Connect with us

Uncategorized

‘Yan Boko Haram Sun Kai hari Garin Chibok, Sun Kashe Mutane Shida

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Akalla mutane shida ne suka mutu da mata biyu da mayakan Boko Haram suka sace a ƙauyen Kwaranglum da ke jihar Borno.

Kwaranglum na kusan kilomita guda ne zuwa garin Chibok, hedikwatar karamar hukumar Chibok na jihar Borno.

Naija News ta samu labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar Kirsimeti, a cewar kwamishinan yada labarai na kawar da talauci, Mista Nuhu Clark, wanda dan asalin yankin ne, ya fadawa manema labarai cewa, ‘yan kungiyar Boko Haram sun mamaye kauyen lokacin sallar magariba (da misalin karfe 6 na yamma), kuma suka fara harbi ba dare ba rana.

Ya lura cewa an lalata wata makarantar firamare a yayin harin kuma an sace abinci mai yawa daga harabar cocin.

Da yake mayar da martani, gwamna Babagana Umara Zulum, ya bayyana juyayinsa ga dukan al’ummar Chibok bisa ga mummunan harin da aka kai.

Gwamnan ya nemi jama’a da su ci gaba da addu’ar neman zaman lafiya, da kwanciyar hankali a jihar, tare da nuna cewa idan ba zaman lafiya da kwanciyar hankali ba, ba za a samu ci gaba ba a jihar.

Naija News ta kula da cewa a wannan bikin sallan Kristoci ta shekarar nan, jihar Borno da Yobe sun fuskancin hari daban daban daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram.