Gobarar Wuta ya kame shaguna Shidda a Kasuwar ‘Yan Rodi a Jihar Kano

Shaguna Shidda sun kame da gobarar wuta a Jihar Kano ranar Lahadi da ta gabata

Wasu sabbin shaguna shidda a ranar Lahadi da ta wuce a shiyar kasuwar Kofar Ruwa (Kasuwar ‘Yan Rodi) da ke a Jihar Kano, ya kame da gobarar wuta.

Kakakin yada yawun hukumar yaki da gobarar wuta na Jihar Kano, Malam Saidu Mohammed, a birnin Kano ranar Litini da ta wuce ya bada tabbacin gobarar wutar ga manema labarai, ko da shike ya fada da cewa harwa yau basu iya gane da sanadiyar gobarar wutan ba tukunna.

A cikin bayanin Mista Saidu, ya bayyana da cewa hukumar su ta karbi kirar gaugawa ne daga wani mutumi mai suna Usman Danladi, a missalin karfe goma na daren ranar Lahadi da cewa gobara ya kame da kasuwar.

”Da zarar da muka karbi kirar, hukumar ta aika a gaggauce da ma’aikata don dakatar da yaduwar wutar, sun kuma sami isa ga wajen a missalin karfe 10:15 na dare don dakatar da yaduwar wuta ga sauran shagunan” inji shi.

Ko da shike ya bada haske da cewa ba wanda yayi rauni ga gobarar wutan, amma dai an yi rashin kayaki da dama.

Mista Saidu ya gargadi masana’anta da zama da kula da kuma yin hankali da duk wata abin da zai iya jawo gobara a cikin kasuwa nan gaba.

Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya cewa Wasu Mutane bakwai sun kuri Mutuwa a wata Gobarar Wutan Motar Tanki da ya faru a shiyar Jihar Benue.

An gane da Gawar wata Yarinya a cikin Rijiya a Jihar Kano

Hukumar Yaki da Gobarar Wuta ta Jihar Kano, ta sanar da cewa ranar Talata da ta gabata sun gane da gawar wata ‘yar karamar yarinya mai shekaru 11 a ciki rijiya.

An gano gangan jikin yarinyar ne da aka bayyana sunan ta da Fatima Abdullahi a cikin wata Rijiya a shiyar Zaura Ganduje, a karamar hukumar Dawakin Tofa, Jihar Kano.

Kakakin yada yawun, Alhaji Saidu Mohammed, ya bayyana ga Kungiyar Manema Labaran Najeriya (NAN) a Jihar Kano cewa sun gane da hakan ne a safiyar ranar Talata da ta wuce.

A bayanin Mohammed da manema labaran NAN, ya bayyana cewa hukumar su ta karbi kirar gaugawa ne daga  Dawanawu cewa wata karamar yarinya ta fada a cikin rijiya.

Ya kara da cewa lallai kamin isar ma’aikata a wajen, yarinyar ta riga ta mutu.

Ya kuma bayyana cewa bayan da hukumar ta gane da gawar yarinyar, sun dauke ta da mika ta ga wakilin garin Zaura, Alhaji Idris Shua’ibu.

“Har yanzu ana kan bincike ga sanadiyar da ya kai yarinyar a cikin rijiyar” inji shi.

#Ramadan: Yashi ya rufe wasu Yara Shidda a Jihar Kano, Uku sun mutu daga cikin su

Ma’aikatan Hukumar Yaki da Gobarar Wuta na Najeriya (Fire Service), sun ribato ran wasu kananan yara shidda da yashi ya rufe da su a kauyan Kuka ta karamar hukumar Gezawa, a Jihar Kano.

Ko da shike abin da takaici, Kakakin yada yawun Hukumar ‘yan Fire Service na Jihar Kano, Malam Saidu Mohammed ya bayyana ga manema labaran NAN a ranar Talata da cewa Malaman Asibitin Gezawa sun bashi tabbacin cewa uku daga cikin yaran da aka tono daga cikin yashi sun mutu.

“Mun karbi wata kirar gaugawa daga rukunin mu ta Gezawa daga wani mutumi mai suna Malam Muktar, a missalin karfe 11:59 na safiya da cewa yashi ya rufe wasu yara shidda a wajen da suke tonon yashi”

“Da jin rahoton, sai Ma’aikata suka yi wuf zuwa wajen, a isar su kuma suka tono yaran, aka kuma isar da su a asibiti don binciken lafiyar jikunansu” inji Saidu.

Ga sunayan yaran a kasa kamar yadda aka bayar ga manema labarai;

  • Abdullahi Abdul         –  Da shekara 12 da haifuwa
  • Aminu Isa                   –  Da shekara 13 da haifuwa
  • Bashir Umar               –  Da shekara 13 da haifuwa
  • Naziru Rabiu              –  Da shekara 17 da haifuwa
  • Usman Garba             –  Da shekara 14 da haifuwa
  • Zakari Dandolo          –  Da shekara 12 da haifuwa

Mista Saidu ya kara da cewa sauran yara ukun na Asibitin Gezawa ana basu cikakken kulawa don ribato ran su.

“mun riga mun mika gawakin yara ukun ga Wakilin Kauyan Gezawa, sauran ukun kuma suna asibiti wajen kulawa, a yayin da zamu ci gaba da bincike akan yadda al’amarin ya faru” inji bayanin Mista Saidu a ranar Litini da ta gabata.

KARANTA WANNAN KUMA: Mazauna Jihar Kaduna sun kai hari a babban hanyar Kaduna-Zaria da Kaduna-Lagos, sun katange manyan hanyoyin da kone-konen tayoyi da wuta don nuna rashin amincewar kisan wani da ‘yan sanda suka yi.

Gobarar wuta ya kame Shaguna Takwas a Jihar Katsina

A yau Jumma’a, 5 ga watan Afrilu, Hukumar Yaki da Gobarar Wuta ta Jihar Kano sun gabatar da cewa gobarar wuta ya kone shaguna takwas a safiyar ranar Jumma’a ta yau a shiyar Randabawul ta Muletara da ke Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gobarar wuta ya kame wani Makarantar Sakandiri a Jihar Kano

Alhaji Saidu Mohammed, Kakakin Hukumar ya bada tabbacin hakan ga manema labarai da cewa abin ya faru ne a missalin karfe shidda na safiyar yau (Jumma’a).

Ya gabatar da cewa sun karbi wata kirar gaugawa a Ofishin su daga bakin wani da ke a shiyar da abin ya faru.

“Hukumar mu da ke yankin Dawanua ta karbi Kirar gaugawa ne da safiyar yau Jumma’a daga bakin Aliyu Mansir da cewa gobara ya kame wasu shaguna a shiyar Randabawul ta Muletara” inji Mista Saidu.

“Da jin hakan, Hukumar mu ta yi wuf da motar kashe wuta tare da Ma’aikata zuwa wajen da abin ya faru. motar ta isa wajen ne da Ma’aikata missalin karfe bakwai da sauran ‘yan mintoci (6:58am). Ma’aikata kuma suka dakatar da yaduwar wutar” inji shi.

Ko da shike, a wannan lokacin, ba a iya bayyana ko menene ya jawo sanadiyar gobarar wutan ba, amma dai an samu kashe wutar daga yaduwa.