Mahara da Bindiga sun sace mutane 11 a Jihar Rivers

‘Yan hari da bindiga a Jihar Rivers sun hari wata motar Toyota Sienna SUV da ke kan tafiya daga hanyar Abuja zuwa Port-Harcourt, inda suka tare motar, suka kuma sace direban tare da fasinjoji goma (10) dake cikin motar, anan karamar hukumar Abua – Odual.

Muna da sani a Naija News da cewa hare-hare ya soma yawa a Jihar Rivers. A baya mun ruwaito da cewa wasu ‘yan hari da bindiga sun sace ciyaman na Jam’iyyar APC a wata yankin Jihar Rivers.

Mun samu rahoto ne da cewa ‘yan hari da ke sanye da abin rufe ido sun fada wa motar ne da hari a anan mahadin hanayar Rumuekpe da ke nan Emohua, karamar hukumar Jihar.

“Maharan sun fito ne daga cikin daji suka fada wa motar da hari, suka kuma sace direban motar da fasinjoji da ke ciki” inji wani mazaunin shiyar da ke da sanin yadda abin ya faru.

Ko da shike bai bayyana sunan sa ba, amma ya bayyana da cewa sun fito ne daga cikin dajin da harbe-harben bindiga, daga nan suka sace mutanen da ke cikin motar hade da direban sa.anan suka bar motar suka wuce” inji shi.

“Na cinma motar Sienna din ne da safiya misalin karfe 9 na safe, sa’an da na dawo kuma misalin karfe 11, na kara cinma motar a wajen” inji shi.

“Na san direban, mukan kira shi da suna ‘Star’. Mun yi kira ga taimako da muka gane da abin da ya faru, ina kuma addu’a ga Allah ya sa da shi da fasinjojin sun kubuta daga wannan harin” inji shi.

A yayin da aka karbi rahoton nan, kakakin jami’an tsaron Jihar, Mista Nnamdi Omoni, ya fada da cewa bai samu cikakken bayyani ba tukunna game da harin.

 

Karanta wannan kuma: Dan takaran Sanata a Jihar Kwara ya kure mutuwa sakamakon harbin ‘yan hari da bindiga

An sace Onuoha, babban mai bada shawara ga Gwamna Nyesom Wike

Mun samu tabbacin labari da cewa ‘Yan hari da bindiga sun sace babban mai bada shawara ga Gwamnan Jihar Rivers, Shugaba Anugbom Onuoha.

Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar sun tabbatar mana da wannan cewa an sace shugaba Anugbom Onuoha, babban mai bada shawara ga Nyesom Wike, Gwamnan Jihar River.

An saci Onuoha ne a daren jiya bayan jami’an tsaron ‘yan sanda sun yi musayar wutan harsasu da ‘yan hari a wata gidan nishadin Onuoha da ke nan anguwar Ada George, a nan Port Harcourt.

Mai yada yawun yankin dakarun ‘yan sandan Jihar, DSP Nnamdi Omoni ya ce, maharan su fito ne sanye da kayaki iri ta sojoji.

“Wannan abin takaici ne, kuma ba mu ji dadin hakan ba, zamu fita don neman ribato shi daga hannun maharan ba tare da bata lokaci ba” in ji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da safen nan da cewa ‘yan ta’adda sun fada wa dan takarar Gwamnan Jihar Taraba daga Jam’iyyar APC, Sani Danladi da hari har sun kashe mutane ukku a take.

“An rigaya an aika wa sauran hukumomin tsaro sako don samun nasarar ribato shi ba tare da bata lokaci ba” inji Nnamdi.

Ya ce “Mun bukaci al’umma duka su kira mu da wuri ga duk wata kula ko alamu da zai iya sa mu gano inda ya ke kuma mu ribato shi ba tare da wata matsala ba”.

Karanta kuma: An kashe mutane Uku, wasu kuma sun yi raunuka a sakamakon wata hari da ‘yan hari da bindiga suka kai yankin Jema, Jihar Kaduna