Uncategorized
Asalin naman Kilishi da dandalin sa
Shirin naman Kilishi da yadda ake shirya shi
Hausawa na da ire-iren abinci da su ke ci dabam-dabam, haka kuwa akwai ire-iren nama da ake ci a kasar Hausawa da dama. A kowace Jiha ko yanki ta kasar Najeriya, akway ire-iren abinci da kowane yanki ke ci da kuma ji da ita sosai, kamar yadda al’adun mu suka zama dabam-dabam haka kuwa kowane yanki ke da irin na ta salon abinci.
Ire-iren abinci da ake ci a kasar Arewacin Najeriya sune kamar haka;
- Tuwon dawa
- Tuwon Shinkafa
- Taushe
- Masa
- Dage-dage
- Kosai
- Hoce
- Suya
- Kilishi
- Hura da Nono; da dai sauransu.
Zamu tattauna daya daga cikin wadanan da na lisafta a sama; watau Kilishi.
Kilishi
Naman Kilishi na daya daga cikin abincin da malam bahaushe ke ji da ita. Kilishi abu ne mai dadi kwarai da gaske.
Ko da shike malam bahaushe ne aka fi sani da cin naman kilishi, a halin yanzun nan ma, da yawa ga al’umman kasar Najeriya sun fada wa son cin naman Kilishi, musanman ga Matasan kasar gaba daya.
Yadda ake Shirya Kilishi
Kilishi ya tsiro ne daga naman Suya, akan shirya Kilishi ne daga namar Shanu, Rago, ko naman Akuya. ana iya shirya Kilishi daga kowane irin nama da na lisafta a sama.
- Bayan an yanka naman, sai a tsarrafa shi kamar fefa don ya bushe da wuri.
- Sai a kada garin da aka shirya da ga kuli da ruwa dadai yadda ba zai yi ruwa da yawa ba
- Sai a kayan dandano da gishiri da albasa
- wasu ma kan sa zuman kadan don kara masa dandano
Bayan an kada wannan, sai a shafa hadin ga naman da aka rigaya aka yanke aka kuwa shinfida, sai a shinfida shi ga rana dan ya bushe da kyau.
Bayan ya bushe da kyau, sai a jera su ga wuta don ya gadu da wuta da kyau. bayan haka naman kilishi na shirye don ci ga kowa.
A kan sayar da naman Kilishi a kasuwa, wajen mahauta, a gidan kallo, a hanya, har ma a kan hanya ga manyan garuruka. Kilishi kan dauki tsawon kwanaki da daman kamin ya baci.
Ina da fatan ka samu sani a yadda ake shirya Kilishi da kuma ire-ire abincin Hausawa da ake da shi a Arewacin kasar
Samu labaran Najeriya a kan hausa.naijanews.com
Karanta Kuma: Takaitaccen tarihin Ali Muhammad Idris da aka fi sani da Ali Artwork, dan Wasan kwaikwayo da kuma Mai Editan wasannai.