Uncategorized
Sabuwa: ‘Yan Ta’adda sun haska wa Ofishin Hukumar INEC wuta a Jihar Akwa Ibom
Wasu ‘yan ta’adda da ba a gane da su ba sun haska wa ofishin hukumar gudanar da zaben kasa da ke Jihar Akwa Ibom wuta a yau Jumma’a, 8 ga watan Maris, shekarar 2019.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a yayin da ‘yan ta’addan suka haska wa ofishin INEC da ke karamar hukumar Ibesikpo Asuntan a nan Jihar Akwa Ibom, ‘yan awowi da soma zaben gwamnonin Jiha da ta gidan majalisar wakilan jihohin kasa.
An bayyana da cewa wasu kayakin zabe sun lallace da kuma konewa da wuta sakamakon wannan harin. Wani mazaunin shiyar ya gabatar da cewa jami’an ‘yan sandan jihar sun samu ribato wasu kayaki a yayin da suka samu isa wajen kamin wutar ta sauwa.
Mun tuna a baya da cewa Jihar Akwa Ibom na daya daga cikin jihohin kasar da aka samu matsalar zabe a lokacin da aka gudanar da hidimar zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, 2019 da ta gabata.
Karanta wannan kuma: Manyan Shugabannan Fulani 66 hade da wasu dag Jihar Sokoto sun yi murabus da Jam’iyyar PDP zuwa APC gabadin zaben gwamnoni.