Connect with us

Labaran Najeriya

Miyetti Allah ta yi Bayani akan zabi tsakanin Buhari ko Atiku a zaben 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Miyetti Allah na shirin bayyana zabin su ga Zabe Shugaban Kasa ta Shekarar 2019 Presidential Candidate

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, watau ƙungiyar zamantakewa da al’adu ta Fulani, sun fada da cewa sun kusa su nuna zabin su tsakanin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Dan Adawan sa Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa watau Atiku Abubakar.

Babban Shugaba na wannan Kungiya, watau Alhaji Bello Abdullahi Bodejo, da Sakatare na kungiyar mai suna, Engr. Saleh Alhassan ya fadi wannan ne a ranar Jiya a Abuja a wata taron labarai.

“Mun tabbatas da cewa yan kungiya duka sun yi rajista ga zaben da kuma ganin cewa ba wani shiri na tashin hankali a ko ina zasu jefa zaben su.

“Mu sa nufi da ganin cewa duka yan kungiya su fito domin jefa zaben su. muna kuma murna da cewa Hare-hare Makiyaya nan ya zo kasa ganin cewa Manyan yan Takaran Shugaban Kasa biyu da aka Tsayas Fullani ne.

“Wannan ya zama abin amfana ga kasa dubin cewa ba zabi don yare, ko addini, ko karkara. wannan abin fahariyya ne ga kasa.

“Game da zabin mu ga wanda zai zama Shugaban Kasa ta mu, har yanzu muna awo da dubi mai zurfi ga abin da yan takaran biyu zasu iya fidda shi, abin da za su iya yi wa kasan, da kuma matakai da zasu iya dauka domin yanayin hare-hare da ake kai wa yan addinin Krista. Idan mu gama wannan bin ci ke da dubi, zamu iya bayyana zabin mu ga duniya duka don su sani. Mun iya nuna wa yan kungiyan mu duka su shirya da katin zaben su duka, su kuma jira har lokacin zabe kowa yayi zabi ta kwarai wanda zai amfanemu duka da kasa.

“Zamu yi bincike ga ajanda da yan takaran guda biyu ke da shi akan kungiyar mu” in ji shi Bodejo.