Labaran Najeriya
Goodluck Jonathan Ya Bayyana Abin Da Jami’an Tsaro Zasu Yi Kan Wadanda Suka Kai Hari Gidansa

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi bincike kan harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai wa gidansa.
Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa, tsohon shugaban bai sami rauni ba a harin wanda aka yi zargi da kisan gilla ne.
Ko da shike wani jami’in tsaro da ke tsaye a gidan ya lashe mutuwa a harin amma har yanzu ‘yan sanda basu fitar da wata sanarwa ba.
Naija News ta ruwaito da cewa Jonathan Jonathan ya yi kira ga hukumomin tsaro a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari da su kama wadanda suka aiwatar da wannan harin da kuma tabbatar da cewa irin wannan harin kunar bakin wake bai sake faruwa ba a cikin harabarsa ko wani wuri a cikin kasar ba.
Tsohon shugaban ya bayyana harin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka kai masa a gidansa da “marasa tausayi”.
“Ku yi taka-tsantsan yayin da kuke kokarin kame da hukunta wadanda suka aikata wannan mumunar harin da kuma tabbatar da cewa wannan mummunan harin bai sake faruwa a kowane bangare na kasar nan.” Inji Jonathan.