Muna Zantawa Da Buhari Kan Yanayin El-Zakzaky – Gwamnatin Iran

Iran Ta Tattaunawa Da shugaba Buhari Kan Zancen El-Zakzaky

Gwamnatin Iran ta sanar da cewa tana cikin tattaunawa da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya kan batun jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, IMN, da aka fi sani da ‘Yan shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Abbas Mousavi, ya ce kasar tasu ta hanyar diflomasiya, tana hulda da gwamnatin Najeriya kan yanayin halin da El-Zakzaky ke a ciki.

Mousavi a hirar ya fadawa manema labarai a Tehran, babban birnin Iran a ranar Lahadin da ta gabata cewa Shugaba Buhari da Mataimakin Shugaban Harkokin tattalin arzikin Iran, Mohammad Nahavandian, sun gana kwanan nan a Malabo, Equatorial Guinea, kuma sun tattauna kan batutuwa da dama, ciki har da batun El-Zakzaky.

Taron ya gudana ne a yayin taron kolin kungiyar kasashen waje na fitar da Gas (GECF) a Equatorial Guinea.

Jami’in ya kara da cewa “Muna fatan cewa shawarwari da shirye-shiryen da ake yi tare da gwamnatin Najeriya za su yi cinma buri a gagauci wajen warware wannan matsalar ta El-Zakzaky,” in ji jami’in na Iran.

Naija News ta tuna cewa El-Zakzaky yana a tsare tun Disambar 2015, bayan shi da magoya bayan sa suka yi artabu da sojojin Najeriya a cikin jerin gwanon Hafsan Rundunar Sojojin kasar, Tukur Buratai, a cikin Zariya a jihar Kaduna.

Bayan haka, hukumar DSS a ranar Jumma’a da ta gabata ta dauki El-Zakzaky da matarsa ​​Zeenat daga Ma’aikatarta zuwa Gidan Horon Al’umma da ke a Kaduna, kamar yadda Babban Kotun Jihar Kaduna ta umarce su da yi.

Kotu Ta Umurci Hukumar DSS Da Ta Mayar Da El-Zakzaky Ga Cibiyar Horon Al’umma

Wata babbar kotun jihar Kaduna ta ba da umarni ga hukumar DSS da ta dauki shugaban IMN, kungiyar ci gaban Musulunci da aka fi sani da ‘Yan Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da uwargidansa Zeenat daga tsarewar ma’aikatarta zuwa cibiyar gyara halin al’umma ta jihar Kaduna.

Alkalin kotun ya bayyana da cewa yin hakan na da kyau don inganta da samun saukin saduwa da shi.

Wakilin kamfanin dilancin labarai na TVC, Tesem Akende, ya ce a duk lokacin da aka gabatar da zancen, hukumar kan tsauya zancen don tabka magudi a babban birnin jihar kamar yadda aka saba yi a koyaushe a duk lokacin da za a fara sauraron karar.

A haka an sanar da daga karar zuwa 6 ga Fabrairu na shekara mai zuwa don sauraron kara.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da ya sa har yanzu ba a biya Albashin NPOWER Na Watan Oktoba da Nuwamba ba.

Shiites: Kalli Hotunar Isar El-Zakzaky da Matarsa a kasar India a yau

Bayan hukunci da Kotun Koli ta Jihar Kaduna ta bayar ga sakin Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, shugaban Kungiyar ci gaban Harkar Musulunci (IMN) da aka fi sani da ‘Shi’a, rahotannai sun bayyana da tashin El-Zakzaky da Matarsa zuwa Turai daga birnin Abuja a jiya, Litini, 12 ga watan Agusta.

A yau Talata, 13 ga watan Agusta 2019, Naija News Hausa ta karbi rahoto da tabbacin isar El-Zakzaky da Matarsa Zeenat, a kasar Indiya.

Ka tuna da cewa ‘Yan Kungiyar shi’a a baya sun tayar da zanga-zanga a kasar da bukatar a saki shugaban su. Har ma sanadiyar hakan, an kashe rayuka da dama a birnin Tarayya, da kuma barin mutane da yawa da raunuka.

