Uncategorized
Gwamnatin Tarayya ta gabatar da hutu aikin ranar Jumma’a 22 ga Watan Fabrairu
A yau Alhamis 21 ga watan Fabrairun, Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ranar Jumma’a, 22 ga watan Fabrairun, 2019 a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan kasa don samun daman tafiya ga ma’aikata da ‘yan kasa ga shirin zaben shugaban kasa da na gidan majalisa da za a gudanar a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairun.
An gabatar da wannan sanarwan ne daga bakin Ministan Harkokin Kasa, Abdulrahman Dambazau a wata gabatarwa da sakataran Ministan harkokin waje, Barr Georgina Ehuriah ya sanya hannu daren ranar Laraba ta gabata.
An bada wannan hutun ne don ma’aikata su samu lokacin tafiya zuwa jihohi, da yankunan su don jefa kuri’ar su a matsayin dan kasa a zaben shugaban kasa da za a yi ranar Asabar.
“An umarci hukumomin tsaron kasa duka don samar da isashen tsaro ga matafiya kamin zabe da kuma bayan zaben” inji Dambazu a cikin gabatarwan sa.
Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa ‘Yan Hari da bindiga sun kashe wani ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar Imo