Connect with us

Labaran Nishadi

Kannywood: Takaitaccen Labarin Nafisat Abdullahi

Published

on

Nafisat Abdulrahman Abdullahi, wadda akafi sani da Nafisat Abdullahi, kyakyawa ce da kuma shahararrar ‘yar shirin fim a Kannywood, watau kamfanin hadin fim na Hausa a Najeriya.

An haifi Nafisat ne a ranar 23 ga watan Janairu ta shekarar 1991 a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

Nafisat ita ce ‘ya ta hudu ga Mallam Abdulrahman Abdullahi, wani dillalin motoci da kuma dattijo masu ruwa da tsaki a kasar.

Karatun Nafisat Abdullahi

Naija News Hausa ta fahimci cewa kyakyawar tayi karatun ta na farko ne a Makarantar ‘Air Force Private School’ a nan Jos, bayan nan ta koma Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, inda ta shiga makarantar Sakandare ta Gwamnati, Dutse, Abuja.

Tun tana yarinya, ta shiga masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood inda ta fara shirinta a karkashin FKD Production tare da Ali Nuhu, a matsayinsa na mai bada shawara na farko a gareta.

Ta Yaya da Kuma Wani Lokaci Ne Ta Fara Hadin Fim?

Nafisat Abdullahi dai ta fara aikin fim ne tun tana ‘yar shekara 19 tare da FKD Production, a matsayin kamfanin shirya fina-finanta na farko inda ta fara fitowa a cikin fim din ‘Sai Wata Rana’ a shekarar 2010, fim da aka shirya ta hannun babban kwararre da jigo a Kannywood, Ali Nuhu.

Ainihi, Nafisat ta fara aikinta na fim ne a matsayin kwararra da farkon shekarar 2010, lokacin da ta taka rawar gani na farko a jagorancin Sai Wata Rana a matsayinta na babbar jigo a fim din.

Ta samu kyautar shiri daga ‘City People Entertainment’ a shekarar 2013 don taka rawar gani, da kuma kwarewa da lambar yabo ta Kannywood a cikin 2014 don Mafi kyawun shahararriya a Kannywood.

Kyautuka Da Nafisat ta Lashe a Shirin Fim:

Shekara      Mai Bayar da Kyauta                                Sashen Kyautar                      Fim

2013,  City People Entertainment Award    – Shahararrar ‘Yar Shirin fim  –   A Fim din (Ya Daga Allah)

2014            Kyautar Farko a Kannywood   – Fitacciyar ‘Yar Shirin Fim     –   Dan Marayan Zaki

2014            AMMA Awards                       – Fitacciyar ‘Yar Shirin Fim      –   Dan Marayan Zaki

2015           Kyautar Kannywood ta Biyu    – Kyautar Musanman a Kannywood
2016           City People Entertainment      – Fitacciyar ‘Yar Shirin Fim      –     Kyautar Musanman
2016           AMMA Awards                        – Fitacciyar ‘Yar Shirin Fim      –     Da’iman
2016           Kyautar Kannywood Na Uku   – Fitacciyar ‘Yar Shirin Fim      –     Baiwar Allah

Ga Jerin Fina-Finai da Nafisat Abdullahi ta Fito a Ciki:

Ummi
Zango
Ya daga Allah
Yar Agadez
Addini ko Al’Ada
Ahlul Kitab
Alkawarina
Alhaki Kwikwiyo
Alhini
Allo (film)
Auren Tagwaye
Baban Sadik
Badi Ba Rai
Ban Kasheta Ba
Blood and Henna
Cikin Waye?
Dan Almajiri
Dan Marayan Zaki
Dare
Dawo Dawo
Farar Saka
Fataken Dare
Gabar Cikin Gida
Haaja
Har Abada
Jari Hujja
Laifin Dadi
Lamiraj
Madubin Dubawa
Guguwar So
Baiwar Allah

Labaran Nishadi

Takaitaccen Labarin Rayuwar Hafsat Idris (Barauniya)

Published

on

Jaruma Hafsat Ahmad Idris, wadda aka fi sani da kiranta Hafsat Idris, yar wasan fim ne a shafin masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood.

Hafsat asalinta ‘yar jihar Kano ce, arewacin Najeriya. Amma an haife ta da kuma girmar da ita ne a Shagamu, jihar Ogun.

Tauraron Jarumar Hafsat Idris ya hasko ne da bayyanata a hadin fim da ta yi inda ta taka rawar gani cikin fim din mai taken ‘Barauniya’, wannan shirin ne fim na musanman da ya haskaka jarumar da kuma daukaka ta a harkar fim.

