Labaran Najeriya
DSS na Bayar da damar Amfani da Wayar Tarho ga kwamandojin Boko Haram – Sowore
Omoyele Sowore, mai gabatar da zanga-zangar #RevolutionNow da kuma jagoran Kanfanin Dilancin yada Labarai ta Sahara Reporters, ya bayyana cewa ba a ba shi izinin amfani da wayar tarho ba yayin da yake tsare da ma’aikatar Tsaron Gwamnatin Tarayya (DSS).
Dan takar kujerar shugaban kasar a zaben 2019, Sowore ya zargi jami’an DSS da barin kwamandojin Boko Haram da aka katange a Ofishin Hukumar don yin amfani da wayar salula don sadarwa.
Naija News Hausa ta sanar a shafin Manyan Labaran Jaridun Najeriya ta yau da cewa Mai shari’a Ijeoma Ojuwku na babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, ta ba da umarnin a tsare Omoyele Sowore a hannun Ma’aikatar Tsaron Kasa ta (DSS), yayin da za a saurari karar neman belin nasa a ranar 3 ga Oktoba 2019.
Wanan na biyo wa ne bayan da Sowore ya ki amincewa da kuma kin neman afuwa game da tuhume-tuhume bakwai da ake masa na zamba, cin amanar kasa, satar kudi da kuma yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa.