Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 30 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 30 ga Watan Disamba, 2019

1. Abinda Zai Faru Da Najeriya A Shekarar 2020

Aare Gani Adams, Sarkin Onakakanfo na Yarbawa ya bayyana abin da zai faru da kasar Najeriya a 2020.

A cikin bayanin Sarki Adamu, za a sami takunkumi da kalubalai daga bangarorin kasashe daban-daban na duniya a kan Najeriya a shekarar 2020.

2. Nnamdi Kanu Ya Bayyana Dalilin da ya sa ‘Allah Ke Fushi da Najeriya

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) kuma Daraktan Rediyon Biafra, Nnamdi Kanu, ya ce Allah ya na fushi da Najeriya.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa Kanu ya yi wannan ikirarin ne yayin hirar sa da aka gabatar kwanan nan a Radio Biafra inda ya ba da sanarwar cewa “Biafra ita ce masarautar da kawai muke nema a kasar.”

3. Biafra: Nnamdi Kanu Ya Yi Zargi Kan Shugaba Buhari

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB) kuma Daraktan Rediyon Biafra, Nnamdi Kanu, ya zargi ma’aikatan kamfanin Facebook a Najeriya da hada baki da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari don cire mabiyansa da rage sakonnansu a shafin sa na dandalin sada zumunta na yanar gizo, watau Facebook.

Naija News ta rahoto cewa shugaban IPOB din da ya yi wannan ikirarin a wata sanarwa kwanan nan da ya sanya hannu, ya ce abin ya yi muni kwarai da gaske cewa babbar shafin sadarwa ta yanar gizon tana karkatar da wasu daga mabiyanta zuwa wata asusun karya da aka bude da sunansa, don kawai a lalata kokarinsa ga samun ‘yanci ga Biafra.

4. Ba a Dakatar Da Obaseki Ba, Oshiomhole Kuma yaci gaba da Jagoran mu – APC

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na Jihar Edo, Anselm Ojezua, ya ce shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole, ba shine shugaban jam’iyyar a jihar ba.

Ojezua ya sanar da hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar bayan wata ganawa da ya yi da shugabannin jam’iyyar a Edo ta Arewa a karamar hukumar Jattu-Uzaire, karamar hukumar Etsako ta yamma na jihar.

5. ISWAP: Musulmai Suna Allah Wadai Da Kashe Kashen Kiristoci – Shehu Sani

Tsohon Sanata a Jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani ya yi Allah wadai da kisan Kiristocin da membobin kungiyar Islamic State a Afirka ta Yamma (ISWAP) suka yi a kwannanan.

Ka tuna, Naija News ta ruwaito a baya da rahoton cewa membobin kungiyar ISWAP a ranar Kirsimeti sun kashe mutane goma sha daya, wadanda yawancinsu duk Kiristoci ne.

6. APC Da PDP Ba zasu Zantar da Ayyukan Majalisar Dattawa ba – Lawan

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan ya ce Jam’iyyun All Progressives Congress (APC) da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba za su tantance ayyukan majalisar dattawa ba.

Shugaban Majalisar Dattawa ya sanar da hakan ne a ranar Asabar a jihar Yobe, yayin wani liyafar da aka gudanar don girmama masa.

7. ‘Yan Shi’a:‘ Yancin El-Zakzaky Ba A Hannun El-Rufai Yake ba – IMN Sun fada wa Gwamnatin Shugaba Buhari

Kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wacce kuma aka fi sani da suna Shi’a, ta yi Allah wadai da bayanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari na cewa ‘yancin shugabanta, Ibrahim El-Zakzaky ya dangana ne a hannun gwamna Nasir El-Rufai na Kaduna.

Naija News ta tuno cewa yan Shi’a sun yi kiran a saki El-Zakzaky ne bayan sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore.

8. Yadda DSS Suka Aiko Da ‘Yan Ta’adda Don Bubbuge Ni – Deji Adeyanju

Dan gwagwarmayar siyasa Deji Adeyanju ya zargi Ma’aikatar Tsaro ta Kasa (DSS) da aikar da wasu ‘yan ta’adda da suka yi masa mugun bugu a yayin zanga-zanga.

Naija News ta tuno da cewa wasu ‘yan ta’adda sun hari Adeyanju tare da sauran masu zanga-zangar neman a saki Omoyele Sowore a Abuja.

Ku samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa