DSS Sun Kame Wanda Ya Shirya Bidiyon Shairi Kan Auren Shugaba Buhari Da Zainab, da Sadiya Farouq

Ofishin Hukumar Tsaron Kasa (DSS) at sanar da kama Kabiru Mohammed, mutumin da ake zargi da kulla shellan karya kan auren Shugaba Buhari.

Naija News ta tuna cewa an bayyana wani rahoto a kusan  Oktoba ta shekarar 2019 cewa Shugaba Buhari ya shirya aure da Ministan Kulla da Al’umma, Sadiya Umar Farouq.

Day Dr. Peter Afunaya, kakakin yada yawun hukumar ke bada bayani kan lamarin, ya ce, an fara gudanar da bincike ne, biyo bayan korafin da Ministan Kudi ya yi wa Ma’aikatar.

Naija News ta fahimci cewa an kama Mutumin, mai shekaru 32 ga haifuwa ne saboda kirkirar wata bidiyo da kuma yada bidiyon karyar wanda ke nuna Shugaba Muhammadu Buhari na bikin auren Ministan Kasa, Zainab Ahmed da Ministan Harkokin Al’adu da Ci gaban Jama’a, Sadiya Farouq.

Ya bayyana da cewa sunyi kamun ne bayan da daga cikin Ministocin tayi gabatar da karar a ofishin su da neman su kame duk wanda suka gane da shirya da kuma watsar da bidiyon.

“Hukumar mu kuwa ta gane da kuma kame wanda ya shirya da kuma watsar da bidiyon. Sunansa Kabiru Mohammed. Dan Kano ne da kuma shekara ga 32 haifuwa. Ya kuma karanci yaran Fulfude da Hauda a makarantar jami’a ta Federal College of Education, Kano, da kuma karatun sashin Sadarwa daga Aminu Kano Islamic School.“

“Ya riga ya amince da aikata hakan kuma mun ci gaba da bincike kan dalilin hakan.” Inji shi.

Mutumin kuwa a ganewar Naija News Hausa ya nemi afuwa kan laifin sa da kuma bayyana cewa lallai aikin Sheidan ne. Ya kuma kara da cewa shi dan Jam’iyyar

Kwakwasiya ne a jihar Kano.

2023: Kalli Yankin Da Matasan Arewa Suka Ba wa Goyon baya Ga Shugaban Kasa

Wata gamayyar kungiyoyin matasan Arewa ta yi kiran da a sauya shugabancin kasar daga arewa zuwa yankin Kudu maso Kudu kafin zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Hadin gwiwar, a karkashin kungiyar ‘Arewa Youths Assembly’, ta ce ba zai zama da adalci ba ga Arewa ta fito da shugaban Najeriya na gaba tare da lura cewa yankin ta mamaye matsayin fiye da sauran yankuna tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kanta a 1960.

Saboda haka, kungiyar sun bayyana cewa sun fara neman dan takara daga Kudu maso Kudu mai shekarun haifuwa tsakanin shekara 40 zuwa 50 da zai karbi shugabanci daga Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Shugaban kungiyar, Mohammed Salihu Danlam ne ya bayyana wannan matsayin kungiyar a gaban wani taron manema labarai a jiya.

Yayin da Danlam ke jawabinsa, ya bayyana cewa dan takarar “dole ne ya kasance yana da cudanya na kwarai da kasashen duniya, dole ne ya shiga cikin tsarin mulki na lokaci mai tsawo, ya kasance da kwarewar sadarwa, dole ne ya zama iya ba da fifikon tabbatar da adalci na zamantakewa da kyautatawa kan ci gaban tattalin arziki.”

“Arewa ta mamaye matsayin shugabancin kasar nan tun lokacin da ta sami ‘yancin kai, fiye da kowane yanki; lokaci ya yi da matasan Kudu maso Kudu za su fitar da shugaban kasa shekarar 2023,” in ji Danlam.

“Najeriya kasa ce da ke baya a tsakar cin gaba da alkawurai da kuma zama cikin duhun rashin adalci. Muna rayuwa da rashin tabbas. A yadda abubuwa suke a yanzu, bamu da masaniyar al’ummar da za su faru idan Arewa ta ci gaba da mulki a 2023. inji shugaban Kungiyar Matasan Arewa.