Hotunan da ke kasa da Naija News ta ci karo da shi ya bayyana tabbacin isar El-Zakzaky da matarsa a kasar Indiya don binciken Lafiyar Jikunansu.

Kalli Hotuna;

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 26 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 26 ga Watan Maris, 2019

1. An Mika wa shugaba Buhari Rahoton Albashin Ma’aikata

An bayar da takardan rahoto akan yadda za a samu biyan kankanin kudin albashin ma’aikatan kasa ta naira 30,000 ga shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga takardan biyan kankanin albashin ma’aikata na naira dubu talatin.

2. Mataimakin dan takaran kujerar Gwamna a Jam’iyyar AAC ya koma PDP a Jihar Rivers

Jam’iyyar PDP ta yi sabon bako a yayin da mataimakin dan takaran kujerarn Gwamna daga jam’iyyar AAC a Jihar Rivers ya janye daga jam’iyyar da komawa ga jam’iyyar PDP.

Akpo Bomba ya gabatar ne da hakan ‘yan kwanaki kadan bayan da aka kamala zaben gwamnoni a jihohin kasar.

3. Ba zamu raba shugabancin mu da PDP ba – inji Oshiomhole

Babban Ciyaman na Jam’iyyar APC ga hidimar zaben tarayya, Adams Oshiomhole ya gabatar da cewa jam’iyyar APC ba za ta rabar da kujerar shugabancin ta da jam’iyyar PDP ba a gidan Majalisar Dattijai.

Oshiomhole ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da yayi ga zaman tattaunawar da Jam’iyyar APC tayi da ‘yan gidan majalisa.

4. An kara daga karar El-Zakzaky zuwa gaba

Kotun Koli ta Jihar Kaduna ta daga zancen karar shugaban kungiyar ‘yan Musulumman Najeriya da aka fi sani da IMN,  Ibrahim El-Zakzaky, da Matarsa, Zeenat.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan Shi’a sun gudanar da zanga-zanga a garin Abuja don bukatar a saki shugaban su.

5. Kotu ta Janye Karar dakatar da hidimar zabe a Jihar Bauchi

Kotun Koli ta birnin Abuja tayi watsi da karar da Gwamnan Jihar Bauchi, Mohammed Abubakar da Jam’iyyar APC suka gabatar na kalubalantar hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) akan dakatar da hidimar zaben Jihar Bauchi a baya.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kotun Koli ta birnin Abuja ta hana hukumar INEC da gudanar da hidimar zabe a Jihar Bauchi.

6. Jam’iyyar APC ta Jihar Sokoto sun yi watsi da sakamakon zaben Jihar

Jam’iyyar APC ta Jihar Sokoto sun gabatar da rashin amincewar su ga sanar da Gwamna Aminu Tambuwal, dan takaran kujerar Gwamna daga jam’iyyar PDP a matsayin mai nasara ga zaben kujerar gwamnan Jiahr ga zaben ranar Asabar da ta gabata.

Hukumar INEC ta sanar a ranar Lahadi da ta gabata da cewa Tambuwal ne ya lashe tseren takaran kujerar gwamnan Jihar, bisa yawar kuri’u fiye da dan adawan sa.

7. Kasar Turai sun kafa baki ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari

Kungiyar Kasar Turai (EU) ta jinjina da kuma taya shugaba Muhammadu Buhari murna ga samun cin nasara ga zaben shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu.

Kungiyar sun gabatar ne da gaisuwar a wata wasika da aka wallafa ga shugaban da kuma aka bayar a ranar 22 ga watan Maris 2019.

8. Sanata Saraki na kokarin ya ci gaba da cin albarkacin shugabanci

Jam’iyyar APC a gidan Majalisar Dattijai na zargi da kuma jita-jitan cewa shugaban Sanatocin kasar Najeriya, Bukola Saraki na kokarin ya ci gaba da cin albarkacin shugabancin gidan majalisar bayan da ya fadi ga zabe.

Naija News Hausa na da sanin cewa Sanata Saraki ya fadi daga tseren takaran kujerar Sanata daga yankin Jihar Kwara.

Ka samu cikakken labarun kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa