Uncategorized
Ana kalubalantar nasarar da Tambuwal ya samu a Jam’iyyar APC tun 2014
‘Yan APC sun maka Tambuwal kara a gaban babban Kotun Najeriya
- Wasu ‘Yan APC su na karar nasarar da Tambuwal ya samu a zaben 2014
- ‘Yan takarar sun ce bai dace Jam’iyya ta saida Gwamnan tun a farko ba
- Lauyan APC ya koma bayan ‘Yan takaran bayan Tambuwal ya koma PDP
Yan Jam’iyyar APC sun shigar da karar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sokoto gaban Kotu inda ta ke nema a sauke Gwamnan daga kujerar sa. APC tace ba a bi matakin da ya dace tun farko wajen tsaida Tambuwal takara ba.
A kwanakin baya Sanata Umar Dahiru da kuma Aliyu Abubakar Sanyinna sun maka Tambuwal a manyan Kotun Kasar inda su ke kalubalantar nasarar da ya samu na lashe zaben fitar da gwani da aka yi a Jam’iyyar APC a 2014.
Jam’iyyar mai mulki ta juyawa Gwamnan baya ne saboda sauya-sheka da yayi zuwa PDP. Yanzu Abduganiyu Arobo wanda shi ne sabon Lauyan APC a shari’ar da ake yi da Gwamnan ya marawa Dahiru da Sanyinna baya a Kotu.
APC ta dauko hayan sabon Lauyan ne a madadin Jibrin Okutepa wanda a baya ya rika kokarin kare Aminu Tambuwal kafin ya bar Jam’iyyar. Yanzu Arobo da sauran Lauyoyi sun yi taron dangi su na kalubalantar Gwamnan.
Kafin a dage shari’ar, Lauyan da ke kare Abokan hamayyar Gwamnan watau Roland Otaru ya fadawa Alkali Mohammed Dattijo cewa wadanda su ka zabi Tambuwal a matsayin ‘Dan takarar APC a zaben 2014 ba su cancanta ba.
KATANTA: Dariya A Jihar Neja Yayin da aka fara biyan Yan Fansho kudin sallama