Gwamnatin Jihar Zamfara ta kafa dokar Zama daki Rufe ga dukan Kananan hukumomin Jihar bisa Matsalar tsaro

Gwamnatin Jihar Zamfara, a jagorancin Gwamna Abdulaziz Yari, sun gabatar da dokar zama daki rufe a yau Laraba, 3 ga Watan Afrilu 2019 na tsawon awowi daga karfe bakwai na dare zuwa bakwai na safiyar ranar da ke biye.

Naija News Hausa ta samu wannan rahoton ne a yayin da Kwamishanan Harkokin Kananan hukumomin Jihar, Bello Dankande Gamji, ya bayyana ga manema labarai a garin Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.

Gamji, ya bayyana ne da cewa gwamnatin Jihar ta dauki wannan mataki ne a kan dole bisa mumunar hari da matsalar tsaro da ake samu a Jihar. Musanman wata Macce da aka sace da diyar ta a yau a yayin da ta shiga Keke NAPEP zuwa gidan ta.

Don bada tabbaci da wannan, Kwamishanan Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar, Mista Celestine Okoye ya bayyana da cewa hukumar su zata watsar da jami’an tsaro a dukan yankunan da ke Jihar, ya kuma shawarci mutanen Jihar da bin doka sabili da cewa ‘yan sanda za su kame duk wanda aka gane da rashin bin dokar ‘Zama daki Kulle’ bisa tsawon awowi da aka sanar.

“Mun gane da cewa wannan matakin zai zama da tsanani kwarai da gaske ga mutanen Jihar, amma zai fi kyau muyi hakan don magance wannan matsalar da kuma tabbatar da tsaron rayukar mutanen mu da tattalin arzikin su.” inji Dankande.

Ya karshe da gabatar da cewa hukumar ta gane da hadin kan masu babura da motocin kasuwanci ake aiwatar da sace-sacen mutane a Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Mahara da Bindiga kashe mutane fiye da 13 a wata sabuwar hari a kauyuka biyu ta karamar hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara ranar Lahadi da ta gabata.