Connect with us

Labaran Najeriya

Hidimar Rantsarwa 29 Mayu: Ku ci gaba da shugabanci, Buhari ya gayawa Ministocin Najeriya

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Ranar Rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni ga Ministocin kasar Najeriya da ke kan shugabanci da ci gaba da hakan har sai ranar 28 ga watan Mayu, 2019.

Umarnin shugaba Buhari ke nan a lokacin da yake gabatarwa a hidimar bankwana ga Kwamitin Dattijan Tarayyar Najeriya, a fadar shugaban kasa ranar Laraba da ta gabata, a birnin Abuja.

Ka tuna da cewa Shugabancin Kasar Najeriya ta sanar a baya cewa za a gudanar da hidimar rantsar da shugaba Muhammadu Buhari a matsayin shugaban kasar Najeriya a karo ta biyu, ranar 29 ga watan 2019.

Naija News Hausa ta kula cewa Buhari ya bada daman hakan ne ga Ministocin har zuwa ranar 28 ga Mayu, kwana daya ga rantsar da shi shugabancin kasa bisa zaben 2019.

A taron, Buhari ya bukaci cewa a mika gabatarwan hidimar rantsarwan sa ga babban sakataren tarayyar Najeriya,  Boss Mustapha.

“Mun gode kwarai da gaske ga dama da kuma yanci da kaga ya dace da mu a shugabancin ka tsakanin shekaru 3 da rabi, muna mai nuna godiya” inji Ministoci 31 da suka yi shugabanci da Buhari.

KARANTA WANNAN KUMA; Wani Babban Jami’in Sojan Najeriya ya Kone a Gobarar Hadarin Mota