Uncategorized
Kannywood: Fati Washa Ta Karbi Karin Girma Na Kyautar Gwarzuwar Jaruma a Birtaniya
Shaharariyar jarumar a shirin fina-finan Hausa a Kannywood, Fatima Abdullahi, da aka fi sani da suna Fati Washa ta lashe wata sabuwar kyautar gwarzuwar jaruman Hausa a wani kasaitaccen bikin fina-finan Afirka wadda ya gudana a kasar Birtaniya.
Ka tuna da kamar yadda Naija News Hausa ta ruwaito a baya, da cewa Masoyan Jaruma Fati Washa sunyi Allah wadai da wasu Hotunan da ta watsar a layin yanar gizo ranar zagayowar ‘yancin Najeriya da aka yi a watan da ta gabata.
Washa ta lashe matsayin gwarzuwar jaruma ne a taron karrama ‘yan Fim da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata a birnin London, a wata Biki mai taken ‘Afro Hollywood Awards’, wanda ya shafi karrama jaruman fina-finan harsunan Najeriya guda uku Hausa da Yoruba da Igbo da kuma harshen Inglishi, watau Turanci a sassan kasashen Afirka.
Naija News Hausa ta fahimci cewa jaruma Fati Washa ta kai ga nasarar lashe kyautar ne saboda rawar gani da ta taka a Fim dinta mai taken ‘Sadauki.’
A yayin mayar da martani akan kyautar, jaruma Fati Washa ta bayyana farincikinta ga masoya. Ta ce ta “sadaukar da kyautar ga masoyanta tare da godiya garesu.”
Wannan zancen ya fito ne a bidiyon da ta wallafa a shafinta na Instagram inda take bayyana farincikinta.
Kalli Bidiyon Lokacin da aka baiwa Fati Washa Kyautar;
https://www.instagram.com/p/B4YXIPtBwnV/?utm_source=ig_embed
Kamfanin Dilancin Labarai ta Naija News Hausa ta gane bisa bincike da cewa wannan itace karo na 23 da ake gudanar da bikin karrama jaruman fina-finan, wanda Jaridar African Voice da ke Birtaniya tare da tallafin gudauniyar Esther Ajayi da Ned Nwoko ke daukar nauyinta.
A bayanin Mashiryan bikin a Birtaniya, sun iya bada haske da cewa fiye da fina-finai 500 ne daga nahiyar Afirka ke shiga gasar da aka fara tun 1996 da ya shige.
KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da Yasa Shahararren Jigo, Adam A. Zango ya fita daga Kannywood.