Gwamnan Jihar Kwara ya gabatar da Matashiya mai shekara 26 a matsayin Kwamishina

Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, ya nada Miss Joana Nnazua Kolo, mace mai shekaru 26 da haihuwa da ke hidimar bautar kasa (NYSC), a matsayin kwamishina.

Naija News ta ba da rahoton cewa Matashiyar mai shekaru 26 na daga cikin kwamishinoni mata hudu wadanda aka zaba da mika sunayensu ga majalisar dokokin jihar Kwara a ranar Talata, 17 ga Satumbar don tantancewa.

Kolo, ƙaramar yarinya a tarihin jihar, zabbbiya a cikin jerin sunayan kwamishinoni, ta kammala karatun digiri dinta ne a Makarantar Kimiyya ta Jami’ar Kwara (KWASU), ƙwararrace kuma wajen fafutukar ci gaban al’umma.

Idan har aka tabbatar da ita daga Majalisa a matsayin, za ta zama kwamishina mafi karancin shekaru a Najeriya, zata kuwa dauki matsayin karancin shekaru daga Oluwaseun Fakorede, Kwamishana mai shekaru 27 a jihar Oyo.

Naija News Hausa nada sanin cewa Kolo har yanzu tana cikin hidimarta na bautar kasar, watau “National Youths Service Corps” NYSC a Jigawa, inda take koyarwa a Makarantar Sakandare ta Model Boarding Secondary School Guri.

Za’a kuwa gudanar da nata binciken ne akan kujerar majalisar minista bayan da ta kammala hidimar NYSC dinta a makonni biyu da ke gabatowa.

 

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 16 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 16 ga Watan Agusta, 2019

1. El-Zakzaky da Matarsa sun kamo hanyar dawowa Najeriya

Ibraheem El-Zakzaky, jagoran Kungiyar Harkar ci gaban Musulunci ta Najeriya (IMN), wanda kuma aka fi sani da Shi’a da Matarsa, Zeenah Ibrahim, suna kan hanyarsu ta dawowa Najeriya daga kasar Indiya.

Naija News ta fahimci cewa su biyun za su dawo kasar ne bayan tafiyar kwana uku na ziyarar Indiya don binciken lafiyar jikinsu.

2. Kotu ta Ba da belin N20m Ga Surukin Atiku

Dakta Abdullahi Babalele, suruki ga dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya sami damar beli daga Kotu.

Alkali Nicholas Oweibo na babbar kotun tarayya da ke Legas ne ya bayar da belin a ranar Alhamis da ta gabata.

3. Gwamnatin Tarayya ta canza suna Na Hanyar Yanar Gizon Twitter

Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Alhamis da ta wuce, ta sanar da canza da sunan shafin yanar gizon da gwamnati ke amfani da ita a layin twitter.

Naija News Hausa ta fahimci cewa a yanzu sunan ya koma @NigeriaGov, maimakon @AsoRock, kamar yada take a da.

4. Abin da Ubana ya gaya mani a Indiya – ‘Yar El-Zakzaky

Suhaila Zakzaky, ‘ya ga El-Zakzaky’ ta bayyana cewa mahaifinta na fama da gubar dalma da kuma guba ta cadmium.

Ka tuna da cewa tun da farko shugaban IMN din ya ki karbar magani daga wasu likitoci da bai san da su ba da aka sanya don yi masa magani a Indiya.

5. Jam’iyyar PDP sun kalubalanci Umarnin Shugaba Buhari zuwa ga CBN

Jam’iyyar Dimokradiyya, babbar Jam’iyyar Adawa ta Najeriya (PDP) ta bayyana umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari ga Babban Bankin Najeriya (CBN) kan shigo da abinci a matsayin mataki mara wadataccen tsari.

Naija News ta tuna cewa Buhari ya umarci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ta daina ba da kudin musayar kasashen waje don shigo da abinci cikin kasar.

6. Kotun Kara ta sanya ranar yin hukunci akan Zaben Jihar Kwara

Kotun sauraren kararrakin zaben jihar Kwara ta sanya ranar Juma’a, 20 ga Satumbar, 2019, don gabatar da hukunci akan takarda kara da dan takara, Rasak Atunwa, dan jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), ya kalubalanci nasarar gwamna AbdulRahman AbdulRazaq a zaben Gwamnonin Jihar.

Naija News ta fahimci cewa dan takarar PDP a zaben gwamna a shekarar 2019 na kalubalantar zaben AbdulRazaq a kotun bisa dalilin cewa gwamnan ya gabatar da takardar shaidar kammala makarantar sakandare ta karya wanda bai cancanta ba.

7. Shugaba Buhari ya wallafa Matakai da Manufofi kan sabbin Ministocin da ke shigowa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya fada da cewa Ministocin da ke shigowa zasu yi aiki ne bisa tsari da karbar umarni.

Naija News ta gane da cewa Shugaba Buhari ya sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da aka sanya a shafin yanar gizon Twitter, ranar Laraba, 14 ga Agusta da ta wuce da yamma.

8. Gidan Majalisar Wakilai ta yi kirar zama ga Emefiele, NNPC, shugaban DSS

A ranar Alhamis din da ta gabata ne majalisar wakilai ta yi kirar gaugawa ga  Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele; Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari; da Babban kwamandan Hukumar Kwastam na Najeriya, Col. Hameed Ali (retd.); da Darakta-Janar, Ayukan Jiha, Yusuf Bichi.

Naija News ta fahimci cewa an yi masu kirar zaman ne saboda gazawar su ga halartar sauraron karar da majalisar ta shirya kan matsalar tashoshin jiragen ruwa a cikin kasar.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNews.Com