Connect with us

Uncategorized

Takaitaccen Labarin Rayuwar Maryam Booth

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Maryam Ado Muhammed, wata Kyakyawa da aka fi sani da Maryam Booth, Shahararra ce a fagen wasan kwaikwayo na Kannywood, Tana kuma da Fasaha wajen aikin Dinke-dinke.

ASALIN MARYAM BOOTH

Maryam Ado Muhammed ‘yar haifuwar Jihar Kano ce a arewacin Najeriya, an kuma haife ta ne a ranar 28 ga Watan Oktoba, a shekaran 1993.

Mahaifiyarta Maryam kuwa Ita ce, Zainab Booth, Ita ma kwararra ce kuma daya daga cikin wadanda suka dade a shirin wasan kwaikwayo na Kannywood. Haka Kazalika dan uwan Maryam, watau Ahmed Booth, shi ma Gwarzo ne a filin hadin Fim na Kannywood.

Ko da shike Kaka ta Mace ga Maryam Fulani ce, amma Kakanta namiji dan Turai ne, daga Scotland.

KARATUN MARYAM BOOTH

Booth ta yi makarantar farko ne a Ebony Nursery and Primary school, ta kuma yi kara gaba ga makarantar sakandare na Ahmadiyya, inda tayi karatun Sakandare nata.

SHIGAN MARYAM BOOTH A FAGEN FINA-FINAN HAUSA

Maryam tayi shigan ta a shirin fim na farko ne a lokacin da take ‘yar shekara 8 da taimakon ‘yar uwarta da ita ma ke cikin shirin fina-finan hausa a lokacin.

‘Yan lokatai kadan kuma sai aka fara gane da kwarewar Maryam a fagen fim, musanman a cikin wata fim mai liki ‘Dijangala’.

A Filin Kannywood; Maryam Booth ta samu daman fita cikin fina-finai da dama, kamar su; Alawiyya, Ankwa, Bani Adam, Dare, Baya, Halisa, Garin Gaka, Mai Lita dadai sauransu.

Ba shirin Fim kawai Booth ke yi ba, Naija News Hausa ta gane da cewa Maryam Booth Oga ce a wata kamfani na kanta. Itace shugaban kamfanin Mbooths Beauty Parlor, inda take zane-zane da shafe-shafen kayan adon mata da ake cewa  (Makeup Artist) da kuma aikin Dinke-dinke iri daban daban.