Labaran Nishadi
An sace Onuoha, babban mai bada shawara ga Gwamna Nyesom Wike
Mun samu tabbacin labari da cewa ‘Yan hari da bindiga sun sace babban mai bada shawara ga Gwamnan Jihar Rivers, Shugaba Anugbom Onuoha.
Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Jihar sun tabbatar mana da wannan cewa an sace shugaba Anugbom Onuoha, babban mai bada shawara ga Nyesom Wike, Gwamnan Jihar River.
An saci Onuoha ne a daren jiya bayan jami’an tsaron ‘yan sanda sun yi musayar wutan harsasu da ‘yan hari a wata gidan nishadin Onuoha da ke nan anguwar Ada George, a nan Port Harcourt.
Mai yada yawun yankin dakarun ‘yan sandan Jihar, DSP Nnamdi Omoni ya ce, maharan su fito ne sanye da kayaki iri ta sojoji.
“Wannan abin takaici ne, kuma ba mu ji dadin hakan ba, zamu fita don neman ribato shi daga hannun maharan ba tare da bata lokaci ba” in ji shi.
Naija News Hausa ta ruwaito da safen nan da cewa ‘yan ta’adda sun fada wa dan takarar Gwamnan Jihar Taraba daga Jam’iyyar APC, Sani Danladi da hari har sun kashe mutane ukku a take.
“An rigaya an aika wa sauran hukumomin tsaro sako don samun nasarar ribato shi ba tare da bata lokaci ba” inji Nnamdi.
Ya ce “Mun bukaci al’umma duka su kira mu da wuri ga duk wata kula ko alamu da zai iya sa mu gano inda ya ke kuma mu ribato shi ba tare da wata matsala ba”.
Karanta kuma: An kashe mutane Uku, wasu kuma sun yi raunuka a sakamakon wata hari da ‘yan hari da bindiga suka kai yankin Jema, Jihar Kaduna