Connect with us

Uncategorized

Ambaliyar Ruwa ya tafi da Dan Sanda, Soja da wasu mazauna a Zamfara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jarumin Sojoji daya, Dan Sanda, da wasu Mutane biyu sun rasa rayukansu a yayin da ambaliyar ruwa ya fyauce da gidaje da barin akalla mutane 3,201 da rashin gidan zama a Zamfara.

Aƙalla mutane huɗu ne suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa da guguwa, a yayin da aka kiyasta mutane 3, 201 da bala’in ya shafa a cikin yankunan 21 a kananan hukumomi shida na jihar Zamfara.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne a wata sanarwa da aka bayar ga manema labaran DAILY POST daga hannun Babban sakataren zartarwa ga Hukumar ZEMA ta Zamfara, Eng. Sunusi Muhammad Kwatarkwashi.

Kwatakwashi ya bayyana da cewa mutane hudu ne suka mutu a wannan bala’in; ciki har da dan sanda da wani jami’in soja, tsakanin ranar 6 ga Yuni zuwa ranar 17 ga watan Yuli na wannan shekarar.

A karin bayanin Sakataren, ya sanar da cewa, kimanin kayan arziki da tattali da suka lallace a ambaliyar ta fi karfin miliyoyi kadan.

Haka kuwa ya lisafta kananan hukumomin da abin ya shafa, sun hada kamar haka; Talatar Mafara, Bungudu, Maru, Anka da Gusau kananan hukumomin jihar.

Koda shike ya ce bayyana da cewa an dauki matakan musanman don magance irin wannan mumunar al’amarin a nan gaba.

Shugaban hukumar ZEMA ya gargadi al’ummar jihar da su daina gine-gine kan hanyoyin da ruwa ke bi, da kuma tare da tsaftace magudanan ruwa domin hada gwiwa da taimaka wa gwamnatin jihar don ceton rayuka da kaddarorin mutane.

KARANTA WANNAN KUMA; Jami’an Tsaro sun Cafke wasu Mutane biyu a Kano da zargin Kashe ‘yan Shekara Takwas