Uncategorized
Cututtuka da Namijin Goro ke Iya Warkas wa a jikin Dan Adam
Tasirin da Anfanin Namijin Goro ga Dan Adam
Namijin goro wani ‘ya’yan itace ne da a Turance ake kira da ‘Garcinia Kola’, asali amfi samun sa ne a kasashen Afrika, wadda tun dinbin shekarru ana amfani da shi a matsayin wani nau’i na magani a al’adun ‘yan Afrika.
A ganewa da fahimtar Naija News Hausa, bisa bincike Namijin goro na dauke ne da sinadiran ‘Dimeric Flavonoid’ wanda bincika ya tabbatarda yana magungunna da dama.
Anfi sanin noman namijin goro ne a kasar Afrika, kamar Najeriya, Congo, Gana, Senegal, Benin, dadai sauransu.
Bisa ganewa da kuma binciken likitocin Afrika, sun yi imani da bada tabbacin cewa namijin goro nada sinadiran da zai iya warkas da cututtuka da dama a Afrika.
Ga Jerin Cututtuka da Namijin Goro zai iya magance a jikin dan Adam
1. Namijin Goro na maganin matsalar ido, watau (Glaucoma)
Bisa wata rahoto da masu fasaha a kasar New York Times suka bayar, yawan matsalar ido na zama sanadiyar kamuwa da glaucoma. Akwai kuma wani binciken da aka yi a sashen asibitin koyarwa na jami’ar jihar Lagos, a Najeriya, a cikin rahoton an bayyana amfanin da ruwan maganin da ake digawa cikin ido wanda kuma ya kunshi Sinadirin Namijin Goro.
Anfani da maganin sau biyu kai da kai zai kawo saukin cutar da ake fama da ita.
2. Yana kashe Dafin Maciji da Kunama:
Anfani da Namijin goro na kashe dafin cizon maciji, idan maciji ya ciji mutum to a bashi namijin goro guda kawai ya ci. Da yardan Allah nan take zai kashe rabu da dafin cizon macijin.
3. Nakar da Abinci da kuma Tseda Gudawa
Namijin Goro na taimakawa wajan saurin narkar da abinci a ciki. Idan ciki ya kume, kokuma anci abinci marasa kyau, ko kuma abinda idan anci zai bata yanayin ciki, sai a tamna namijin goro, zaitaimaka wajan narkar da abincin da gaggawa batare da cikin ya baciba. Hakazalika yanada sinadarin dake taimakawa wajan tseda guduwa.
4. Kashin Maciji
Idan an gane da wani waje a gida da Maciji ke yawo, Ana iya shanya namijin goro har ya bushe sai a daka, bayan an daka sai a barbada a wajen, ko kuma duk inda ba a so a gan maciji, idan macijin ya ketara wannan garin namijin goron to nan take macijin zai mutu.
5. Maganin Sanyin Kashi
Sanyin Kashi wani ciwo ne da a Turance ake kira da (Osteoarthritis), wanda aka fi sani ciwon gabobi, da kuma samun matsala wajen juya su, kamar dai yadda cibiyar kasa mai kulawa da lafiya ta bayyana.
Bisa binciken masana daga jami’ar Obafemi Owolowo a Najeriya, a jagorancin Mista Olayinka O. Adegbehingbe, a wata rahoto da ya kuma wallafa a Watan Yuli na shekarar 2008 da ta gabata, Sun bayyana bayan binciken su da cewa Namijin goro idan ana anfani da shi bisa sharadi a hankali yana rage zafin ciwon Sanyin Jiki, samar da dama ta yadda za a rika motsa gabobin jiki kuma.
6. Namijin Goro na Wankin Mara da Kara Karfin Jima’i
Cin Namijin Goro yana da sinadarin da ke taimakawa wajen wanke mara, da kuma ba taimakawa ma’aurata karfi, sha’awa da gamsuwa wajen jima’i a koyaushe.
Ba nan ta kare ba, akwai Tasiri da dama a jikin Namijin Goro da ba iyaka. Naija News Hausa na mai bada shawara ga Al’umar Najeria da Afrika gaba daya da tabbatar da amfani da Namijin Goro a hanyoyi da suka dace don magance matsalolin jiki, ba tare da kashe-kashen kudi ba ga sayan magunguna da basu taimakawa, ko kuma da tsadar gaske ba kuma da biyan bukata.
Kankanin mu tun kafin bayyanar na’urar bincike sun yi amfani da ‘ya’yan itace da bawar itace don magance matsalolin da ya shafi lafiyar jikunan su.
KARANTA WANNAN; Jerin sabbin Fina-Finan Hausa da baka kalla ba tukuna da kuma yadda zaka kalle su.