An zabi Hafsat a matsayin jarumar Kannywood da ta fi fice a shekarar 2017 daga kamfanin dilancin shiri ta City People Movie Awards.

Hafsat Ahmad Idris ta fara shirin fim ne a shekarar 2016 a fim din Barauniya, tare da jarumi Ali Nuhu.

Naija News Hausa bisa bincike ta fahimta da cewa jarumar ta shiga masana’antar kannywood ne bayan da ta gwada hannun ta a harkar kasuwanci. Takan yi tafiye-tafiye mafi yawan lokuta daga Oshogbo, jihar Osun zuwa Kano saboda kasuwanci.

Ko da shike, duk da cewa ta fi kyau a harkar kasuwanci, amma sha’awar Hafsat ta karkata ga zama ‘yar wasa.

Hafsat ita ma ta mallaki kamfanin shirya fina-finai da aka sani da Ramlat Investment, kuma ta fitar da fina-finai da dama a shekarar 2019 ciki har da fim mai ‘Kawaye’, babban shirin ya hada da manyan ‘yan wasa da shugabannai a Kannywood, kamar su Ali Nuhu, Sani Musa Danja, hadi da ita Hafsat.

Hafsat ta fice a cikin fina-finai da yawa, kamar su; Biki Buduri, Furuci, Labarina, Barauniya, Makaryaci, Abdallah, Ta Faru Ta Kare, Rumana, Da Ban Ganshi Ba, Wacece Sarauniya, Zan Rayu Da Ke, Namijin Kishi, Rigar Aro, Yar Fim, Dan Kurma, Kawayen Amarya, Dr Surayya, Algibla, Ana Dara Ga Dare Yayi, Mata Da Miji, Dan Almajiri, Haske Biyu, Maimunatu, Mace Mai Hannun Maza, Wazir, Gimbiya Sailuba, Matar Mamman, Risala, Igiyar, Zato, Wata Ruga, Rariya.

Continue Reading

Labaran Nishadi

Kalli Klub Da Zasu Hade A Karo Na 16 Ga Gasar cin Kofin Zakarun Turai

Published

on

Wannan itace Tsari da Jerin Klub da zasu hade a Gasar cin Kofin Zakarun Turai zagaye na 16, bisa kacici-kacici da aka yi a ranar Litini (yau) 16 ga watan Disamba 2019.

*Barcelona vs Paris Saint-Germain
*Real Madrid vs Man City
*Atalanta da Valencia
*Atletico Madrid vs Liverpool
*Chelsea vs Bayern Munich
*Lyon vs Juventus
*Tottenham vs RB Leipzig
*Barcelona vs Barcelona

A halin da ake ciki, wasan farko na cin Kofin Zakarun Turai din ta zagaye na 16 zai fara ne daga ranar 18/19/25/26 a watan Fabrairu, yayin da juyi ta biyu kuma zai gudana ne daga ranar 10/11/17/18 ga watan Maris a shekara ta 2019.

Continue Reading

Labaran Nishadi

Ni Ba ‘Yar Kano Bace, Saboda Haka Ba Ku Da Iko A Kaina – Sadau Ta Gayawa Kannywood.

Published

on

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana da cewa shugabancin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa a Kano wace aka fi sani da Kannywood, cewa basu da ikon daukan matakan hukunci a kanta, don ita ba ‘yar Kano ba ce.

Wannan zancen ya fito ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai ya bayar a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba 2019.

A bayan hakan ne aka gano wasu hotuna da faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram, inda jarumar ke cikin wani yanayi da shiga marar kyan gani na rashin da’a, tana ta taka rawa, inda wani sassa na jikinta musamman ta kafarta duk a waje yake.

Shugaban ya ce kungiyar na fuskantar matsala game da daukar mataki kan jarumar, Rahama Sadau. A yanayin da ya bayyana da mara kyan gani da kuma abin kyama wacce yake zargin jarumar ta yi akan ikirarin cewa ita fa ba ‘yar Kano bace saboda haka ba su da iko akanta.

Sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da sa ido kan jarumar domin gano gaskiyar ikirarin da ta yi.

“Matukar muka gano cewa tana karkashin ikon mu ba zamu bata lokaci ba wajen daukar matakin ladaftarwa akanta. Ba zamu saurara mata ba, Ina tabbatar muku matukar ta yi kokarin shirya film a yankin da muke iko wato nan jihar Kano,” inji Yakasai.

“Amma a yanzu bamu da iko saboda bazan iya yin hukunci a wata jiha ba saboda suma da nasu shugaban cin” Inji Shi.

Continue Reading

Trending