Mutane Takwas Sun Mutu Sakamakon Fashewar Gas a Katsina

Wau Mutane takwas ‘yan gida guda sun mutu a ranar Asabar din da ta gabata a wani fashewar gas a karamar hukumar Danmusa da ke jihar Katsina.

Maƙwabta ga mutanen da abin ya faru da su sun sanar da wakilin kamfanin dilancin labarai ta PUNCH da cewa lamarin ya kashe mata uku ne da yara biyar.

Wata majiyar ta ce, ‘yan sanda da suka zo daga baya sun yi kokarin rushe katangar gidan don su samu damar shiga gidan, amma a wannan lokacin zuwar su ya yi latti saboda mutanen sun rigaya sun kone harma baka iya gane fuskarsu kuma.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Katsina, SP Isah Gambo, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa, “Gaskiya ne. ”

Haka kazalika wani dan uwa ga mutanen da abin ya shafa mai suna, Mai Yusuf Lawal, shi ma ya tabbatar da faruwar.

Ka tuna Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Kimanin mutane 28 sun kone kurmus fiye da gane wa a ya yin wata sabuwar hadarin wani mota da ya afku a kan babbar hanyar Ningi da ke jihar Bauchi.

“Wannan mummunan labari ne kuma abin bakin ciki ne ga mutane 28 daga dangi guda su mutu a hadari guda a cikin rana guda. Abin da bakin ciki a gaskiya.” inji Abdullahi Yamadi, dan uwa ga wadanda suka mutu a hadarin.

Abin Takaici! Gobara Ya Kone Wata Shiyar Kwalejin Kimiyya ta Tarayya da ke Bauchi

Abin bakin ciki ne a ranar Lahadin da ta gabata ga daliban Kwalejin Kimiyya ta Tarayya da ke Bauchi, a lokacin da gobara ta tashi a kan dakin kwanan wasu daliban hade da wani dan jarida a kauyen Gwallameji.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana da cewa gobarar ta fara ne da misalin karfe 1:30 na rana a daya daga cikin dakunan da ke gidan Tinubu kafin ta bazu zuwa wasu dakuna.

Duk da kokarin mazauna da masu nuna juyayi, sun yi iya kokarinsu don ganin sun lafar da gobarar amma duk kokarinsu a banza ne.

A cewar wani mazaunin gidan, David Adenuga wani Dan Jarida da ke aiki a gidan Jaridar Nation ya ce yayin da yake ba da labarin abin da ya faru kamar mafarki ne a gare shi kuma ya rasa dukkan kayayyakinsa a wutar.

Ya kara da cewa lallai babu wutar lantarki a lokacin kuma har yanzu ba a san musabbabin barkewar lamarin ba. Ya ce wutar ta shafi dakuna tara yayin da ma’aikatar kashe gobara suka isa wajen da taimaka wajen kashe wutar daga yaduwa zuwa sauran dakuna.

A cewar wata ‘yan macce, daliba da gobarar ta shafa, ta ce ba ta san inda za ta fara ba, abin da za ta yi ko ta inda za ta kasance yayin da wutar ta ƙone dukkan takaddun ƙima da shaidar karatunta duka zuwa toka.

Wani wanda abin ta rutsa da shi, dan Jarida tare da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN, Saheed Ola, ya ce kayan aikin nasa da sauran kayan masarufin sun tafi tare da wutar amma ya gode wa Allah kan rayuwarsa.

Wani shaidar gani da ido shi ma ya kara da cewa gas din dafa abinci da dalibai ke amfani da shi ya taimakawa wutar da yaduwar, yana mai cewa galibin dakunan suna dauke da ‘gas na dafa abinci’

Gobara Ya Lashe Shashen Gidan Gwamnatin Jihar Neja

Naija News Hausa ta karbi rahoton yadda Gobara ta kame ofishin Sakataren dindindin na gidan gwamnatin jihar Neja, sakamakon hadewar wayar wutar lantarki.

Rahoto ya bayar da cewa ya kame ne da gobara a yayin da ake kan aiki da gyara gidan gwamnatin. Gobarar ya dauki sama da mintuna 15 kafin wasu ma’aikatan hukumar kashe gobara ta jihar suka isa wajen don tsayar da gobarar da yaduwa.

A bayanin Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), an gano ma’aikatan Ofishin suna gudu don tsira da rayukansu kafin ma’aikatan hukumar kashe gobara suka isa da manyan motoci uku a wajen.

Sun bayyana da cewa kayan aiki na ofishin, masarufi da takardu masu mahimmanci duk sun kone a cikin gobarar.

Mataimakin shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Neja, Malam Salihu Bello, a yayin zanta da manema labarai ya bayyana da cewa saurin isar ma’aikatan kashe gobarar ya taimaka kwarai da gaske wajen rage munin alamuran.

Ya fada da cewa rashin manyan motocin kashe gobara a gidan gwamnati ba da niyya ba ne yayin da ake shirin tsaida daya a wajen don saurin magance irin wannan a gaba.