Uncategorized
Gwamnan Jihar Kwara ya gabatar da Matashiya mai shekara 26 a matsayin Kwamishina
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara, ya nada Miss Joana Nnazua Kolo, mace mai shekaru 26 da haihuwa da ke hidimar bautar kasa (NYSC), a matsayin kwamishina.
Naija News ta ba da rahoton cewa Matashiyar mai shekaru 26 na daga cikin kwamishinoni mata hudu wadanda aka zaba da mika sunayensu ga majalisar dokokin jihar Kwara a ranar Talata, 17 ga Satumbar don tantancewa.
Kolo, ƙaramar yarinya a tarihin jihar, zabbbiya a cikin jerin sunayan kwamishinoni, ta kammala karatun digiri dinta ne a Makarantar Kimiyya ta Jami’ar Kwara (KWASU), ƙwararrace kuma wajen fafutukar ci gaban al’umma.
Idan har aka tabbatar da ita daga Majalisa a matsayin, za ta zama kwamishina mafi karancin shekaru a Najeriya, zata kuwa dauki matsayin karancin shekaru daga Oluwaseun Fakorede, Kwamishana mai shekaru 27 a jihar Oyo.
Naija News Hausa nada sanin cewa Kolo har yanzu tana cikin hidimarta na bautar kasar, watau “National Youths Service Corps” NYSC a Jigawa, inda take koyarwa a Makarantar Sakandare ta Model Boarding Secondary School Guri.
Za’a kuwa gudanar da nata binciken ne akan kujerar majalisar minista bayan da ta kammala hidimar NYSC dinta a makonni biyu da ke gabatowa.