Sabuwa: Shugaba Buhari Na Taron Siri da Shugabannin Tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Talata, ya na wata ganawar sirri da shugabannin tsaron kasar da kuma shugabannin hukumomin tsaro.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta samu tabbacin sanar da cewa taron na gudana ne a fadar shugaban kasa, Aso Rock Villa da ke Abuja.

Sanarwan taron ya bayyana ne a shafin yanar gizon gizo ta mataimakin shugaban kasar a hanyar sadar da labaran yanar gizo, Bashir Ahmad; wanda ya aika da cewa “Shugaba Muhammadu Buhari a haka yana wata taron siri da manyan shugabannin tsaron kasa da kuma shugabannin hukumomin tsaro a Abuja.”

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, yayin da yake magana kan halin da Najeriya ke ciki, ya bayyana cewa idan har Annabi Isa zai kasance a wannan kasar a wannan lokacin, zai yi korafi kan yadda masu iko ke tafiyar da mulkin kasar.

Tsohon Shugaban a cikin sanarwar sa ya karfafa malaman adinin Kirista da cewa kada su yi shuru game da abin da ke faruwa a kasar amma a koyaushe su fadi gaskiya ga mutanen da ke kan mulki.