Connect with us

Uncategorized

Dariya A Jihar Neja: Yayin da aka fara biyan Yan Fansho kudin sallama

Published

on

Daruruwan tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jihar Nejan Nigeria ne sun yi dafifi a harabar ofishin hukumar fansho ta jihar domin karbar kudadensu na sallama daga aiki da hukumar kula da kudaden fanshon ta fara biya a ranar Litinin goma ga watan Disamban 2018.

Tsofaffin ma’aikatan dake cikin wani yanayi na nuna tausayi saboda yadda tsufa ya taso masu gadan gadan, sun share shekara da shekaru suna jiran wannan rana da wasu ma wakilansu ne suka zo karbar kudaden nasu saboda rai ya yi halinsa.

Wasu daga cikin wadanda Muryar Amurka ta zanta dasu sun nuna farin ciki matuka a kan samun kudaden fanshon, su kwatanta wannan a matsayin babbar rana a rayuwarsu, sun kuma ce wadannan kudade zasu taimakawa rayuwarsu.

Shugababn hukumar fanshon a jiha Nejan Alhaji Usman Tinau, yace sama da tsoffin ma’aikata 1,600 ne da suka hada da na jiha da na kananan hukumomi zasu samu kudadensu na sallama a wannan karon sakamakon samun kudi Naira miliyan dubu uku daga Gwamnatin jihar Nejan.

Sai dai wasu tsofaffin ma’akatan sun yi korafin cewa sunayensu bai fito cikin wadanda za a biya ba, amma Alhaji Usman Tinau yace wadanda basu samu ba a wannan karon suyi hakuri watakila nan gaba kadan sunayensu zasu fito.

 

KARANTA: Matakan Tsaro sun kama wani mai suna Musa Mora wanda aka taras da shi da makamai daga garin Babana a Karkarar Borgu ta Niger.