Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta Ranar Litini 7, ga Watan Janairu, a Shakara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini 7 ga Watan Janairu, 2019

1. Amina Zakari ta bayyana dangantakar ta da Shugaba Buhari

Amina Zakari, Kwamishanan Tarayya na Hukumar (INEC), ta yi magana a kan zargi da fade-faden da ake yi da cewar ta na da dangantaka da Shugaba Muhammadu Buhari.

Amina Zakari ta ce, “Ni ba yar’uwa, ko diya, ko kanuwa ba ce ga Shugaba Buhari”, ta bayyana wannan ne a wata ganuwa da ta yi da manema labaran BBC.

2. Kungiyar KSB sun samar da wuta ga kamfanin Conoil da ke a Jihar Bayelsa

Gidan Kampani Mai na Conoil da ke a Koluama, Yankin Ijaw na Jihar Bayelsa ta fashe da wuta a wannan karshen mako da ta gabata.

Wata rukuni, wanda sun bayyana kansu da suna ‘Koluama Seven Brothers (KSB) sun dauki alhakin fashewar wutar da ta auku a wannan gidan man.

3. Rundunar sojojin ta mamaye ofishin Jakadancin

Sojojin Najeriya sun mamaye ofishin ‘Yan yada Labarai ta Daily Trust da ke a Maiduguri, Jihar Borno a ranar Lahadi, sun kuma kama Editan Labarai na Yankin mai sun Uthman Abubakar da kuma wani mai gabatar da labarai Ibrahim Sawab.

Sun kuma bukaci ganin Editan labaran Siyasa, Hamza Idris wanda sunansa ya bayyana a cikin jerin muhimman labarai na gidan labaran yankin.

4. Fayose ya bukaci Aisha Buhari ta bayyana Rukunin da ke cikin shugabancin Buhari

Ayodele Fayose, Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti ya ce ‘yan Najeriya za su dauki bukatar Uwargida Buhari, Aisha Buhari na neman a sake zaben mijinta ga mulki da mahimancin idon har za ta bayyana rukuni da ke cikin shugabacin da ta ce da baya cewa su ne sanadiyar kasawar mijinta a mulki.

Ya kara da cewa za ta renar ma ‘yan Nijeriya da hankali idan har ta bukaci neman a sake zaben mijinta ga mulki kuma taki gabatar ga al’umma wadannan rukuni da ta fada da baya.

5. Amaechi na yi wa Buhari gwallo da dariya

Reno Omokri, tsohon ma’aikata na shugaban kasa na da, Goodluck Jonathan ya fito da wani sabon bidiyo wanda ministan harkokin sufuri, Rotimi Amaechi ya yi wa shugaban kasar Muhammadu Buhari dariya da gwallo.

Ya kara da barazanar cewa zai fito da wasu odiyo inda Amaechi ya zargi shugaba Buhari, idan har ministan bai bar yin hakan ba.

6. Gwamnatin Tarayya ta umarci sojoji su janye kansu daga shafin yanar gizon Daily Trust

Gwamnatin tarayya ta ba da umarni ga sojojin Najeriya cewa su janye kansu daga harin da suka kai a Ofishin ‘yan Jaridan Daily Trust da ke a Maiduguri a ranar jiya.

Gwamnatin Tarayyar ta bukaci Sojojin su warware masalolin da ke tsakanin su da Manema labaran ta hanyar tattaunawa.

7. Jam’iyyar ASUU ta amince da hada hannu da Hukumar INEC ga zaben 2019

Cibiyar Harkokin Jami’ar ASUU ta amince da cewa za su hada hannu da hukumar zaben a zaben 2019 ta gaba.

Cibiyar kungiyar tarayya ta Jami’o’in da Hukumar INEC sun kai ga wannan yarjejeniya ne a ranar Juma’a, a birnin Abuja.

8. Kungiyar NANS ta karyata zargin cewa ta karbi kudi daga shugabancin

Ƙungiyar ‘Yan Jami’ar Najeriya (NANS) ta yi watsi da zargin da ake yi na cewar kungiyar ta karbi Naira Miliyan Dari da Hamsin (N150m) daga shugabancin, sun fada da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ba mutum ba ne mai bada kudin cin hanci.

‘Yan Jagorancin NANS sun janye kansu daga wannan zargin da Jam’iyyar (ASUU) ke dauke da shi.

9. Sanata Dino Melaye ya sunbuke a hannun ‘Yan Sanda

Dan Majalisar Dattijai, Sanata Dino Melaye wanda ke wakiltar Yamma ta Jihar Kogi, ya sumbuke a hannun ‘yan sanda bayan da ya mikar da kansa ga jami’an bayan kwana takwas 8 da suke mamaye a gidansa don neman kama shi.

Sanatan ya fadi ne a yayin da ya ke kokarin shiga motar ‘yan sanda bayan mikar da kansa.

10. Sojoji sun ci nasarar mulki a Gabon

Sojoji da ke Gabon sun karbi iko a kasar mai arzikin man feturr, inda dangin Ali Bongo sun yi shekaru 50 da mulki.

Sojojin sun ce sun kaddamar da rukuni dan dawo da “dimokuradiyya a kasar. an bada labarin ne ga BBC a ranar Litinin.

Samu karin labaran Najeriya akan hausa.naijanews.com