Connect with us

Uncategorized

An kame Barayi Hudu masu sace-sacen Mutane a Jihar Neja

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotun Majistare da ke a garin Minna, babban birnin Jihar Neja ta bada umarnin a dakile wasu mutane hudu da aka gane da laifin sace mutane.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa kotun tayi hakan ne bayan da aka  gabatar da karar mazaje hudu da suna, Legbo Yasaba, Ndako Adamu, Makun Mohammed da Baba Salla akan zargin sace-sacen mutane.

Jami’in tsaro da ya gabatar da kara, ASP Daniel Ikwoche ya bayyanar da karar ne ga kotu bayan da suka karbi kiran kula da kuma kara mai tabbaci daga wani mai suna Mohammed Gbako daga kauyan Etsu Audu, a karamar hukumar Agaie, ranar 5 ga watan Yuni da zancen gane su hudun da kokarin kadamar da sace-sacen mutane a yankin.

A bayanin jami’in tsaron, Ikwoche, ya fada da cewa mista Gbako ya sanar da su da cewa bayan da ya tashi daga barci a wata safiya a gidansa, sai ya tarar da wata wasika da aka wallafa da kuma jiye kofar gidansa.

“Marubucin wasikar ya bukace ni da biyan kudi naira miliyan biyar (N5m) ko kuma kuma ya sace ni da iyalai na” inji bayanin mai bada kara ga jami’an tsaro.

“Da jin hakan sai rukunin tsaron mu ta dauki mataki a gaggauce don kame wanda ya wallafa wasikar. Da muka kuma samu kame daya daga cikinsu, sai ya furta da cewa lallai ya hada kai ne da mutane Uku don shirya da yin hakan” inji Ikoche.

Jami’in tsaron ya kara da cewa lallai wannan laifin ya karya dokar jihar Neja da kasa.

A haka, Alkalin da ke jagorancin karar a kotu, Hauwa Yusuf ta bada umarnin cewa a dakile mutane hudun, ta kuma daga karar zuwa ranar 1 ga watan Yuli 2019 don karshe karar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa wani barawo da aka kame a  Jihar Neja ya bayyana cewa kungiyar su kan sace Mata ne da ake shirin Aurar da su ko kuma wadda aka gama auren ta bada jimawa ba.