Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 8 ga Watan Mayu, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 8 ga Watan Mayu, 2019

1. Masu Zanga-Zanga sun Katange Osinbajo akan wata zargi

‘Yan zanga-zangar adawa a ranar talata sun katange mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a babban hanyar Umaru Musa Yar’Adua ta birnin Abuja.

Hakan ya faru ne a yayin da Osinbajo ya ci karo da Gwarawa (Gbagyi) garin Goza, lokacin da yake zuwa filin jirgin sama don wata tafiya.

2. Kotu ta bada belin Adeleke, ta kuma daga karar da ke da shi zuwa gaba

Wata kotun majistare dake a Mpape, Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya ta bada daman belin naira miliyan biyu ga Ademola Adeleke, Sanatan da ke wakiltar yankin Jihar Osun.

Mun ruwaito a baya a gidan labaran nan tamu da cewa Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya sun kame Adeleke, Sanata daga Jam’iyyar PDP da ke wakilcin yankin Osun akan wata zargi.

3. Shugabancin kasar Najeriya tayi watsi da zargin bada kudi Miliyan (N100m) ga miyetti Allah

Babbar Mataimakin musanman ga Shugaba Muhammadu Buhari ta harkan Sadarwa, Garba Shehu, ya ce Kungiyar Miyetti Allah’s Association of Breeders Association ta Najeriya daya take da kungiyar Afenifere (Yarbawa) da kuma Ohanaeze Ndi Igbo (Iyamirai), dukan su kungiyoyin zamantakewa da al’adun kasar ne, don haka kada a dauke su ‘yan ta’adda.

Shehu ya fadi hakan ne a ganawar da aka yi tsakanin shugaban Jami’an tsaron ‘yan sanda, Mohammed Adamu da jagorancin Miyetti Allah.

4. Majalisar Dattijai da ‘Yan Sanda sun amince da hada hannu don yaki da Matsalar tsaro a Najeriya

Ganawar Majalisar Dattijan Najeriya da shugaban Jami’an tsaron ‘yan sandan Najeriya, IGP Adamu, ya kai su ga amincewa da juna ga hada kai wajen dakatar da ta’addanci da matsalar tsaro da ake fuskanta a kasar Najeriya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a ranar Talata da ta gabata da cewa Majalisar Dattijai da IGP Adamu na ganawa a birnin Abuja akan Matsalar tsaron kasar Najeriya.

5. Rundunar NAF sun kashe ‘yan ta’adda 20 a Jihar Zamfara

Rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) sun gabatar da cewa rukunin yakin su ta “Operation DIRAN MIKIYA” sun ci nasara da rutsa shugaban ‘yan ta’adda, Alhaji Lawal, da kuma samun kashe kimanin mutane 20 a shiyar Rugu ta Jihar Zamfara.

Naija News ta gane da hakan ne bisa sanarwan da aka bayar ranar Talata da ta wuce, daga bakin Ibikunle Daramola, Magatakardan rundunar Sojojin Sama.

6. Kotun Karar Zabe ta bada sakon musanman ga Atiku Abubakar

Dan takaran kujerar shugaban kasar Najeriya a zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya karbi sakon kulawa da kara ta farko daga hannun Kotun da ke Karar Lamarin Zaben Kasa.

Ka tuna da cewa Atiku na Gwagwarmaya da kokarin kwato yancin sa akan rashin amincewa da sakamakon zaben 2019, wanda aka gabatar da Buhari a matsayin shugaban kasa bayan kirgan kuri’u.

7. Matasa da basu da aiki sun shiga Hidimar Ta’addanci – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yayi bayani akan hare-hare da kashe kashen da ke aukuwa a kasar Najeriya a wannan lokaci da ake ciki.

Buhari ya ce “Matasa Mara sa Aiki sun shiga zancen ta’addanci a kasar Najeriya wai don amfani da ta’addanci don taimaka wa zaman rayuwansu.”

8. Matsalar da Najeriya ke ciki ba Cin Hanci da Rashawa bane, Rashin Shugabancin Kwarai ne – Dogara

Kakakin Yada Yawun Gidan Majalisar Wakila, Yakubu Dogara, ya bayyana da cewa ba matsalar cin Hanci da Rashawa Najeriya ke fuskanta ba, amma matsalar rashin shugabancin kwarai.

Wannan ita ce bayanin Dogara a ranar Talata da ta gabata, a wata taron tattaunawar shugabanci da  aka yi a birnin Abuja.

9. Liverpool sun lashe wasan sun da Barcelona da Gwalagwalai 4

Wasan Kwallon kafa tsakanin Kungiyar ‘yan wasan Kwallon kafa ta Ingila, Liverpool da Kungiyar wasan kwallon Barcelona da aka buga a daren ranar Talata da ta gabata ya karshe da Gwalagwalai 4:0.

Naija News Hausa ta gane da cewa Liverpool sun ci nasara da Barcelona don kai ga wasan karshen Champions League.