Connect with us

Uncategorized

Rukunin Tsohon Shugaban Kasa Jonathan tayi Magana kan Murabus dinsa zuwa APC

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wata rukunin watsa labarai ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ta karyata da kuma yi watsi da zargin da ake mai cewa tsohon shugaban kasar ya kammala shirye-shiryen ficewa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party zuwa jam’iyyar All Progressives Congress.

Bayan rikice-rikicen da aka samu tsakanin gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson da tsohon Shugaban, akwai jita-jitar cewa Jonathan ya goyi bayan dan takarar APC, David Lyon a zaben gwamna na Nuwamba 16.

Naija News ta fahimta da cewa ana zargin Jonathan ne da hakan bayan da ake lura da cewa ya yi murna da nasarar David Lyon, dan takarar Gwamna a Jam’iyyar APC daga jihar a zaben ranar Asabar da ta gabata.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasa, INEC ta gabatar da sakamakon zaben Bayelsa na karshe daga dukkan kananan hukumomin (LGAs) inda aka gudanar da zaben gwamnonin.

Rahoton ya bayyana Lyon da samun yawar kuri’u 352,552 da ya kaishi ga kayar da abokan karawarsa da kuma dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babbar jam’iyyar adawa ta Najeriya, Duoye Diri, wanda ya sami yawar kuri’u 143,172.