 

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 31 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 31 ga Watan Disamba, 2019

1. Shugaba Buhari ya Tsauta Wa Ministoci Da Mataimakansu da Tafiye-tafiye

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da wasu sabbin umarni da ke takaita adadin lokuta da Ministoci zasu iya tafiya a cikin shekara guda.

Ministan yada labarai, al’adu da yawon shakatawa, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan a ranar Litinin.

2. Buhari Da Bakare Sunyi Wani Ganawar Siiri A Aso Rock

Fasto Tunde Bakare, babban Fasto na Majami’ar Latter Rain a ranar Litinin, ya yi wata ganawar siiri da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa a Aso Rock Villa, Abuja.

Ganawar siiri da Bakare yayi tare da Shugaban kasar ta fara ne da misalin karfe 3 na rana, kuma ya dauki kusan mintuna 30 kamin karsheta a fahimtar Naija News.

3. Buratai Ya Kaurace Wa Taron Da Buhari Yayi Da Shugabannin Ma’aikata

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin din da ta gabata ya yi wata ganawar siiri da shuwagabannin ma’aikata a gidan gwamnati da ke Abuja, an yi imanin cewa taron itace na karshe ga shekara ta 2019.

An yi imanin cewa taron ya kasance ne kan zancen tsaron kasa daga hannun shugabannin tsaro.

4. Buba Galadima Ya Bayyana Wanda Shugaba Buhari yake Tsoro Fiye Da Allah

Buba Galadima, wanda shine tsohon kakakin kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari yana tsoron ‘yan farar fata, musamman gwamnatin Amurka fiye da Allah.

Naija News ta ruwaito cewa Galadima yayi wannan furucin ne yayin martani kan ikirarin da Lauyan Janar din kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya bayar cewa an saki Sambo Dasuki, tsohon mai ba da shawara kan harkar tsaro, da Omoyele Sowore, dan jaridar Sahara Reporters, bisa dalilan jin kai.

5. 2023: Buba Galadima ya aika da Gargadi mai karfi ga Tinubu game da Buhari

Alhaji Buba Galadima, jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da kuma tsohon abokin hamayya na Shugaba Muhammadu Buhari, ya koka da cewa shugaban kasar ba ya taba taimaka wa kowa.

A cikin bayanin Galadima, ya kara da cewa ba a san Buhari da taba taimakawa wadanda suka taimaka masa a harkan siyasa ba.

6. Gwamnatin Legas Tayi Ikirarin Kame Duk Asibitocin Da Suka gaza bada Kulawa ga wadanda suka jikkata da harbin bindiga

Gwamnatin jihar Legas ta yi kira ga dukkanin asibitoci da wadanda ke a fannin kiwon lafiya, hadi da wadanda ke cibiyoyin kiwon lafiya na gwamnati da na masu zaman kansu da ke aiki a jihar da su daina yin watsi da wadanda ‘yan bindiga suka rutsa da su.

Gwamnatin jihar ta kuma nemi asibitocin da su janye daga halin guji da rashin bada kulawa ga masu mugun rauni a kan uzurin neman rahoton ‘yan sanda ko kuma bukatar samar da shaidar kudade kafin fara jinyarsu.

7. 2020: ‘Yan Najeriyar Za Su Fuskanci Mawuyacin Yanayi A Karkashin Mulkin Buhari – Shehu

Shehu Sani, tsohon Sanata wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a jagorancin Sanatoci na 8 na Najeriya, ya ce ‘yan Najeriya za su kara fuskantar wahala a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari a shekarar 2020.

Naija News ta samu labarin cewa tsohon dan majalisar ya yi wannan tsokaci ne yayin wani shirin rediyo a gidan Rediyon Invicta FM a Kaduna ranar Lahadin da ta gabata.

8. PDP Ta Kalubalanci APC Akan Yawan Karuwar Rashin Aiki A Najeriya

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sake yin tir da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kan karuwar rashin aikin yi a kasar.

A wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar PDP, Mista Kola Ologbondiyan, ya fada da cewa jam’iyyar APC cewa ta lallatar da harkokin kasar ta hanyar tafiyar da harkokin a siyasance da musanman kan yanayin rashin aiki a kasar, da kuma cewa su shirya don fuskantar kalubalan ayukansu a shekara ta 2023.

Ku sami kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau a shafin Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 30 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 30 ga Watan Disamba, 2019

1. Abinda Zai Faru Da Najeriya A Shekarar 2020

Aare Gani Adams, Sarkin Onakakanfo na Yarbawa ya bayyana abin da zai faru da kasar Najeriya a 2020.

A cikin bayanin Sarki Adamu, za a sami takunkumi da kalubalai daga bangarorin kasashe daban-daban na duniya a kan Najeriya a shekarar 2020.

2. Nnamdi Kanu Ya Bayyana Dalilin da ya sa ‘Allah Ke Fushi da Najeriya

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) kuma Daraktan Rediyon Biafra, Nnamdi Kanu, ya ce Allah ya na fushi da Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa Kanu ya yi wannan ikirarin ne yayin hirar sa da aka gabatar kwanan nan a Radio Biafra inda ya ba da sanarwar cewa “Biafra ita ce masarautar da kawai muke nema a kasar.”

3. Biafra: Nnamdi Kanu Ya Yi Zargi Kan Shugaba Buhari

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) kuma Daraktan Rediyon Biafra, Nnamdi Kanu, ya zargi ma’aikatan kamfanin Facebook a Najeriya da hada baki da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari don cire mabiyansa da rage sakonnansu a shafin sa na dandalin sada zumunta na yanar gizo, watau Facebook.

Naija News ta rahoto cewa shugaban IPOB din da ya yi wannan ikirarin a wata sanarwa kwanan nan da ya sanya hannu, ya ce abin ya yi muni kwarai da gaske cewa babbar shafin sadarwa ta yanar gizon tana karkatar da wasu daga mabiyanta zuwa wata asusun karya da aka bude da sunansa, don kawai a lalata kokarinsa ga samun ‘yanci ga Biafra.

4. Ba a Dakatar Da Obaseki Ba, Oshiomhole Kuma yaci gaba da Jagoran mu – APC

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Jihar Edo, Anselm Ojezua, ya ce shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, ba shine shugaban jam’iyyar a jihar ba.

Ojezua ya sanar da hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar bayan wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Edo ta Arewa a karamar hukumar Jattu-Uzaire, karamar hukumar Etsako ta yamma na jihar.

5. ISWAP: Musulmai Suna Allah Wadai Da Kashe Kashen Kiristoci – Shehu Sani

Tsohon Sanata a Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da kisan Kiristocin da membobin kungiyar Islamic State a Afirka ta Yamma (ISWAP) suka yi a kwannanan.

Ka tuna, Naija News ta ruwaito a baya da rahoton cewa membobin kungiyar ISWAP a ranar Kirsimeti sun kashe mutane goma sha daya, wadanda yawancinsu duk Kiristoci ne.

6. APC Da PDP Ba zasu Zantar da Ayyukan Majalisar Dattawa ba – Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce Jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba za su tantance ayyukan majalisar dattawa ba.

Shugaban Majalisar Dattawa ya sanar da hakan ne a ranar Asabar a jihar Yobe, yayin wani liyafar da aka gudanar don girmama masa.

7. ‘Yan Shi’a:‘ Yancin El-Zakzaky Ba A Hannun El-Rufai Yake ba – IMN Sun fada wa Gwamnatin Shugaba Buhari

Kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wacce kuma aka fi sani da suna Shi’a, ta yi Allah wadai da bayanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa ‘yancin shugabanta, Ibrahim El-Zakzaky ya dangana ne a hannun gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.

Naija News ta tuno cewa yan Shi’a sun yi kiran a saki El-Zakzaky ne bayan sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore.

8. Yadda DSS Suka Aiko Da ‘Yan Ta’adda Don Bubbuge Ni – Deji Adeyanju

Dan gwagwarmayar siyasa Deji Adeyanju ya zargi Ma’aikatar Tsaro ta Kasa (DSS) da aikar da wasu ‘yan ta’adda da suka yi masa mugun bugu a yayin zanga-zanga.

