Connect with us

Uncategorized

Kannywood: A Yau Mun tuna da Marigayi Rabilu Musa ‘Dan Ibro’

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Yau a Naija News Hausa muna tunawa da shahararen dan wasan fim na Kannywood, marigayi Rabilu Musa da aka fi sani da suna ‘Dan Ibro’.

Yau Shekaru Hudu da Wata Daya da ‘yan kwanaki da ‘Dan Ibro’ ya rabu da wannan duniyar, Allah ya jikan rai.

Rabilu Musa na daya daga cikin ‘yan wasan fim na kannywood da ba za a taba manta da gurbin su ba. Mutum ne da ake ji da shi, kuma mutun ne mai bada dariya kuwa. Mutuwar ‘Dan Ibro’ ya bawa mutane da yawa mamaki da kuma tausayi, har ma wasu sun ce ko mafarki suke yi da jin labarin mutuwarsa, amma ga shi a yau abin ya kai har shekara hudu da kwanaki.

Takaitacen Rayuwar Rabilu Musa ‘Dan Ibro’

  • An haifi Rabilu Musa ne a ranar 12 ga Watan Disamba, Shekara ta 1971 kamar yadda tarihi ta bayar.
  • Rabilu Musa kuwa ya mutu ne a ranar 9 ga Watan Disamba, shekara ta 2014 a Jihar Kano

Maimacin da aka haifa a Jihar Kano ya yi rayuwar shekaru 41 a duniya kamin Allah ya sa ya kai ga hutawa.

Karatun ‘Dan Ibro’

  • Dan Ibro ya yi karatun Firamari ne a Danlasan Primary School da ke a Wudil, Jihar Kano
  • Ya kara gaba da karutunsa a makarantar Government Teachers College a nan Wudil.
  • Rabilu Musa ya shiga aikin Jami’an Kula da Kurkuku (NPS) a shekara ta 1991 ya kuma bar hukumar bayan ‘yan lokatai kadan ya koma wa shirin fim da wasan kwaikwayo na ban dariya.

Shirin Fim. 

Bayan da Rabilu Musa ya janye ga aiki da Jami”an tsaron Kurkuku a shekara ta 1991, ‘Dan Ibro ya fada wa shirin fim. Wasan farko da ‘Dan Ibro yayi itace; ‘Yar Mai Ganye’ wannan shirin ya daukaka Rabilu Musa da gaske har sunan shi ya bi ko ta ina.

Ya kuma fito cikin wasannai kamar; Andamali, Bita Zai Zai, Ibro Aloko, Ibro Angon Hajiya da sauran su dai.

Waka;

Bayan fita shirin fim da jagoran wasannai, ‘Dan Ibro na da baiwar waka kuma. Sau da yawa a fim ya kan watsa muryan sa ga waka, ko ga shirin da aka bukace shi da hakan ko kuma nasa shirin.

Rabilu Musa yayi wakoki kamara: Bayanin Naira, Idi Wanzami, Dureba Makaho, da sauran su dai.

Muna isar da gaisuwar mu ga Iyalan Rabilu Musa da ‘yan uwan sa duka don hakkuri da abin da Allah kawai ya isa yi. kuma muna mai cewa “Harwa yau muna ji da Rabilu, ko da shike bai saura da rai ba”. 

“Allah ya sa ya huta Lafiya” Amin.

Naija News Hausa

Kalla: Kadan daga cikin Shirin da ‘Dan Ibro’ ya fito ciki kamin rabuwarsa da mu

Ku sami karin cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa