Uncategorized
Bukola Saraki da Yakubu Dogara na ganawa da Gwamnonin Jam’iyyar PDP a Gombe
Shugaban Sanatocin Najeriya, Bukola Saraki na wata ganawa da Gwamnoni kasar hade da wasu manyan shugabannan Jam’iyyar Adawa, PDP.
Naija News ta fahimta da cewa zaman da suke yi a gidan hutun Gwamnoni a Jihar Gombe zai shafi tattaunawa ne akan wanda za a nada sabon Ciyaman na Kungiyar Gwamonin Jam’iyyar PDP.
Hakan ya biyo ne bayan ganewa da cewa saura ‘yan kwanaki kadan Ciyaman na Kungiyar, Gwamna Ibrahim Dankwambo, zai karshe shugabancin sa kan kujerar, kamar yadda dokar su ta bayar.
Zaman ya samu halartan Manyan shugabannan Jam’iyyar, kamar su; Kakakin yada yawun gidan Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara, Mataimakin shugaban kasa ga takaran zaben 2019, Mista Peter Obi, Ciyaman Tarayya na Jam’iyyar PDP, Prince Uche Secondus, Gwamna Seriake Dickson, daga Jihar Bayelsa, Gwamna Samuel Ortom, daga Jihar Benue, Gwamna Udom Emmanuel, daga Jihar Akwa Ibom, Gwamna Ifeanyi Okowa, daga Jihar Delta, da Gwamna Aminu Tambuwal, daga Jihar Sokoto.
Idan akwai wata bayani da ya biyo baya ga tattaunawar, zamu sanar a shafin mu ta Hausa.NaijaNews.Com