Gwamnatin Tarayya ta Kafa Bultsatse 295, Gidan Bayi 152 a Karamar Hukumar Adamawa 7

Don cika ga alkawarin kulawa da bada Tallafi ga yankunan da ke fuskantar rashin tsaro, da ta’addanci, Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sake gyara da tsarafa Mabultsatsan ruwa 295 da kuma ɗakin bayan gida 152 a cikin kananan hukumomi bakwai da ke fama da matsaloli a Jihar Adamawa.

Naija News Hausa ta sami tabbacin hakan ne a wata bayanin da Jami’in Harkokin Cigaba da Farfado da Yankin Jihar Adamawa, Dakta Maurice Vonubolki, ya bayar a wata hira da yayi ranar Laraba a Yola da manema labarai.

Vonubolki a cikkin bayanin sa ya bayyana da cewa shirin na tare ne da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da bankin duniya kan farfadowa da kuma sake gina ababen more rayuwa da rashin tsaro ya lalata a yankin.

Ya kara da cewa ana aiwatar da aikin murmurewar ne a jihohi ukun da suka hada da Adamawa, Borno da Yobe, yana mai cewa “tuni an samar da fanfunan ruwan bultsatse guda 295 da kuma Injimin ruwa mai aiki da Sola 50.

“Haka kazalika, an gina ɗakin bayan gida 152 a cikin yankuna bakwai a kananan hukumomin jihar da ke fama da rikice-rikice a cikin Adamawa,” Inji Kwadinetan.

Jami’in ya kara bayyana da cewa wuraren da za a amfana sun hada da kananan hukumomin Madagali, Maiha, Mubi-Arewa, Mubi-South, Maiha, Hong da Gombi.

Mista Vonubolki ya kuwa gargadi mazauna yankunan da su tabbatar da yin amfani da wadannan ayukan yadda ya kamata da kuma kula da su.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnatin Jihar Neja a wata sanarwa ta bayyana da cewa ta kusa kamala Gyaran munanan hanyar Suleja zuwa Minna.