Connect with us

Uncategorized

Jihar Neja: Mu kan Sace Mata ne da ake batun Aurar dasu ko wadda aka gama Auren ta – inji Barawo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wani barawo da Jami’an tsaro suka kame a Jihar Neja ya bayyana cewa kungiyar su kan sace Mata ne da aken kusa da Aurar da su, ko kuma wadda aka gama auren ta bada jimawa ba.

“Mukan sace su don mun gane da cewa saurayi da ke batun auren yarinyar ko kuma wanda ya yi sabon aure aka sace matarsa zai bada hadin kai wajen biyan kudi ba da jinkirta ba don ribato ta” inji shi.

Naija News Hausa ta karbi rahoto cewa Hukumar Jami’an ‘Yan Sandan Jihar Neja sun yi nasara da kame wani mamban wata rukunin barayi masu sace-sacen mutane a shiyar Kpakungu, a karamar hukumar Chanchaga ta Jihar Neja.

Barawon mai shekaru 25 ga haifuwa da suna Mohammed Yakubu, ya sace wata mata ne a Jihar, ya kuma boye ta da tsawon mako biyu da bukatar a biya shi kudi naira dubu dari da hamsin (N150,000) kamin ya sake ta.

Da aka kuma kama shi ya bada tabbacin cewa lallai ya sace matar mai suna Halima Ibrahim a ranar 11 ga watan Mayu, 2019.

“Muna daga shiyar karamar hukumar Katcha ne a Jihar Neja. Ina kuma da cikakken sanin cewa Aliyu Musa na zancen Auren Halima, na kuma san da cewa zai iya yin komai don neman yancin ta, a hakan ne na sace Halima” inji bayanin barawon.

“Na kira Aliyu ne da lambar Halima, na kuma bayyana mi shi cewa lallai na sace ta kuma sai ya ajiye kudi naira dubu N150, 000 a wata wuri kami na sake ta. Shi kuma sai ya yi roko da biyan naira dubu sittin da biyar (N65,000).”

Don bada tabbacin kame barawon, kakakin yada yawun jami’an tsaron Jihar Neja, Muhammad Abubakar, ya bayyana ga manema labarai cewa lallai rukunin tsaro da ke a shiyar Kpakungu ne suka kame barawon, bayan da suka karbi wata kirar kula a Ofishin su kan sace Halima.

Ya bada tabbacin cewa Halima ta samu yanci an kuma dakile barawon a Ofishin Jami’an tsaro a yayin da ake shirin  gabatar da shi a kotu, bayan an kare bincike.