Naija News ta tuno da cewa wasu ‘yan ta’adda sun hari Adeyanju tare da sauran masu zanga-zangar neman a saki Omoyele Sowore a Abuja.

Ku samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Shugabansa Muhammadu Buhari Na Ganawar Siiri Da Shugabannan Hukumomi

Naija News Hausa ta fahimta a yau Litinin da cewa Shugaba Muhammadu Buhari yayi wata ganawar siiri da tare da wasu shugabannin hukumomi a nan Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Ko da shike ba a bada hasken dalilin taron ba, amma ana sa ran shugabannan za su tattauna ne kan sake duba yanayin tsaro a kasar da wasu zance kuma da ta shafi ci gaba.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa an yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yarda ‘yan ta’adda su raba kasar biyu ta hanyar addini.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya sanya wa hannu da kuma aka bayar ga manema labarai bayan wata kisa da ‘yan kungiyar ISWAP suka yi na kashe Kiristoci goam sha daya a ranar kirsimeti.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Asabar, 28 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Asabar, 28 ga Watan Disamba, 2019

1. Boko Haram: Shugaba Buhari Ya Roki ‘Yan Najeriya

An yi kira ga ‘yan Najeriya da kada su yarda ‘yan ta’adda su raba kasar biyu ta hanyar addini.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Garba Shehu ya sanya wa hannu da kuma aka bayar ga manema labarai a yau.

2. Jirgin Sama Dauke Da Tarin Mutane 100 Ta Rushe

Wani jirgin sama dauke da mutane 100 a cikinta ta fadi a Kazakhstan, inda tayi sanadiyar mutuwar a kalla mutane goma sha hudu, bisa fahimtar Naija News.

A cewar jami’ai, jirgin na Bek Air ya fadi ne jim kadan bayan tashinsa daga tashar jirgin saman ta Almaty da safiyar ranar Juma’a.

3. Tsohon Mashawarcin Tsaron Kasa, Dasuki Ya Bayyana Shirinsa Na gaba Bayan Sakinsa Daga Shekaru 4 Kame

Wani tsohon mai ba da shawara a kan tsaro na kasa (NSA), Kanal Sambo Dasuki, wanda ya samu ‘yanci kwanan nan bayan tsare shi da aka yi na tsawon shekaru hudu a kurkuku, ya bayyana cewa ba zai ba da wata hira ga manema labarai ba.

Dasuki, wanda shi ne Yarima na Khalifancin Sakkwato, ya yi wannan wahayin ne a cikin wata ganawa da manema labaran DAILY POST ta hanyar wani abokinsa, a Daren ranar Alhamis, 26 ga Disamba.

4. Jonathan Ya Shawarci Shugaba Buhari Kan Matakin Da Zai Dauka Ga Maharansa

Tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari da ta kama tare da tsananta wa ‘yan bindigar da suka kai hari gidansa a Otuoke, Jihar Bayelsa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, tsohon shugaban bai sami rauni ba a harin wanda mutane da yawa ke zargin cewa ana son ne kashe shi.

5. Shugaba Buhari ya bayyana Ra’ayinsa a kan Shugaban Majalisar Dattawa, Lawan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a yayin da yake ba da shawara ga dan Lawan, Ibrahim, a wajen bikin auren sa.

6. Ohanaeze Sun yi Magana kan Tsige Shugaban kasa Buhari

Kungiyar gamayyar al’adu na Igbo, Ohanaeze Ndigbo ta ce furcin da kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya yi na cewa akwai wasu rukuni a fadar shugaban kasa dake tafiyar da lamarin kasar ya isa ma kawai a tsige shugaban.

A cewar Shehu, Rukunin mutane ne masu nasarori da yawa ne da kuma girmamawa a kasar.

7. Wani Mutum Ya Bugi Matarsa Har Ga Mutuwa Ranar Kirsimeti

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Ogun ta kama wani mutum da aka sani da suna Mutiu Sonola, da laifin buge matarsa Zainab, har ga mutuwa a ranar Kirsimeti.

