Uncategorized
APC/PDP: Yakin Basasa Ne Ya Faru a Jihar Kogi Ranar Asabar ba Zabe ba – Dino
Sanata Dino Melaye ya bayyana abin da ya faru a jihar Kogi a ranar Asabar din da ta gabata a matsayin yakin basasa ba zabe ba.
Ka tuna da cewa Dino ya nemi kujerar Majalisar Dattawa ta yankin Kogi ta yamma a zaben da aka yi ranar Asabar, 16 ga Watan Nuwamba a zaben Sanata da aka yi hade da ta gwamnoni a Jihar.
Ko da shike hukumar INEC ta gaza sanar da mai nasara ga zaben akan wata babban sanadiyya, Dino ya ce zaben kamar yakin basasa ce a yayin da zaben ta yi sanadiyar rasa rayukan mutane 16.
Ya ce zai kai karar Yahaya Bello, Smart Adeyemi, Sunday Faleke da sauransu ga kasashen duniya sannan daga nan ya wuce zuwa Hague.
“Abin da ya gudana a Jihar Kogi ba zabe ba ne, abin da ya afku yakin basasa ne wanda ya yi sanadiyar mutuwar rayuka 16. Zan yi karar Bello, Smart Adeyemi da Taofik, Kakakin majalisar Kolawole da Sunday Faleke ga manyan kasashen duniya sannan daga nan in tafi Hague. Wannan itace alkawari na,” in ji Melaye.