Kannywood: Takaitaccen Labarin Jaruma Jamila Nagugu

A yau Naija News Hausa ta na gabatar maku da takaitaccen Sarauniyar Kannywood, da aka fi sani da Jamila Nagudu, a yadda sunan nata yake.

Ka tuna a baya Naija News ta ruwaito da cewa Jamila Nagugu ta ce ‘Ba Ta son ta Auri Mai Arziki.

A takaice dai, Jaruma Jamila Nagudu ‘yar wasan finafinan Hausa ce wacce aka Haifeta a ranar 10 ga watan Agusta.

Jamila Umar Nagudu a nata bangaren Sarauniyar Kannywood ce, ma’ana, ita babbar jaruma mace ne a fagen shirya fina-finan Hausa, watau Kannywod wacce take da hedkwatarta a Kano, arewacin Najeriya.

Jarumar ta shiga fagen masana’antar fim na Hausa ne shekaru da yawa baya, amma ‘yan shekaru da suka gabata, babban Froduza na fina-finai, Aminu Saira ya sanyata a cikin fitaccen fim din da aka yi wa take ‘Jamila da Jamilu’, watau tun a fim dinne tauraron jaruma Jamila ya haska da bayyana ta ko ta ina saboda irin kwarewa da taka rawar gani a fim din.

Jamila dai ta sami lambobin yabo bakwai na masana’antu kuma ta fice a fina-finai da yawa.

A wata ganawa da Jaruma Jamila tayi da BBC Hausa a shekarar 2016, Nagudu ta shaida wa BBC cewa ba ta da saurayi a cikin masu yin fina-finai a Kannywood.

Amma dai a lokacin hirar ta kara da cewa idan ta gamu da wanda ranta ke so a cikin abokan aikinta ba za ta yi kasa-a-gwiwa wajen aurensa ba.

A cikin karin bayanin nata, Fitacciyar jarumar ta yi watsi da zarge-zargen da ake yi wa ‘yan fim cewa ba sa son yin aure, tana mai cewa “idan lokacin yin auren mutum bai yi ba babu yadda za a yi ya yi da kansa”.

“Mutanen da suke cewa ba ma son zaman aure, su dubi sauran al’umma mana. Akwai mata da yawa wadanda suka girme ni amma ba su da aure saboda Allah bai sa lokacin yinsu ya yi ba.” Inji cewarta.

Ga Fina-Finai da dama da Jamila Nagugu ta fice a cikinsu;

Jamila Mai Wasa Da Kura, Kama Da Wane, Kanin Miji, Kishiya Ta, ‘Ya ‘Ya Na, Alhaki Kwikwiyo, Aska Tara, Bashin Gaba, Cikar Burina, Farin Dare, Fataken Dare, Fitilar Dare, Ga Fili Mai Doki, Gamdakatar, Halisa, Haske, Hindu, An African Extra Vagrant, Inda Ranka (Kasha Kallo), Jamila da Jamilu, Jani Jani, Jarumta, Laifin Dadi, Larai, Mai Dalilin Aure (Match Maker), Marayan Zaki, Masu Aji, Muradi, Sai a Lahira, Salma Hayat,
Ya Salam. Da dai sauransu.

Sabuwar Fim: Mu Zuba Mu Gani | Hade da Ali Nuhu, Fati Washa, Jamila Nagudu da Sauransu

Naija News Hausa na tura muku wannan sabuwar fim na Hausa don nishadewa.

“Mu Zuba Mu Gani” sabuwar fim ne da ya kasance da shahararrun da kwararru a Kannywood, kamar su Sarkin Sangaya; Ali Nuhu, Fati Washa, Jamila Nagudu da dai sauransu.

Kalli Fim din A Kasa;

https://www.youtube.com/watch?v=Cf0Rsik_9xs