Jami’an Sojojin Najeriya sun kame wasu yan Mata biyu da suka yi kokarin shiga yankin Sojojin don kai masu hari

Wasu yan mata biyu da ake tugumar su da zaman yan Boko Haram su fada hannun Sojojin Najeriya. Rahoto ta bayas daga bakin wani Jami’in tsaro na NSDCC mai suna Ibrahim cewa an kame yan matan ne biyu a daren Laraba 19, ga watan Disamba 2018, shiyoyin karfe tara 9 na dare a yankin Konduga ta Jihar Borno.

Bayan an kame su an iya gane da cewa guda cikin yan matan mai suna Fatima Muhammed Kabir a na sanye da rigan bama-bamai a jikin ta. an kame ta ne da abokiyar ta mai suna Amina Salihu a wata gareji motoci a babbar hanyan Borno. sun bayyana cewa wannan shiri ne na kai hari a yankin Maiduguri.

Naija News ta ruwaito Wasu yan hari sun kai farmaki da har sun kashe mutane 14, sun kuma yiwa mutane 17 rauni a daren Lahadi da ta gabata, a wata kauye, mai suna Ungwan Paa-Gwandara a yankin Jema’a na Jihar Kaduna.

A bayyanin shi Ibrahim, ya ce wasu yan kungiyar Boko Haram din da kimanin mutane arba’in 40 su tabbatar da cewa su fita, kuma sun musunci kungiyar ta’addan nan, kuma sun bayar da kayakin harin su ga jami’an tsaro.

“Mun musunci kungiyar ta’adda ta boko haram, kuma a halin yanzu muna sallah so biyar a rana fiye da yadda muke yi a cikin jejin sambisa” in ji ‘yan ta’addan da suka tuba.

Karanta kuma Jam’iyyar PDP a Jihar Benue sun bayyana bacin ran su game da matakin da gwamnatin tarayya ta ki ta yi a kan zargin da ake yi wa shugabannin miyetti da laifin kisan gillar da aka yi a jihar.

‘Yan sanda sunyi Gwagwarmayar hana tashin Bomb ta Tsarin wata yar Yarinya A Maiduguri

An Gwagwarmayar hana fashewar Bam a Borno

Ya makonni kadan da Kirsimati, ‘yan sanda a Jihar Borno sun ce mutanen su sunyi gwagwarmaya da nasarar kan tsayar da wani harin bam a ranar Laraba a Maiduguri.

Kwamishinan ‘yan sandan, Mista Damian Chukwu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a kan waya cewa, lamarin ya faru ne kimanin karfe 8:30 na yamma a garin Maiduguri.

Chukwu ya bayyana cewa wata matashiyar yarinya ta yi ƙoƙari ta tsaga tsakanin yan tsaro, ganin haka jami’an tsaron suka harbe ta tare kunshi bam din wanda aka hada da (IEDs) a jikinta.

Ya ce wannan fashewar ya wasar da yarinyar a yankuna, yana mai cewa babu wadanda suka mutu ko samu rauni a harin.

Kwamishinan ya kara da cewa an tura ma’aikatan Haramtacciyar (EOD) da kuma sanarda yankunan.

Naija News ta ruwaito Yan Hari Sun Kai Farmaki A Madagali

Karanta KumaYan sanda sun karbi rajistan mutane 104,289 daga’ yan Najeriya bisa bukatar su da tanmanin mutane 10,000 kawai.