Rundunar Sojojin Najeriya su yi nasara da kashe wasu ‘yan Ta’adda biyu a Borno

A wata sabuwar zagayen Rundunar Sojojin Najeriya a yaki da ta’addanci, Sojojin sun ci nasarar kashe mutane biyu da ake zargi da zama ‘yan ta’adda a Gwoza, Jihar Borno.

Naija News Hausa ta sami tabbacin hakan ne a tabbacin da Kakakin yada yawun Rundunar Sojojin Najeriya, Colonel Sagir Musa, da cewa rukunin darukan Sojojin ta 26 Task Force Brigade sun kase ‘yan ta’addan a hanyar da ta bi Sabon Gari zuwa ga kauyan Jirawa , a ranar Jumma’a, 28 ga watan Yuni, 2019 da ta gabata.

A bayanin Colonel Sagir, “Rukunin Darukan Sojojin ta ci nasara da hakan ne bayan da ta karbi wata kirar kula daga wani mazauna mai halin kwarai”

Ya kuma kara bada haske da cewa nasarar ya kunshi hadin kan rukunin Sojojin ta Operation Halaka Dodo da wasu kananan hukumomin tsaron da ke a Jihar.

“Maharan na kokarin ne su bi mazauna da ke aiki a kan gonakin su, su sace mata da yaran su da kuma tafi dasu don tilasta su da yi masu bauta bayan sun sace su” inji Sagir.

“rundunar Sojojin ta sami karban makamai iri-iri, kamar su Ak 47, Harsasai daban daban, Babur (Bajaj) da kayakin sawa masu tsadar gaske daga hannun ‘yan fashin”

KARANTA WANNAN KUMA; Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da ranar Jarabawa ga masu neman aikin tsaro.