Jihar Plateau: Zamu samar da tsaro ga Jihar, Mafarauta sun gayawa Simon Lalong

Wata kungiyar Mafarautan Jihar Plateau (PHA) sun yi barazanar cewa zasu karfafa tsaro a Jihar Plateau.

Kwamandan Kungiyar (PHA), Mista Igyem Danladi ya gabatar da cewa kungiyar na goyon bayan Gwamna Simon Lalong saboda irin gwagwarmaya da kokarin sa na ganin cewa akwai zamantakewar lafiya a Jihar Plateau.

“Zamu karfafa samar da tsaro a kewayen Jihar Plateau don magance duk wata rukuni na ‘yan ta’adda” inji Danladi, shugaban kungiyar (PHA) a yayin da suka gana da Gwamnan Jihar a yau Talata 29 ga Watan Janairu.

“Sau dayawa mun kwato dabbobi daga hannun mahara a yankin a yayin da suke kokarin sace ta daga masu shi” in ji Danladi.

“Sau da dama kuwa mafarauta sun bi ‘yan hari har cikin bakin daji don kwato hakin mutane daga garesu, harma da kame barayi da ke muzunta mutane a yankin Shedam” inji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Kashim Shettima, Gwamnan Jihar Borno ya gabatar da cewa zai sanya Mafarauta ga yaki da Boko Haram a Jihar.

Karanta kuma: Yan Hari da bindiga sun Kashe Insfektan ‘Yan Sanda biyu a Jihar Katsina