Kakakin rundunar, Abimbola Oyeyemi ne ya bayyana hakan.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau da kullum a shafin Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumm’a, 27 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumm’a, 27 ga Watan Disamba, 2019

1. Ayodele Ya Sanar da Annabcin 2020 A kan Buhari, Tinubu Da Sauransu

Wanda ya kirkiro cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Oke-Afa, Ejigbo Lagos, Primate Babatunde Elijah Ayodele ya fitar da annabce-annabce na shekarar 2020 akan Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari.

Mashahurin malamin ya yi wahayin ne a yayin taron INRI Evangelical Church of Spiritual Church na shekara da shekara.

2. Bakar Ranar Kirsimeti A Ikilisiyar RCCG Yayin Da Fasto, Dansa Da Diyarsa Suka Mutu Cikin Ruwa

Gabriel Diya, Fasto na Ikilisiyar Cocin Christian Church of God (RCCG) da ke a kasar Landan da ‘ya’yansa biyu, sun mutu a wani wurin wanka a Costa del Sol, a kudu na Spain a Kirsimeti.

Naija News ta samu labarin cewa Fasto na RCCG din da ‘yarsa, Comfort Diya ‘yar shekara 9, da dansa, Thanks-Emmanuel Diya, dan shekaru 16, duk sun fada cikin wata tafki.

3. Atiku Na Iya Fita Don Takara Ga Zaben Shugaban Kasa A PDP,  Shekarar 2023 – Inji Shugaban BoT

Shugaban, kwamitin amintattu na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Sanata Walid Jibrin, ya ce tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na da ‘yanci don neman tikitin takarar shugaban kasa a shekarar 2023.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Kaduna, jigon a jam’iyyar PDP ya ce duk wani mai so da kuma ke da cancanci a jam’iyyar daga kowane bangare na Najeriya yana da ‘yancin neman tsayawa takarar shugaban kasa a tsarin sa.

4. ISWAP ta Kashe Mutanen Da Suka Sace A Ranar Kirsimeti Da bada Hujjoji

Kungiyar Islamic State West Africa a ranar Kirsimeti ta yanke hukuncin kisa ga wasu fursunoni goma sha daya, wadanda yawancinsu Kiristoci ne.

Ahmad Salkida, wani dan jaridar da ya shahara wajen sanya ido kan ayyukan ta’addanci ne ya sanar da hakan.

5. Ba a tsananta wa Kiristoci ba a Najeriya – Sultan ya gaya wa CAN

Mai Martaba Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, ya ce ya kadu matuka da ikirarin Kungiyar Hadin Kan Kiristocin Najeriya (CAN) na cewa ana tsananta wa Kirista a kasar.

Naija News ta ba da rahoton cewa kungiyar Kiristocin ta goyi bayan hada Najeriya a cikin jerin kasashen da suka amince da tafiyar da hidimar addini da Amurka ta saki.

6. Fadar Shugaban Kasa tayi bayanin Dalilin da yasa DSS ta saki Dasuki Da Sowore

Fadar shugaban kasa ta ba da dalilan da ya sa suka sa aka saki tsohon mai bada shawara kan tsaro (NSA) ga shugaban kasa, Sambo Dasuki da jagoran zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, Ma’aikatar Tsaro ta kasa (DSS) a ranar Talata ta saki su biyun sakamakon umarnin daga babban lauyan hukumar kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

7. Gwamna Makinde yayi Magana akan Mutuwa Kafin Shekaru 30

Gwamna Seyi Makinde, Gwamnan jihar Oyo a ranar alhamis ya bayyana cewa yana tsoron kar ya mutu kafin ya cika karin shekaru 30.

Gwamnan jihar Oyo ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wurin bikin godiya don bikin zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 52 a Ikilisiyar St Peter’s, Aremo, Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Ka samu kari da Cikkaken Labaran Najeriya a Shafin Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 26 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 26 ga Watan Disamba, 2019

1. Boko Haram: Shekau Ya Saki Sabuwar Bidiyo Ranar Kirsimeti

Abubakar Shekau, shugaban kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram, ya fitar da sabon bidiyo a yayin bikin Kirsimeti na shekarar 2019.

