Labaran Najeriya
Hukumar FIRS ta tara ma gwamnatin Buhari makudan kudi N5,000,000,000,000
FIRS ta fitar bayyana da cewa ta tara wa gwamnati makudan kudade da suka kai naira tiriliyan biyar (N5,000,000,000,000)
Ta tabbata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tottoshe ramukan da kudaden gwamnati suke sulalewa, bayan sanarwar da hukumar tara harajin kudaden gwamnatin tarayya.
Amma ya ce ba zasu raunana a gwiwa ba har sai sun tara naira tiriliyan biyar da biliyan dari uku kafin shekarar 2018 ta kare, watau yana nufin suna fatan zasu kara akalla kudi naira biliyan dari uku akan kudaden da suka tara zuwa yanzu.
Har Idan FIRS ta cika alkawalin ta na tara kudi kimanin naira tiriliyan biyar da biliyan dari uku, ya zamto hukumar ta kafa tarihin da ba’a taba kafawa ba a Najeriya, saboda a tarihinta, mafi yawan adadin kudinda ta taba tarawa a shekara shine naira tiriliyan biyar da biliyan bakwai a shekarar 2012.
Masana na ganin FIRS ta cancanci yabo da jinjina ko a haka da ta tara naira tiriliyan biyar, a yanzu da farashin mai ya karye gaba daya, inda farashin gangan mai yake hawa da sauka a tsakanin dala 50 da dala 70, amma a shekarar 2013 yana tsakanin dala 100 da dala 120.
A jawabinsa, shugaban FIRS, Babatunde Fowler ya bayyana farin cikinsa da wannan cigaba da suka samu a hukumar, inda yace hakan ba zai yiwu ba sai da gudunmuwar da suka samu daga fadar shugaban kasa, ma’aikatan kudi, hukumar JTB da sauran masu ruwa da tsaki.
“Muna fatan zamu kai naira tiriliyan 5.3 zuwa karshe shekara, wanda zai zamto haraji mafi yawa da FIRS ta taba tarawa a tarihinta, kuma ina fatan da wannan karin kudin, gwamnatin tarayya, ya jihohi da ta kananan hukumomi zasu kara kaimi wajen gudanar da ayyukan cigaba don amfanin jama’a.” Inji shi.
Naija News ta ruwaito Yan sanda sun karbi rajistan mutane 104,289 daga’ yan Najeriya bisa bukatar su da kimanin mutane 10,000 kawai ga wannan dauka.