuwese ta mayar da dan takarar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Bayelsa da ya fito takara bayan da ya sami mafi yawan kuri’u a zaben.

Rahoton ya bayyana Lyon da samun yawar kuri’u 352,552 da ya kaishi ga kayar da abokan karawarsa da kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, Duoye Diri, wanda ya sami yawar kuri’u 143,172.

Wannan sakamakon zaben da rahoton nasarar David Lyon ya tabbatar da jihar Bayelsa a zaman jihar APC, musanman sake lashe zaben Jihar a wannan karo kuma.

Kogi: Kalli Yawar Kuri’u Da Yahaya Bello ya baiwa PDP a Runfar Zaben sa

Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello ya ci nasarar da yawar kuri’u a runfar zaben sa a zaben yau Asabar.

Bisa rahoton da Naija News ta karba, Bello ya lashe dukan mazabar jam’iyyar sa a kananan hukumomin Jihar Kogi.

Kalli tsarin yadda aka Bello ya sami kuri’u a mazabar sa ta PU 11, Okene-Eba/Agasa/Ahache Ward, karamar hukumar Okene.

Sakamakon Zaben Runfar da Jam’iyoyi a kirga ta farko.

APC: 546

SDP: 0

PDP: 0

Kuri’ar da ba a amince da ita ba: 1

Sakamakon Zaben Runfar da Jam’iyoyi a kirga ta biyu

APC: 716

SDP: 0

PDP: 0

Ko da shike dai, Hukumar INEC ne ke da tabbaci da ikon bayar da sakamako ta karshe kan wannan zaben.

APC/PDP: ‘Yan Ta’adda Sun Yi Fada Kan Kayakin Zabe a Jihar Bayelsa

Fada ya Tashi a Yayin Hidimar Zaben Gwamna a Jihar Bayelsa

Masu fafutukar siyasa sun yi karo da juna game da yadda za a samar da kayayyakin zabe zuwa rumfunan zabe a Otueke, karamar hukumar Ngbia na jihar Bayelsa.

Naija News ta ba da rahoton cewa lamarin ya faru ne a Cibiyar Rajista ta INEC (RAC) a cikin Makarantar Sakandaren Unguwar Otueke da karfe 10.45 na safe inda ‘yan tawayen da ke dauke da makamai suka watsar da ‘yan jaridu da masu sa ido kan zaben.

Matasan sun tayar da fada ne a yayin gardama da rashin jituwa game da inda za a kai wasu kayan zaben.

Wani jami’i da kuma ma’aikacin hukumar INEC, wanda ya zanta da ‘yan jaridar The Punch ya danganta rade-radin rarraba kayayyakin zaben akan tsanancin wasu matasa a cikin yankin.

“Ku zargi matasan yankin da jinkiri da sakaci wajen rarraba kayan zaben. Kayakin zaben sun isa runfar zabe ne da misalin karfe 11:30 na safe bisa agogo, amma matasan yankin sun nace kada mu tafi da kayaki.”

APC/PDP: Kalli Lokacin Da Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Ya Isa Mazabarsa

A Yayin da Hidimar zaben Gwamnoni a Jihar Kogi ke gudana, Gwamna Yahaya Bello ya isa Runfar Zabensa don jefa nasa kuri’ar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dan jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP da kuma dan takarar kujerar Sanata a ‘Kogi West Senatorial’ a zaben na ranar Asabar, Dino Melaye, ya yi ikirarin cewa an riga an sanya tsare-tsare domin kadamar da makirci a zaben Jihar ta ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.

Dino ya jadada da cewa lallai akwai shirin don sayar da zaben gobe ga gwamnan jihar, Yahaya Bello da kuma Smart Adeyemi, dan takaran gidan Majalisa.

Zaben Gwamnoni: An Fara Rabar da Kayan Zabe a Jihar Bayelsa (Kalli Hotuna)

Hukumar Gudanar da Hidimar Zabe ta Kasa (INEC), a yau Juma’a ta fara rabas da kayakin zabe don zaben Gwamnonin Jihar Bayelsa.

Ka tuna da cewa Naija News ta ruwaito a baya da cewa INEC ta sanya ranar Asabar, 16 ga Nuwamba, 2019, don zaben Gwamnoni a Jihar Bayelsa da Kogi.

David Lyon na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Sanata Douye Diri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) sune manyan ‘yan adawar juna a hidimar zaben Bayelsa.

Dubi hotunan rarraba kayan zaben a kasa kamar yadda jaridar The Punch ta samar:

APC/PDP: An Bada Hutun Aiki ga Al’ummar Jihar Kogi don Zaben Ranar Asabar

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayar da hutu ga mai’aika, ‘yan makaranta da al’umar jihar domin hidimar zaben tseren kujerar gwamna da za a yi a jihar a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba 2019.

Gwamna Yahaya Bello ya amince da ranar juma’a, 15 ga Nuwamba a matsayin ranar hutu ta jama’a da dukkanin makarantun da ke jihar.

A wata sanarwa da Sakataren dindindin na ma’aikatar ilimi na jihar, Mista Eric Aina ya sanya wa hannu, ya ce dukan makarantun gwamnati da masu zaman kansu za su ci gaba da hutu daga ranar 15 ga Nuwamba, 2019, gabadin zaben ranar 16 ga Nuwamba da zai gudana a jihar.

Gabatar da hutun ya kunshi ganin tabbatar da cewa dukkan dalibai sun hade da danginsu yayin hidimar zaben jihar da ya gabato.

Naija News ta samu fahimtar cewa hutun zai kawo karshe ne a ranar Litini, 18 ga Nuwamba, 2019 a yayin da makarantu zasu ci gaba da ayukansu.

Ka tuna a wata faifan bidiyo wadda kamfanin dilancin labarai ta Naija News Hausa rabas kamar yadda ta gano a layin sada zumunta ya nuna lokacin mutanen Kogi suka kunyatar da Gwamna jihar Kogi, Yahaya Bell a garin Lokoja, babban birnin Jihar.

Abin ya faru ne da gwamnan a yammacin ranar Lahadi, 10 ga Nuwamba a Lokoja, babban birnin jihar Kogi a yayin yawon neman zaben da Bello yayi a jihar.

A cikin faifan bidiyon wanda aka rabas ta shafin yanar gizon Twitter a hannun Sanata Dino Melaye, yayi nunin yadda mutanen Lokoja suka yiwa gwamna tsuwa da zage-zage a lokacin da ayarin motocin sa suke wucewa ta hanyar Lokoja.

Kogi: Gobara ta Afka da Kone Sakatariyar Jam’iyyar SDP a Jihar Kogi

Rahotanni da suka iso ga Naija News ya bayyana da cewa an kona sakatariyar Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar rahoton da wakilinmu ya tattara, mutane da ba a san ko su wanene ba amma da ake zargi da zaman ‘yan tada zama tsaye wajen hidimar siyasa, sun kutsa cikin sakatariyar jam’iyyar SDP da sanyin safiyar ranar Litinin, suka kuma kone ofishin kurmus.

Al’amarin ya faru ne kwanaki biyar kacal ga hidimar zaben kujerar gwamnan jihar, wadda hukumar INEC ta sanar da gudana a ranar 16 ga Nuwamba a jihar.

Kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta ruwaito a baya da cewa an kai wata hari kan sakatariyar SDP a ranar Lahadin da ta gabata.

An bayar da cewa an lalace dukan kofofin sakatariyar, yayin da aka kuwa lalata wasu kayan hidimar neman zabe tare da musanya wasu da fostocin dan takarar jam’iyyar APC, Yahaya Bello.

Jam’iyyar SDP ta zargi jam’iyyar APC da wata shirin kai hari kan ayarin dan takarar gwamna a jam’iyyar  SDP, Natasha Akpoti da neman sace ta.

Ku tuna da cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Alhamis, ta umarci Hukumar gudanar da hidimar zabe (INEC) da ta maido da Madam Natasha Akpoti, ‘yar takara a karkashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaben gwamna na ranar 16 ga Nuwamba mai zuwa a jihar Kogi.

KARANTA WANNAN KUMA; Idan ba za ku iya ciyar da Iyalanku ba, to kada ku tura yaranku don yin bara a Madadin ku – inji Sarkin Kano.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 16 ga Watan Satunba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 16 ga Watan Satunba, 2019

1. Xenophobia: Shugaban kasar South Afirka na shirin Aika da Wakilan musanman ga Shugaba Buhari, tare da wasu

Shugaban kasar South Afirka, Cyril Ramaphosa, na a shirye a yayin da yake batun aika da jakadu na musamman ga shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari da sauran shugabannin Afirka da dama kan harin ta’addancin da ‘yan kasar suka yi a kwanakin baya.

Bisa rahoton da News24 ta bayara, Wakilan musamman za su isar da sakon ne ga shugabannin kasashen Afrika da gwamnatoci da dama a fadin Afirka.

2. Biafra: Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu zai gana da jami’an Majalisar Dinkin Duniya ranar Talata

Jagoran kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) a ranar Talata, 17 ga Satumbar, zai gana da jami’an Majalisar Dinkin Duniya a ofishin sa da ke a Geneva, a kasar Switzerland.

Naija News ta fahimta da hakan ne bisa wata gabatarwa da Magatakardar kasar, ya bayar ga manema labarai.

3. ‘Yan Sanda Sun Ba da Gargadi mai Karfi ga Daliban FUOYE

‘Yan sanda a Jihar Ekiti sun yi gargadin cewa daliban Jami’ar Tarayya, Oye Ekiti (FUOYE) da su guji duk wani taron jama’a da zai iya haifar da tashin hankalai a kasar.

Naija News ta samu sanin cewa rundunar ‘yan sanda ta jihar yayin da take bayar da gargadin, ta jaddada cewa daliban su guji duk wani nau’in zanga-zanga, musamman zanga-zangar da aka danganta da kisan dalibai biyu a Jami’ar kwanar baya.

4. Kungiyar CUPP ta Bayyana shirin Gwamnatin Tarayya kan karkashiyar makircin da ta ke yi kan Hukunci zaben Shugaban Kasa

Kungiyar Hadin Kan Jam’iyyun Siyasa (CUPP) ta zargi Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da shirin makirci hade da alkalan Kotun koli gabanin hukuncin karar da Atiku Abubakar ya yi game da hukuncin Kotun Shugaban Kasa Petition Tribunal (PEPT).

Naija News ta tuno cewa Kungiyar ta PEPT ta yi watsi da karar da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP ya kalubalanci nasarar Shugaba Buhari da shi a zaben 2019.

5. Tsohon Gwamnan Benue, Suswam na batun barin Jam’iyyar sa

Rahoton da ke isa ga Naija News ya nuna cewa tsohon gwamnan jihar Benue da Sanata mai wakiltar mazabar Benue ta Gabas ta Tsakiya, Gabriel Suswam zai iya koma ga Jam’iyyar All Progressives Congress a cikin kankanin lokaci.

Wata majiya ne ta bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labaran Naija News.

6. Ku gayawa Buhari ya yi biyayya da Umurnin Kotu – SERAP ta gayawa AGF Malami

Kungiyar ‘Socio-Economic rights and Accountability Project (SERAP) ta bukaci Attorney Janar na Tarayya da Ministan Shari’a, Abukabar Malami, da su ba Shugaba Muhammadu Buhari shawarar biyayya ga hukuncin kotu.

SERAP ta yada hakan ne ga zancen hukuncin da mai shari’a Chuka Austine Obiozor ya bayar na ba da umarnin sakin bayanan biyan dukan kudaden da ya shafi aikin wutar lantarki da kamfanoni tun 1999.

7. Xenophobia: Abin da ya kamata Gwamnatin Tarayya ta yi ga gwamnatin South Afirka – Akinyemi

Farfesa Bolaji Akinyemi, tsohon Ministan Harkokin Waje, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ja Gwamnatin kasar South Afirka zuwa Kotun Duniya ta kasa saboda rashin kulawa da ‘yan Najeriyar da ke zaune a kasar South Afirka.

Ya fadi wannan ne sakamakon harin ta’addanci d ‘yan kasar suka yi wa ‘yan Najeriya da ke zaune a can.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa