Uncategorized
‘Yan Sanda Jihar Neja Sun Kame Mutane Biyu da Zargin Sanadiyar Mutuwar Wata Yarinya
Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta bayyana yadda suka kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata kisan gilla wanda ya yi sanadiyar mutuwar Hannatu, wata ‘yar shekara 23 a kauyen Gauraka a karamar hukumar Tafa da ke jihar.
A yayin mayar da martani akan alamarin, Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adamu Usman ya bayyana a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Minna ranar Juma’a da cewa lallai hakan ya faru.
“a ranar 6 ga watan Nuwamba da misalin karfe 9.30 na safiya, wata yarinya mai suna Favour daga kauyen Gauraka ta gabatar da karar alamarin ga sashin ‘yan sanda da ke a Tafa,” inji Usman.
Yarinyar wacce ta shigar da karar ta ba da rahoton cewa wanda ake zargin ya yi kwancin zina da ‘yar uwarta Hannatu, ya kuma sa ta dauki juna biyu, da mika mata kudi Naira dubu 4 don ta zubar da cikin a wurin wani mai Kemis da ke a Gauraka, bayan da ya gane da cikin.
Favour ta bayar da cea zubar da cikin da ‘yar uwanta ta yi ya haifar da mumunar matsala a yayin da sai da suka haura da ita zuwa Babban Asibitin Sabon Wuse.
Kwamishinan Jami’an Tsaron yankin ya bada tabbacin cewa a yayin kulawa da Hannatu a Asibitin, nan take ta mutu, da cewa ‘yan sanda sun yi nasarar kuwa da kama wanda ake zargin da kuma mai Kemis din.
“Bayan karin bincike, zamu tabbatar da kai su biyun a gaban Kotun Kara” inji Usman.