An Bayyana Lokacin Da ‘Yan Bautan Kasa (NYSC) Zasu Fara Karbar Tallafin N30,000

An tabbatarwa membobin kungiyar ‘yan bautan kasa da aka fi sani da (NYSC), cewa za a sake nazari kan fara basu sabon mafi karancin albashi na N30,000 a kowane wata daga shekarar 2020.

Mista Sunday Dare, Ministan matasa da ci gaban wasanni ya yi wannan sanarwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar daga ofishinsa na watsa labarai a jiya yayin ziyarar Filin ganawa da koyaswa ta hukumar ‘National Youth Service Corps’ da ke a Iyana-Ipaja, jihar Legas.

Ya ce, “Za a sake nazari da shiri domin yadda za a fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 na kowace wata ga ‘yan bautan kasa ta NSYC daga shekarar 2020. An riga an yi adadin wannan shirin a cikin kasafin shekara mai zuwa.” 

“A koyaushe ina bayar da shawarar cewa dole ne Najeriya ta sanya hannun jari ga matasa. Mu a ma’aikatar muna sake duba da kokarin samar da cigaban matasan mu dangane da shirye-shirye.”

“Ma’aikatar ta kirkiro wani shiri mai suna DY.NG. Muna son hakan ya kasance shiri ne na watanni biyu wanda zaku gudanar yayin hidimarku, bayan haka zaku sami wasu matakan takaddun shaida. Zai ba ku wannan damar da ta fiye digiri da kuke da ita.”

Ba mamaki Boko Haram su fada wa Jihohi kamar Bauchi, Taraba, Gombe, Adamawa – in ji Sunday Onuoha

Ganin yadda ‘yan ta’addan Boko Haram ke kai mumunar hare-hare da kashe-kashe a Arewacin kasar Najeriya, “babu mamaki ‘yan ta’addan su fadawa wa sauran Jihohi da ke arewacin kasar, kamar Jihar Bauchi, Taraba, Gombe da Adamawa” in ji Onuoha.

Shugaban kungiyar hadin guiwa da zamantakewa, Bishop Sunday Onuoha ya yi gargadin cewa idan har ba magance matsalar tsaro ba a kasar nan, lallai ba mamaki ‘yan ta’addan su fadawa wa sauran Jihohi da ke arewacin kasar, kamar Jihar Bauchi, Taraba, Gombe da Adamawa.

Sunday Onuoha ya bayyana wannan ne a yayin da yake gabatarwa a wata taruwar tarayya da aka yi a birnin Abuja a ranar jiya da taken, ‘Zaben Tarayya da Tsaron Tarayya’ alhakin zamantakewar addinai duka.

Ya ce, musanman ma kashe-kashe da ake yi a yamma ta kudun kasar, da kuma ‘yan ta’addan da ke kudu maso gabashin kasar, dole ne a nemi hanyar magance wa ‘yan nan ko kuma kasar ta koma wani abu da ba a zata ba.

Ya kara da cewa, rashin tsaro a shekarun baya kamar shekarar 2015 bai raunana kamar ta yanzun nan ba.

Karanta kuma: Dan takarar shugaban kasa ta Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yaba wa Kungiyar Manyan shugabanan Jihar Borno (Elders Forum) don sakon rashin amincewa da shugaba Buhari akan matakin sake ‘yan ta’addan da aka kame.

“Kullum ana karuwa ne da kashe-kashe a Jihar Borno da Yobe, ‘yan ta’addan Boko Haram duk sun bi sun mamaye Jihohin nan da hare-hare. kullum jami’an tsaro da jama’ar kasar na ta rasa rayuwan su” in ji shi.

Bishop din ya umurci jama’ar Ikklisiya duka su shiga addu’a don cin nasara da kuma samar da zaben 2019 da ke gaba cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan Najeriya don su zabe shi ga zabe na gaba

“Lokatai da dama mun samar da ‘yan takara masu karfi da fasaha kuwa, amma harwa yau kasar mu ta raunana sosai. Bukatar mu shi a karshen zaben, kowa ya yi kokarin daukar sakamakon zaben yadda ta zo masa don samun zaman lafiyar kasa” in ji Sunday.

 

Ku sami karin labarai daga Naija News Hausa