Wani fitaccen dan Jarida, Ahmad Salkida ne ya tabbatar hakan ta sakin bidiyon a ranar Laraba, 25 ga Disamba.

2. Sambo Dasuki: Ba Ni da Wata Matsala da Buhari, A shirye Nike Don Fuskantar Shari’a

Tsohon mai ba Shugaban kasa Shawara kan Tsaro, NSA, Sambo Dasuki, a ranar Laraba, ya ce ba shi da wata takaddama a tsakaninsa da Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya ba da umarnin a saka shi shekaru hudu a kurkuku, duk da cewa ya cika sharuddan beli, kuma ya ce a shirye yake da ci gaba da shari’ar sa.

Dasuki ya yi magana ne yayin wata hira da rediyon Muryar Amurka, Sashen Hausa, an nakalto lokacin da aka tambaye shi ko akwai wata takaddama a tsakaninshi da shugaban, kamar yadda yake mayar da martani, ba ni da saɓani da kowa. Na fi wancan. Ba zan iya shiga cikin rikici tare da kowa ba.

3. Fadar Shugaban Kasa ta dauki zafi, Tayi Alkawarin Kalubalantar Sakin Dasuki da Sowore

Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan tsari tare da sakin mai zanga-zangar #RevolutionNow, Omoyele Sowore.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, Ma’aikatar Kula da Harkokin Tsaro ta Kasa (DSS) a ranar Talata da yamma ta saki Sowore daga tsarin da aka masa.

4. Oshiomhole Ya Ki Karban kyaututtukan Kirsimeti na Obaseki

Shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Comrade Adams Oshiomhole, ya yi watsi da kyaututtukan Kirsimeti da gwamnatin jihar Edo ta aika masa.

Mista Crusoe Osage, mai ba bada shawarwari ga gwamnan jihar Edo kan harkokin yada labarai da sadarwa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Benin a ranar Laraba.

5. Sambo Dasuki: Tsohon gwamna, Lamido Ya Kalubalanci Shugaba Buhari

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alh. Sule Lamido ya ce ba da izinin sakin Kanar Sambo Dasuki da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari tayi bai kai abin murna da ita.

Ya ce maimakon haka, yakamata ne ayi binbini da yanayin ne.

6. ‘Yan Boko Haram Sun Kai hari Garin Chibok, Sun Kashe Mutane Shida

Akalla mutane shida ne suka mutu da mata biyu da mayakan Boko Haram suka sace a ƙauyen Kwaranglum da ke jihar Borno.

Kwaranglum na kusan kilomita guda ne zuwa garin Chibok, hedikwatar karamar hukumar Chibok na jihar Borno.

7. Kungiyar ‘Yan Shi’a Ta El-Zakzaky sun halarci Coci Da Bayar da Kyautannai A Ranar Kirsimeti

Wakilan Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), wadanda aka fi sani da Shi’a a ranar Laraba sun halarci hidimar coci ta Kirsimeti a wasu sassan arewacin Najeriya.

A cocin daban daban na Advent, Samaru, Zariya, jim kadan bayan kammala hidimar, shugaban kungiyar, Farfesa Isa Hassan-Mshelgaru ya ce muhinmancin halartar wannan hidimar shine inganta soyayya, hakuri da fahimta a tsakanin yan Najeriya.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta yau da Kullum a Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 23 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 23 ga Watan Disamba, 2019

1. Shugabancin Kasa tayi Magana kan Zancen Buhari na Kafa Dokar Tsawan Shekaru 6 kacal a Mulki

Fadar shugaban kasa ta musanta rade-radin cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne ke bayan kudurin dokar shekaru shida kacal sau daya a karagar mulki wadda Majalisar Dattawa tayi watsi da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa dan majalisar da ke daukar nauyin kudurin ya kawo hakan ne don taimaka wa shugaba Buhari ga tabbatar da wa’adin mulki na uku.

2. TY Danjuma: Dalilin da yasa Fulani zasu ci gaba da mulkin Najeriya – Nnamdi Kanu

Shugaban kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya yi ikirarin cewa Fulani zasu ci gaba da shugabancin Najeriya saboda a haka suna da iko da sojoji, bangaren shari’a da hukumar INEC.

