Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Makami sun kai sabuwar Hari a kauyan Dan Musa ta Jihar Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa an sace wasu mutane uku a sabuwar harin mahara da makami a shiyar kauyan Dan-Ali da ke a karamar hukumar Danmusa, Jihar Katsina.

Bayan da ‘yan harin suka sace mutanen, an bayyana cewa sun sace kudaden su kuma da kayan zaman arzikin su duka.

An sanar da tabbacin harin ne a wata sanarwa da Mallam Tukur Dan Ali ya bayar ga manema labaran gidan talabijin Channels TV, inda ya bayyana da cewa ‘yan uwanshi na cikin mutanen da aka sace.

A bayanin sa, ya bayyana cewa maharan sun isa kauyan ne a missalin karfe biyu na safiyar ranar Talata.

“Sun fada wa kauyan mu ne a missalin karfe biyu saura a asuba’in ranar Talata, suka kuma shiga harbe-harben bindiga ko ta ina kamin suka sace mutane ukun hade da macce daya”.

“A yayin da suke harbe-harben, sai suka fada gidan Alhaji Musa da Alhaji Gambo, inda suka sace mutane ukun” inji Tukur.

Ko da shike ya bayyana cewa da baya maharan sun saki daya daga cikin mutanen da suka sace, watau matar, Hajiya Fatima, ba tare da an biya komai ba.

Ya kara da cewa har missalin karfe biyar na safiyar yau jami’an tsaro basu halarci kauyan ba.

Anyi kokarin karban bayani daga kakakin yada yawun Jami’an tsaron jihar, Gambo Isah, amma ba a samu hakan ba a lokacin da aka karbi wannan rahoton.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta gabatar da hana duk wata hidima a Jihar, musanman Sallar Durbar, don gujewa harin ‘yan ta’adda.