Uncategorized
‘Yan Hari da Makami sun Sace Malamin Makarantan Jami’a a Katsina
Mahara da bindiga sun sace wani malamin makarantan Jami’a na Hassan Usman Polytechnic Katsina, Mista Bello Abdullahi Birchi.
Naija News Hausa ta fahimta cewa hakan ya faru ne bayan da Rukunin Jami’an Tsaro ‘Yan Sanda (Operation Puff Adder) ta kashe daya daga cikin ‘yan hari da makamin da ke tsorata da tsananta wa mazaunan yankin Batsari da karamar hukumar Safana, ta Jihar Katsina.
Mista Birchi, da ‘yan hari da makamin suka sace mazauni ne na shiyar Birchi, karamar hukumar Kurfi, Lakcara ne kuma a Makarantar Jami’a na Hassan Usman Polytechni Katsina a sasshen Technical Education.
Bisa bayanin manema labarai da kuma rahotannai daga shiyar, ‘yan harin kimanin su biyar, sun fada a gidan Mista Birchi ne a daren ranar Laraba da ta wuce akan babura, suka kuma sace shi.
A yayin bayani ga manema labaran THISDAY aka wayan salula, Ciyaman na Hukumar Malaman Makarantar Jami’ar Fasah (ASUP) ta Jihar Katsina, Dakta Sabi’u Abdullahi Ya’u, ya bayyana da cewa hukumar su ta riga ta gabatar da lamarin ga hukumomin tsaro.
“A zaran da na karbi rahoton al’amarin, sai na yi kirar gaugawa da mambobin hukumar mu, na kuma sanar da su ga abin da ya auku, Anan take kuma muka sanar ga hukumomin tsaron Jihar” inji Dakta Sabi’u.
“Ko da shike Maharan sun ajiye lambar wayan su, amma Jami’an tsaron sun shawarcemu da cewa kada mu yi gaugawar kiran lambar. Sun bukace mu da basu damar bincike da ga al’amarin kamin yin hakan”
KARANTA WANNAN KUMA: Kalli Sakon Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ga Matarsa Dolapo