Nnamdi Kanu ya fadi hakan ne don mayar da martani kan kalaman tsohon Ministan Tsaro, Janar Theophilus Danjuma (Rtd).

3. Wata Kungiya ta aika da Gargadi mai karfi ga Amurka Don sanya Najeriya a jerin Kulawa

Wata kungiya da aka sani da suna “Coalition Against Terrorism and Extremism,” ta soke wani rahoto daga Shugaba Donald Trump na Amurka, wanda ya sanya Najeriya a jerin kasashe na musamman da suke wa kanlo shaho da dan kaza.

Kamfanin na Naija News ta ba da rahoton wata sanarwa daga bakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Michael Pompeo, wanda ya yi bayanin cewa Najeriya ta kasance cikin jerin kasashen da kasar Amurka ke danne dan cin mutuncin ‘yancin addini.

4. Shugaba Buhari Ya Bawa Jami’o’in Najeriya Sabuwar Umarni

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin sa ta dogara ne da jami’o’i don taimaka mata wajen aiwatar da ayyukan ta na yabo ta hanyar samar da manyan ayuka kan bincike da kirkire-kirkire.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Shugaban kasar ya yi wannan tsokaci ne a ranar Asabar, 21 ga Disamba a taron taro na 31 na Jami’ar Fasaha ta Tarayya, Akure (FUTA).

5. Sowore: Babban Lauyan Kasa, Malami Ya Musanta karbar wasika daga lauyoyin Amurka

Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN) ya karyata rahotannin da ke cewa ya karbi wata wasika daga lauyoyin Amurka kan la’antar ci gaba da tsare Omoyele Sowore.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ruwaito a baya da cewa Ma’aikatar (DSS) ta saki Sowore da Bakare bayan sun kwashe kwanaki 124 a tsare.

6. Obaseki Ya Zargi Oshiomhole Da Yin Jerin Sunan Kwamishanoni A Dakinsa

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya zargi Shugaban jam’iyyar na All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole da yin karya da zalunci.

Naija News ta tuno da cewa Adams Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo, ya gurbata bayanan da ke cewa yana kokarin shawo kan jagorancin Obaseki a jihar.

7. Shahararren Jarumin Fina-Finan Nollywood ya mutu a Legas

Samuel Akinpelu, wani fitaccen jarumin fim din Nollywood, wanda aka fi sani da ‘Alabi Yellow’, ya mutu.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Alabi Yellow ya mutu ne a ranar Lahadi, 22 ga Disamba a asibitin Hopewell da ke Ikorodu, jihar Legas, garin kasuwanci na Najeriya.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Mai Martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido Ya Karbi Nadin Da Gwamna Ganduje Yayi Masa

Rahoton da ke isa ga Naija News Hausa a wannan lokaci ya bayyana da cewa Mai martaba Sarki Sanusi Lamido Sanusi ya ba da sanarwar amince da nadin nasa a matsayin shugaban majalisar masarautar jihar Kano.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya baiwa mai martaba Sarkin Kano, Sanusi Lamido, kwana biyu don bayyana ra’ayinsa da mukamin da aka bashi ko kuma ya tsige shi daga kujerar sarauta.

A yau 20 ga Disamba 2019, Mataimakin gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakasai, wanda aka fi kira da suna Dawisu ya sanar da tabbaci da cewa sarki Sanusi ya amince da nadin da aka yi masa.

Sakon wadda aka wallafa a shafin yanar gizon zumunta na Twitter na kamar haka;

“Mai martabar, Sarkin Kano, Mallam Muhammadu Sanusi II, a yau, ya amince da nadin nasa da H.E @GovUmarGanduje ya yi a matsayin Shugaban Majalisar Masarautar Kano, wanda ya kunshi dukkan masarautuka 5 a jihar da sauran membobi.”

KARANTA WANNAN KUMA; ‘Yan Najeriya Ba Za Su Sake Barci Ba Da Sun San Abin Da Ke Gudana a Kasar – TY Danjuma